Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMA
Published: 30th, May 2025 GMT
Yawan mutanen da suka rasu a sakamakon mummunar ambaliyar ruwan sama a yankin Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ya ƙaru zuwa 88.
Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Husseini Isah, ne ya sanar da haka a ranar Juma’a.
Ya ce, “adadin mamatan na ci gaba da ƙaruwa, amma a halin yanzu mun ƙirga mutum 88.
Aminiya ta ruwaito cewa wasu mutum 12 ’yan gida ɗaya suna cikin mutanen da ambaliyar ta yi ajalinsu.
NAJERIYA A YAU: Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu? Faransa ta haramta shan sigari a cikin jama’aAmbaliyar ta yi rusa da gidaje sama da 50 tare da sanye murare da dama.
Tun da farko kakakin Hukumar NSEMA, Ibrahim Audu Husseini, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “akwai yiwuwar yawan mutanen da suka mutu da sauran asarar da aka yi za su ƙaru, saboda akwai masu aikin ceto a wurare daban-daban.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas
Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta ce ma’aikatanta hudu sun mutu a gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad da ke Legas, a ranar Talata.
Aminiya ta rawaito yadda gobara ta mamaye ginin da ke dauke da banki, hukumomi da wasu kamfanoni.
Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun Shugaban FIRS, Zaach Adedeji, wato Dare Adekanmbi, ya ce hukumar na cikin jimami da alhini kan rasuwar ma’aikatan nata.
Sanarwar ta ce, “Cike da alhini da bakin ciki, FIRS na sanar da rasuwar ma’aikatanta hudu a gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad, Legas, a ranar Talata. FIRS na daya daga cikin masu haya a ginin, inda Ofishin Binciken Matsakaicin Haraji da Ofishin Haraji na Onikan ke a bene na shida da na bakwai.”
“Jami’an tsaro da na kula da lafiya na hukumar sun gaggauta tuntubar hukumar kashe gobara lokacin da aka sanar da su. Amma da suka isa wurin, hayaki mai kauri da duhu ya turnuke ginin.”
“Hukumar da dukkan ma’aikatanta na cikin alhini kan wannan lamari. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasu, kuma muna tare da su a wannan lokaci mai wahala. Za mu ba su dukkan goyon baya da tallafi da ake bukata.”
“Muna aiki tare da dukkan hukumomin da suka dace a Legas domin gano musabbabin wannan mummunan al’amari. A yayin da ake ci gaba da bincike, za mu duba matakan kiyaye lafiyar dukkan ofisoshin FIRS da ke fadin ƙasa, ko na haya ne ko wanda ta mallaka.”