Kwararran likita tiyata, Farfesa Sani Ali Aji ya bayyana cewa kwarrun likitocin tiyata guda 6 ne kacal suka rage a Jihar Kano, wanda ake has ashen tana da al’umma fiye da miliyan 20.

Farfesa Sani ya kara da cewa wannan karanci na likitoci ya faru ne sakamakon karancin albashi, karanci kayan aiki na zamani da sauransu, wanda hakan ya sa kwararrun likitoci suka koma kasashen Turai da na Larabawa domin samun alfashi mai tsoka.

‘Yansanda Sun Kama Mutane 41 Da Ake Zargi Da Kisan DPO A Kano Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kano

Ya bayyana cewa maganin wadannan matsaloli shi ne, samar da kayan aiki wadatace da albashi ga ma’aikata mai tsoka da sauransu.

Farfesa Sani ya bayyana hakan ne a wurin wani taron samar da kwararrun likitoci, wanda ya gudana a Jihar Kano. Ya ce an saba gudanar da irin wannan taro a kasar Mali, sai dai a bana an gudanar da taron ne a Jihar Kano, wanda ya sama damar halartar dimbin masana harkokin lafiya da sauran al’umma.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Farfesa Sani

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala

Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta.

Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin, da su bayyana a gabanta cikin sa’o’i 24.

Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu

Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɓullar wata muhawara da aka yi tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi kuma ta karade shafukan sada zumunta, wacce hukumar ta bayyana a matsayin karya dokokin aikinta.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan ranar Talata, inda ya ce ɗaukar matakin wani yunƙuri ne na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bin doka tsakanin mawaƙan nishaɗi da na addini.

El-Mustapha, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya kuma ce an haramta duk wata nau’in muƙabala daga mawaƙan addini a jihar ba tare da izinin hukumar ba.

A yayin da yake ƙaddamar da wani kwamitin bincike da shugaban hukumar ya naɗa karkashin Daraktan Ayyuka na Musamman a hukumar, Isah Abdullahi, El-Mustapha ya umarci waɗanda aka gayyatar da su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.

Hukumar ta ce shirya irin waɗannan muhawara ba tare da izininta ba ya saɓa doka kuma zai iya jawo hukunci mai tsanani ga wanda suka karya.

Hukumar ta kuma jaddada ƙudirinta na ci gaba da kula da ayyukan mawaƙan da masu nishaɗantarwa a faɗin jihar tare da yin kira ga jama’a da su zauna lafiya sannan su ci gaba da ba ta haɗin kai a ayyukanta.

Yadda aka yi muƙabala tsakanin Shehi Tajul Izzi da Maidubun Isa

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • An Karrama Farfesa Adamu Gwarzo Kan Gudummawarsa Ga Bunƙasa Ilimin Jami’a A Nijeriya
  • Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja