NAJERIYA A YAU: Tasirin Dangantakar Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan Talaka
Published: 26th, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma.
A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci-gaban kasa.
Sai dai a Najeriya, a wasu lokutan akan zargi ’yan majalisa da zama ’yan-amshin-Shata.
Ko me ya sa haka? Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya?
NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu”Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Majalisar Dokoki Majalisar Zartarwa
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria