Fasahar Shayi Ta Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankali Da Nishadi Ga ‘Yan Nijeriya
Published: 26th, May 2025 GMT
Baki a Nijeriya da abokansu Sinawa sun nishadantu yayin da suka halarci taron gabatar da fasahar hada shayi ta 2025 da al’adun Yaji, wanda aka yi jiya Asabar a Abuja babban birnin kasar. An gudanar da taron ne a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin da hadin gwiwar cibiyar raya al’adu ta lardin Zhejiang, wadda ta samu wakilcin masana hada shayi da ‘yan wasan kwaikwayo na Yue Opera da masu wasan kayan Pipa.
Taron ya samu halartar mutane daga dukkan bangarorin rayuwa da suka hada da jami’an diplomasiyya da na gwamnati da malamai da daliban sakandare da ‘yan wasa da manema labarai da masoya al’adun shayi ta kasar Sin. An kuma gabatar da fasahar rubutun gargajiya ta Sin da zanen fenti da hotunan dake bayyana al’adu da wuraren bude ido na Zhejiang. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babu Wanda Ya Buƙaci Atiku Ka Da Ya Yi Takara A 2027 – ADC
Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici , musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke FluminenseJam’iyyar ta ce: “Ba mu taɓa zama da wasu wakilai daga Kudu domin yin irin wannan magana ba.
“Wannan rahoto ba kawai ƙarya ba ne, yana kuma iya haddasa rikici da rashin fahimta tsakanin ‘yan Nijeriya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp