Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (3)
Published: 31st, May 2025 GMT
Karatu, rubutu,da kuma dabarun lissafi wasu dabaru ne da ake samu ta hanyar iulimi. Wadannan dabarun suna bada dama ta dogaro da kai da kuma samarwa kai aiki.
Karatu yana bude hanyar sanin ilimi da labarin duniya. Saboda mutane suna fara kasuwanci ne idan har za su iya kasafi,da kuma gane abubuwan da aka kashe a kalla.
Ilimin iya karatu da rubutu,da kuma iya samar da hanayar da za aji ra’ayoyi,hakan na kara iya dogaro da kai da kuma samun a rika jin babu wata kasala ko faduwar gaba.
Ilimi yana taimakawa mutane wajen yadda wasu daga zama Sanuwar ware.
Yin makaranta yana koyawa mutane duk wani matakin da za su dauka ya kasance mai ma’ana, wannan kuwa yana sa su shirya lamarin zama matasa,da kuma cikakken mutum, inda duk wani matakin da za’a dauka kowace rana, babba, ko karami zai kasance wani bangare ne na rayuwar su matasan.
Gwargwadon ilimin mutum gwargwadon irin kudin albashin da zai samu.Idan aka samu ilimi maiinganci sau da yawa ko mafi akasari ya kan yi sanadiyar samun aikin da za a rika biyan albashi mai tsoka,da samar da wasu dabaru da suka zama da’iman suna da muhimmanci.
Yana samar da hanyar rayuwa mai sauki, wadda babu wanda ya isa ya dauka elamarin daga wurin kai mai ilimin,. Idan muna da ilimi,wani abu ne wanda namu ne kadai,wanda hakan yana bamu damar mu tsaya da kafafunmu.
Ilimi yana koyawa mutane yadda za su yi tunani sosai har ila yau kuma a cikin tsari,bayanan kuma su yi alkalanci mai hujja ba tare da shawara da wani ba.Matsalolin da ake iya fuskanta idan an fara/ko anyi girma sunesun hada da biyan basuksukan da aka dauka lokacin makaranta,samun aikin yi,sayen gida,da kuma iaya daukar dawainiya ko nauyin iyali.Wadanda suka yi shekaru suna makaranta/karatu,irin su,suna iya yin tunani ko daukar matakai wadanda zasu taimaka masu wajen su matsalolin da aka bayyana.
Abin ya danganta ne ga irin burin da mutum yayi niyyar cimmawa, idan aka yi karatu mai zurfi sosai, yana taimakawa wanda ya yi karatun cimma dukkannin abubuwan da yasa a gabansa.
Ilimi yana kara rayuwa mai tsawo saboda nazarin da aka yi ya nuna kowace shekarar ilimi, ilimi yana kara shekara 1.7 ga mutane lokacin da suka kai shekara 35 cewar.(Lleras-Muney, 2005)
Ilimi yana da matukar muhimmanci ga ci gaban Dan Adam.
Ilimi yana taimakawa mutane su gane ko su, su wanene. Suna iya sanin kansu ta hanyar Littattafai, kwasa- kwasai, har ma da irin shawarar da kwararru.
Ilimi yana bada damar yadda mutane za su san duniya abinda ake ciki,sai kuma su wanene kusa da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyen Katsina, Sun Jikkata Mutane 2, Sun Sace Wasu
“Sun jikkata mutane biyu tare da sace maza, mata da yara da dama.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp