Gaza : EU ba ta gamsu da sabon tsarin raba agaji na Amurka da Isra’ila ba
Published: 28th, May 2025 GMT
Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza.
Babbar jami’ar diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta bayyana cewa Tarayyar Turai ba ta goyon bayan sabon tsarin raba agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke kokarin aiwatarwa wanda ke kaucewa hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji.
Kallas, ta kuma bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza sun wuce abun da suke bukata wajen yakar Hamas, a yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ke ci gaba da karuwa.
Tun bayan da Isra’ila ta dawo da yaki a watan Maris bayan ruguza yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da Hamas, kimanin mutum 3,924 ne sukayi shahada a cewar ma’aikatar lafiyar a Gaza.
Isra’ila dai ta ci gaba da cewa tana kai hare-haren ne don kawar da Hamas da ceto wadanda kungiyar ke garkuwa da su.
Sai dai hare-haren kwanan nan sun yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.
Jawabin Kallas ya biyo bayan kalamman da Firaministan Jamus, Friedrich Merz, ya yi, inda ya bayyana cewa “a yanzu ba ya fahimtar manufar Isra’ila a Gaza.”
Isra’ila dai ta fara kai farmaki a Gaza ne bayan harin ba zata na Hamas a ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 1,200 da kuma sace wasu 251, sai kuma mutane sama da 54,084 a hare-haren ramuwar gayya na Isra’ila.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila
Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu.
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan ‘yan gwagwarmaya da kuma fitattun al’umma da masanan Falasdinawa, biyan ladar moro-maron yahudawan sahayoniyya ne da jami’an hukumar Falasdinu suka ci.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ruguza gidajen mutane a Jenin, tare da koran dubban mutane a Tulkarm, ana kuma kwace yankunan mutane a gabar yammacin kogin Jordan.
Shadid ya bayyana cewa: Wadannan ayyuka suna nuna manufar Hukumar Cin gashin Falasdinawa ne na ganin ta raba ‘yan gwagwarmaya da yankin gabas yammacin kogin Jordan, tare da barin Falasdinu a bude ga sojojin mamayar Isra’ila gungun ‘yan ta’addan su aiwatar da tsare-tsaren Sanya Falasdinawa gudun hijira.