Nigeria: Mutane Da Yawa Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Harin Makiyaya A Jihar Benue
Published: 28th, May 2025 GMT
Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42.
Mahukunta a yankin sun sanar da cewa; an gano gawawwakin mutane 32 da aka kashe sanadiyyar harin da aka kai kauyukan Ahume da Aodona, yayin da aka gano wasu gawawwakin mutane 10 a kauyukan Tyolaha, Tse-Ubiam, kamar yadda shugaban karamar hukuma Gwer ta yamma Victor Omnin ya bayyana.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana wa ‘yan jarida abinda ya faru da cewa; na takaici ne, domin a wannan lokacin da muke Magana ana ci gaba da gano gawawwaki.”
Jahar Benue tana tsakiyar kasar Nigeria ne a yankin da ake kira : Middle-Belt”. An kuma dauki shekaru masu tsawo ana riciki a tsakanin makiyaya da manoma akan kasa saboda rushewar tsarin burtali.
Ofishin Gwamnan jihar ta Benue Hyacinth Lormem Alia, ya kuma sanar da cewa daga cikin wadanda aka kai wa hari da akwai malamin addinin kirista,amma yana a raye.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara
Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna
Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya
Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.
Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina
ShareTweetSendShare MASU ALAKA