Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Yankin Zirin Gaza
Published: 30th, May 2025 GMT
A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan ya biyo bayan sauya ra’ayi da Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bisa la’akari da goyon bayan siyasa da na soji da Amurka ke ba shi, a cikin shiru da kasashen duniya suka yi da kuma gazawar da ba a taba gani ba daga kungiyoyin kasa da kasa.
Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da jerin hare-hare ta sama kan yankunan Gaza, da nufin tsaurara tasirin hana shigar da kayan abinci da ya karu tun farkon watan Maris. Wannan ya ba da mummunan hoto na yunwar da mazauna Gaza ke fuskanta.
A safiyar yau Juma’a, jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da wani mummunan farmaki kan yankunan kudancin Khan Yunus. Kamar yadda sojojin na Isra’ila suka yi luguden wuta kan sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke arewacin zirin Gaza da kuma arewa maso yammacin Rafah.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne
Jami’in harkar shari’ar kasa da kasa ya bayyana cewa: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhu
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya ce: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne, kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.
A yayin wani taron manema labarai da ya yi da wakilan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya fiye da 110 a birnin New York na kasar Amurka a jiya Litinin, Gharibabadi ya bayyana ma’auni na wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauka kan yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma sakamakonsa ga zaman lafiya da tsaro a duniya.
Ya dauki gwamnatin yahudawan sahayoniya a matsayin babbar mai haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a yankin cikin shekaru 80 da suka gabata, yana mai jaddada cewa: Wannan ita ce gwamnatin da ya zuwa yanzu ta aiwatar da ayyukan ta’addanci sama da 3,000, tare da raba Falasdinawa sama da miliyan bakwai da muhallansu, da kashe dubban daruruwan Falasdinawa, tare da kame Falasdinawa sama da miliyan guda.