Ko Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Trump Ya Gujewa Yaki Da Yemen Har Ya Kai Ga Fusata Kawayen Amurka
Published: 27th, May 2025 GMT
Gujewar da Trump ta yi daga yakin Yemen ya harzuka mahukuntan gwamnatin Isra’ila da kasashen Larabawa da suka dogara da shi
Shafin Jaridar Hill ta Amurka ta buga wani sabon labarin da ke bayyana irin kayen da Amurka ta sha a Yemen da kuma irin dimbin hasarar da Amurkan ta yi domin kare yahudawan sahayoniyya kafin ficewa daga kangin matakin martanin kasar Yemen.
Labarin da Imran Khaled ya rubuta mai taken “(Al’ummar Yemen) sun yi tsayin daka da kuma ja da baya da Trump ya yi… Shin Amurka za ta fice daga Yemen?”, yarjejeniyar “dakatar da kai hare-haren wuce gona da irin Amurka kan Yemen” ta bayyana yadda Amurka ta yin watsi da kawayenta cikin sauki, wanda ke nufin gwamnatin ‘yan sahayoniya.
Ya yi nuni da cewa: Barin harin wuce gona da iri kadai a gaban ci gaba da ayyukan Yemen, yana kara karfafa labarin kasar Yemen da suke gabatar da tallafi da taimako a kodayaushe ga gwamnatocin Larabawa da na Musulunci, da hakan ke fayyace cewa Amurka ba abar dogaro ba ce, kuma cikin sauri ta yi watsi da “kawayenta” wanda hakan ya faru a zahiri bayan ficewar Amurka daga “yakin kare yahudawan sahayoniyya”.
Ya bayyana cewa: Mai laifi Trump ya kwatanta mutanen Yemen a matsayin jarumai da masu juriya, bayan da a baya ya yi barazanar “murkushe su baki daya” ya nuna cewa shugaban na Amurka ya mika wuya tare da ayyana shan kaye, amma yana shelanta cewa ya yi nasara, yana mai jaddada cewa sakamakon yakin ya tabbatar da rashin nasara ga Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.