Sojojin HKI Sun Yi Wani Sabon Kisan Kiyashi A Gaza
Published: 26th, May 2025 GMT
Hare-haren sojojin HKI a yankin Gaza sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 57
Majiyar Asibiti a yankin na Gaza,ta sanar da cewa sojojin mamayar sun kai hari ne akan makarantar ” Fahmi al-jarjawi” wacce take a yankin al-Darj’ a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 25.”
Harin ya yi sanadiyyar konewar gawawwakin shahidan da kuma tashin gagarumar gobara a makarantar da ‘yan hijira Falasdinawa suke ciki.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa ya haura dubu 53 da 939.
Haka nan ma’aikatar ta ce; Wadanda su ka jikkata kuwa a wannan tsakanin sun kai dubu 122 da 797.
Sojojin HKI sun shelanta yaki ne akan yankin Gaza da zummar murkushe kungiyar Hamas, sai kuma kwato fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya, lamarin da ya zuwa yanzu babu wanda ya tabbata.
Daga farkon yakin ne dai kungiyar Hamas ta sanar da cewa, ta hanyar tattaunawa ne kadai za a iya yin musayar fursunoni.
Ya zuwa yanzu kuwa an yi musayar fursunonin a tsakanin bangarorin biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.