2025-06-26@15:40:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6043

«gudanar da aikin»:

    An harbe wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne a ranar Talata a yayin wani artabu da jami’an tsaro suka yi a unguwar Makera da ke Kakuri a Jihar Kaduna. Rundunar ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin tare da ƙwato tarin makamai da kayayyaki masu daraja da aka sace daga mazauna garin. An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja A cewar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 3:10 na tsakar dare, inda wasu ’yan bindiga 8 suka kai hari a rukunin gidaje na Estate...
    Yawan gawarwakin da aka tsinta bayan harin duk na mabiyansa ne. Ɗaya daga cikin su, Bashari Maniya, wanda tsohon ɗan bindiga ne da ya ce ya tuba kuma ya fara taimaka wa jami’an tsaro, shi ma ya mutu bayan motar da yake ciki ta faɗa rami mai zurfi. Manga ya bayyana cewa ba da bindiga aka kashe Maniya ba, saɓanin jita-jitar da ke yawo. “Sabuwar mota ce, kuma ba su san dajin sosai ba. Yayin da suke gudu a cikin daji, sai suka faɗa cikin wani rami mai zurfi. Motar ta kife, kuma an kasa ciro ta cikin sauƙi,” in ji shi. Ya ce lokacin da aka zo taimaka musu, an same su a cikin motar a sume. Motar ba...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ​​’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki. Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu. Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan ne manema labarai a hedikwatar rundunar da ke garin Maiduguri. Kwamishinan ’yan sanda, CP Naziru...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ​​’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki. Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu. Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan ne manema labarai a hedikwatar rundunar da ke garin Maiduguri. Kwamishinan ’yan sanda, CP Naziru...
      Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin.   Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana su a matsayin jarumai na kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da ‘yancin Nijeriya.   Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu, yana mai addu’ar Allah ya kara musu lafiya, ya basu hakurin juriya da irin wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    An kama daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutum uku a ƙauyen Daku da ke Gwagwalada Abuja lokacin da yake tsaka da cin kasuwar shanu ta Izom da ke Guraran jihar Neja. Rahotanni sun ce a ranar tara ga watan Yunin 2025 ce dai aka sace wasu makiyaya su biyu da wani direba a kusa da kauyen na Daku. An sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Izom. ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir Mutanen da aka sace ɗin dai a wancan lokacin sai da suka biya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi. Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau An yi jana’izarsu a ranar Talata a Babban Masallacin Abuja, inda manyan jami’ai suka halarta, ciki har da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. An birne su a maƙabtar Gudu, inda Ribadu da Gwamna...
    Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro,  Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa, maharan sun kashe mazauna yankin da dama, tare da hana ayyukan noma, da kuma haddasa durkushewar ayyukan kasuwanci na yau da kullum a yankin. “Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga karkashin jagorancin babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara, jihar Katsina. An hana noma daga Marabar Kankara zuwa ‘Yantumaki, an kashe mutane da dama, an yi garkuwa da wasu, kiwon lafiya ya durkushe. Mazauna garin...
    Gwamnatin Jihar Neja, ta rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai saboda matsalolin tsaro da suka janyo mutuwar wasu ɗalibai. Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata. Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi Gwamna Umaru Bago ya amince da rufe jami’ar nan take, kuma za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sauyi. “Lafiyar kowa, musamman ɗalibai da malamai, na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatin Jihar Neja,” in ji sanarwar. “Mun yi matuƙar baƙin ciki da abin da ya faru, kuma muna ɗaukar matakan...
    Ɗaya daga cikin baƙin da suka tafi ɗaurin aure daga Zariya, Abbas Rufa’i, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga harin da wasu matasa suka kai musu a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato. A cewarsa, “Da muka tsaya a hanya domin yin tambaya, na fito daga motar domin neman hanya. Amma sai na ga yadda mutanen da ke wajen suka fara mana wani irin kallo. Gwamnatin Gombe za ta sayi takin N8.8bn don tallafa wa manoma 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi “Na ji ɗaya daga cikinsu yana cewa, ‘a kashe su gaba ɗaya, a ƙone motar.’” Rufa’i ya ƙara da cewa, “Na cire rigata, na shiga cikin daji har na sai da na samu...
    Majiyoyi sun kuma ce “an kashe adadi mai yawa na ‘yan bindigar”.   Shugaban karamar hukumar, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya ce harin ya kara firgitar da manoman yankin.   Ya ce taimakon gaggawa daga barikin soji na Kontagora ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa zuwa dazuka.   Ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu, sun farfasa shaguna tare da kwashe kayan abinci da kayayyaki masu daraja a shagunan mutanen yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ƙoƙarinta na bunƙasa noma da samar da isasshen abinci, Gwamnatin Jihar Gombe ta amince ta sayi tan 10,000 na taki, wanda ya yi daidai da buhu 200,000 domin shirin noman daminar bana. Kwamishinan Harkokin Noma na Jihar, Dokta Barnabas Musa Malle, ya ce za a kashe Naira biliyan 8.8 wajen sayen takin. 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau Ya ce hakan na nuna yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tallafa wa manoma da kuma ƙara samar da abinci a jihar. Dokta Malle ya ce, “Gwamnati ta fito da sabbin hanyoyin aiki sama da yadda aka yi a baya, kuma za a raba...
    Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ce ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba a zaben 2027 matukar ya canza Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa. Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wa’azi a masallacinsa na ’Yan Taya da ke Jos, babban birnin jihar Filato. Aminiya ta rawaito cewa a zaben 2023 da ya gabata dai Sheikh Jingir ya goyi bayan Tinubu sannan ya umarci magoya bayansa da su ma su yi haka a wancan lokacin. Gwamnatin Kano ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump Jita-jitar da ake yadawa dai a kan cewa akwai yiwuwar Tinubu...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.   Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su. Sai dai a wannan zamani ‘yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikin su ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita. Ko wadanne matakai ya kamata ‘yan Najeriya su ringa dauka wajen kare kan su da ma lafiyar jikin su? NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin...
    Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a matsayi na uku a teburin, inda ta rasa gurbi a gasar cin kofin zakarun yankin Asia na shekara mai zuwa kuma a maimakon haka za ta buga gasar AFC Champions League 2.   Bugu da kari, Al Nassr a halin yanzu ba ta da koci tun bayan da ta raba gari da babban kocinta Stefano Pioli a ranar Laraba, wanda ya zama koci na uku...
    “Na yi aiki a kamfanin NNPC kuma na tafi da mutuncina, babu wanda ya zarge ni da wata zamba a tsawon zamana a Kamfanin, mutanen da ke yada wannan labarin na karya na kamawa da tsare ni kawai suna haka ne domin son su bata min suna.”   Mista Ajiya ya ce a shirye yake a kowanne lokaci don kare martabarsa da kuma tsawon shekaru da ya yi a hukumar ta NNPC, inda ya ce, “Ina kasar nan kuma a kowacce rana da kuma duk lokacin da EFCC ta bukaci na bayyana a gabansu zan zo”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Mozambique Daniel Francisco Chapo, suka mikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu. A cikin sakonsa, shugaba Xi ya bayyana fatansa na kara hadin gwiwa da Chapo, a fannin yayata dadadden zumuncinsu bisa wannan zarafi mai kyau, da kuma zurfafa hadin gwiwarsu bisa tabbatar da ingantacciyar shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da sauransu. A nasa bangare, Chapo ya ce, kasarsa na fatan zurfafa huldar bangarorin biyu, bisa tushen mutunta juna, da samun ci gaba da cin moriya tare, da kuma habaka hadin kai, da kiyaye tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da sauran al’ummar Kano da su yi amfani da wannan dama wajen yin tunani a kan ayyukan da suka yi a cikin shekarar da ta gabata, tare da yin addu’o’in zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a jihar da kasa baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan kasar Sin Li Qiang ya ce, kasarsa a shirye take ta rarraba fasahohinta na ainihi, da dabarunta na kirkire-kirkire tare da sauran sassan kasa da kasa. Li Qiang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na bude taron shekara-shekara, na sabbin jagorori karo na 16, wato dandalin tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos a takaice, wanda aka bude yau Laraba a birnin Tianjin na kasar Sin. Li ya kara da cewa, Sin na da karfin gwiwa, da ikon wanzar da ci gaban tattalin arzikinta, tana kuma kara kaimin zama kasa mai babban matsayin samun kudin shiga, yayin da ake kara daga matsayin sayayya bisa kyakkyawan yanayi a kasar, wadda ita ce ta biyu a girman kasuwar sayayya a...
    Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Borno (PPRO), Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, ta ce an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na jihar da ke Maiduguri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan ƙasarsa za su gana da na Iran domin ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyarta a mako mai zuwa. “Za mu tattauna da Iran a mako mai zuwa, ƙila mu ƙulla yarjejeniya ko kuma akasin haka, ba na ce ba,” in ji shi yayin jawabinsa a taron ƙasashe na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO da ake yi a ƙasar Netherlands. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano “Ba su daɗe da gama yaƙi ba, yanzu za su ci gaba da harkokinsu. Ban damu dole sai na ƙulla wata yarjejeniya da su ba,” a cewarsa. A jiya Talata...
    A yanzu haka, fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI na sauya zaman rayuwar dan Adam. Ga misalin, motoci mara matuki na saukaka tafiye-tafiye na dan Adam, samfurin binciken yanayi na iya hasashen hanyar guguwa a cikin dakika 10 kawai… Amma, fasaha ta zama kamar “takobi mai kaifi biyu”, wadda a lokaci daya take kuma kara haifar da matsaloli, kamar su fallasar sirri, yaudara ta hanyar amfani da AI, da hadarin rashin aikin yi. Bisa wannan yanayin da ake ciki na kasancewar alfanu‌ da ‌matsaloli tare, ‌’dan Adam na bukatar hadin gwiwa cikin gaggawa don daidaita ci gaban fasahar AI, da kafa tsarin gudanar da harkokin fasahar AI na duniya, da nemo daidaito tsakanin kirkire-kirkire da tsaro, da nufin tabbatar...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun kashe ’yan fashi biyu, sannan sun kama wasu biyu a unguwar Makera da ke Kakuri. Wannan ya biyo bayan musayar wuta da jami’an tsaro suka da ’yan fashin. Gwamnan Nasarawa ya sanya wa gadar sama sunan Tinubu PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:10 na dare, bayan da suka samu kiran gaggawa daga mazauna unguwar Gashash a Barnawa. Rahotanni sun ce ’yan fashi guda takwas sun shiga wani gida ɗauke da bindigu da makamai, sun sace wayoyi, kwamfutoci da sauran kayayyaki. Bayan kiran gaggawar, DPO na Barnawa, Kakuri da Sabon Tasha tare da sojoji daga Rundunar 312 Artillery...
      Wasu jihohin da suka hada da Benuwe, Filato, da Borno, a ‘yan kwanakin nan sun samu tabarbarewar tsaro, lamarin da ya sa sojoji da sauran jami’an tsaro suka kara zage damtse wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da kalubalen tsaron ke kara ta’azzara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yaya girman neman fadadar kungiyar NATO yake? Alkaluma ne za su iya fayyacewa: Abun da aka kashe a duniya kan aikin soji a shekarar 2024 ya kai dala triliyan 2.72, inda kungiyar NATO ta dauki dala triliyan 1.5, wato kaso 55 na jimillar ta duniya. Duk da rashin daidaiton karfin soji tsakanin kasashen duniya, NATO na ci gaba da sanya mambobinta su kara abun da suke kashewa a bangaren tsaro zuwa kaso 5 na alkalumansu na GDP. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ya nuna cewa, kaso 67.4 na wadanda suka bayar da amsa sun yi tir da yadda NATO ke gaggauta fadada karfinta na soji, suna gargadin hakan ka iya haifar da sabuwar takarar makamai da yin gagarumar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanya wa sabuwar gadar sama da aka kammala a Lafia, Babban Birnin Jihar, sunan Shugaba Bola Tinubu. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da aikin a Lafia. ’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano Ya ce an gina gadar bisa tsarin Shugaba Tinubu, kuma an kammala aikin ne ba tare da ciyo bashi ba, sakamakon inganta amfani da kuɗin gwamnati. Sabuwar gadar mai tsawon kilomita ɗaya, wadda ke da gadar sama da ƙasa, na ɗauke da sunan ‘Bola Tinubu Exchange Road’. A wajen buɗe aikin, Shugaba Tinubu ya gode wa Gwamna Sule bisa jajircewarsa...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna. An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta A cewar wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin, motar ‘yan sandan na bin wata mota ƙirar Golf kafin a ji ƙarar harbe-harbe. Nan take mutane suka fara kwanciya a ƙasa domin tsira da rayukansu. Wannan...
    Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja. Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano Damagum ya kuma bayyana cewa an soke taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100 da aka shirya yi, saboda wasu matsaloli. Maimakon haka, jam’iyyar za ta gudanar da wani taro a ranar 30 ga...
    Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 120, bisa samun su da laifin satar yara da kuma sayar da su. Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha, da Chinelo Ifedigwe. PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta An same su da laifin ɓoye bayanai, taimakawa wajen aikata laifi, satar yara da kuma safarar su. An sace yaran ne daga Kano, sannan aka sayar da su a garin Onitsha da ke Jihar Anambra. Shugaban tawagar, Paul Onwe, tuni aka yanke...
    Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta mayar da na hannun damar Ministan Abuja Nyesom Wike, wato Samuel Anyanwu kan kujerarsa ta Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Mai riƙon muƙamin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Iliya Damagum ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba. Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara Yayin taron dai, shugaban na tare da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. Damagum ya ce yanke shawarar dawo da Anyanwu cikin kwamitin zartarwar jam’iyyar na ƙasa shawara ce mai...
    Gwamnan ya buƙaci kamfanin da ke aikin da ya yi aiki mai kyau kuma ya kammala a kan lokaci. Ya ce dole ne a gina gidajen cikin inganci domin taimakawa wajen rage matsalar rashin gidaje da jama’a ke fuskanta a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yanzu sun sake nuna sha’awarsu, suna fatan ɗaukar ɗan wasan mai shekaru 28. Manchester United ma ta nuna sha’awar ɗaukar Ndidi idan har ta sayar da Casemiro, wanda ake raɗe-raɗin zai koma Saudiyya. A watan Janairu, Monaco da ke gasar Ligue 1 ta yi ƙoƙarin ɗaukar Ndidi, amma Leicester ta ƙi amincewa. Hakazalika, akwai ƙungiyoyi daga Saudiyya da ke son ɗaukarsa kuma suna shirin ba shi albashi mai tsoka, amma Ndidi yafi son ci gaba da buga wasa a Turai. Ndidi ya koma Leicester City a watan Janairun 2017 daga kulob ɗin Genk na Belgium. Ya lashe kofin FA Cup da Leicester a 2020, kuma ya zura ƙwallaye 11 a cikin wasanni 252 da ya buga wa ƙungiyar cikin shekaru...
    Daya daga cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi. Bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashe din har da wasu jami’an hukumar tsaro ta DSS su hudu da kuma wani tubabben dan bindiga da yanzu yake aikin bayar da bayanai ga jami’an tsaro, Bashar Maniya. Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya. Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027 An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a...
    Jaridar LEADERSHIP ta kuma ruwaito cewa rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta taɓa gargaɗin masu ɗaukar bidiyo da su daina tare hanya da sunan yin fim. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daya daga cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi. Bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashe din har da wasu jami’an hukumar tsaro ta DSS su hudu da kuma wani tubabben dan bindiga da yanzu yake aikin bayar da bayanai ga jami’an tsaro, Bashar Maniya. Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya. Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027 An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a...
    A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba. Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin. Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori. Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13. Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto.   Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet.   “A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki.   “Amma abin ya ba mu...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar damuwar da Sin ke da ita dangane yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, tare da bayyana fatan ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran nan bada jimawa ba. Guo Jiakun ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake tsokaci game da rahotannin dake cewa shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa an cimma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran. Kakakin ya kuma nanata cewa shaidu sun riga sun nuna cewa, matakan soji ba za su kawo zaman lafiya mai dorewa ba, kuma yarjejeniya da tattaunawa su ne kadai hanyoyin warware rikice-rikice. Ya kara da cewa,...
    Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar, Abdullahi ya nuna matukar damuwarsa kan kisan da aka yi wa matafiyan a ranar Juma’a, a lokacin da suka bata kan hanyarsu a yayin da suke tafiya don halartar wani daurin aure a karamar hukumar Mangu.   Ya ce, wadanda aka kashen, ba su dauke da wani makami, kawai suna kan hanyarsu ne ta zuwa daurin aure, wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai musu hari tare da kashe su, lamarin da ya jefa ‘yan uwan matafiyan cikin jimami. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Gwamnatin Nijeriya ta ce babu wata barazanar tsaro a babban birnin ƙasar, Abuja, inda ta yi kira ga mazauna birnin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana. Nijeriya ta musanta batun yiwuwar kai hari kan ’yan Amurka da suke zaune a kasar, sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta Gwamnatin ta bayyana haka ne a matsayin martani dangane da gargaɗin tsaro da Amurka ta aika zuwa ga ’yan ƙasarta da ke birnin Abuja. A sanarwar da Ministan Watsa Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris ya fitar, ya ce, “Gwamnatin Nijeriya ta samu labarin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Mali, Assimi Goita da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Wannan dai na cikin wasu yarjejeniyoyi da Mali da Rasha suka rattaba hannu waɗanda aka tsaro domin inganta alaƙar kasuwanci da tattalin arziki. Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya Shugaba Vladimir Putin ya shaida wa shugaban kasar ta Afirka ta Yamma da ke ziyara cewa akwai wasu fannoni na musamman da za a iya ƙara haɗin kai. Putin ya karbi bakuncin Kanal Assimi Goita a fadar Kremlin, inda suka tattauna tsawon awanni biyu, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati...
    Majalisar ministocin harkokin waje ta kungiyar kasashen musulmi (OIC), ta gudanar da taronta na 51 daga ranar 21 zuwa 22 ga watan nan. Taron ya tabbatar da kokarin Sin na kare al’ummar musulmi tare da yaba wa ci gaban da aka samu na dangantaka tsakanin Sin da kasashen musulmi da kuma sa ran kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyar OIC da kasar Sin. Da yake tsokaci kan hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jian kun, ya ce a ’yan shekarun nan, Sin da kasashen musulmi da ma kungiyar OIC, sun ci gaba da zurfafa aminci a tsakaninsu da fadada hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban da karfafa musaya tsakanin al’ummominsu tare da samun kyawawan sakamako. Ya ce Sin za ta...
    Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Jibrin Barau, ne ya sanar da kudirin bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan samar da kayayyaki.   Adeola ya ce, karin wa’adin ya zama dole domin baiwa gwamnatin tarayya damar kammala wasu manyan ayyuka da suka samu jinkiri sakamakon karancin kudaden shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1447 daga gobe Laraba, 29 ga watan Zulhijjan 1446, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yulin 2025. Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai. Harin asibiti ya kashe mutum 40 a Sudan — WHO EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanar wa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi. A ƙarshe sanarwar ta ce...
    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sama da mutane 40 ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya aka kashe a harin da aka kai wani asibiti da ke Sudan a ƙarshen mako. Ofishin hukumar ta WHO da ke Sudan, ya ce daga cikin waɗanda suka mutu akwai ƙananan yara shida da jami’an kiwon lafiya biyar, sannan kuma an yi wa ginin asibitin mummunar ɓarna. EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn Yarjejeniyar tsagaita wutar Isra’ila da Iran ta samu tasgaro RFI ya ruwaito cewa an dai kai harin ne kan Asibitin Al Mujlad da ke a yammacin Kordofan a ranar asabar da ta gabata, kusa da inda ake fafatawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, a yaƙin...
    Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta tsare wasu tsofafin manyan jami’an Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) kan zargin badakalar kudade da yawansu ya kai Dala biliyan 7.2. Jami’an EFCC sun tsare tsohon Babban Jami’in Kudi na NNPCL, Umar Ajiya Isah da kuma tsohon Manajan-Daraktan Matatar Mai ta Warri, Jimoh Olasunkanmi, kan zargin almundahanar. Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a boye sunansa ya ce hukumar ta tsare tsoffin manyan jami’an na NNPC ne kan zargin wadaka da kudaden gyaran matatun mai da ke Kaduna da Warri da kuma Fatakwal. Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga kakakin EFCC, Dele Oyewale, amma jami’in bai amsa duk kiraye-kirayen da aka yi masa da kuma rubutattun sakon...
    Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya zargi Iran da Isra’ila da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta. Da yake jawabi kafin tafiyar Babban Taron Ƙungiyar NATO, da zai gudana a birnin Hague, Trump, ya bayyana takaicinsa bisa yadda kasashen biyu game da saɓa yarjejeniyar, sa’o’i kaɗan bayan sun amince da ita. Tun da farko sai da ya buƙaci Isra’ila ta janye shirinta na kai wa Iran hari. A safiyar Litinin bayan sanarwar Trump cewa ɓangarorin sun amince su tsagaita wuta ne, Ministan Tsaron Isra’ila ya yi barazanar kai wa Iran hari mai tsanani bayan zargin ta da harbo wa ƙasarsa rokoki. Iran ta musanta zargin tare da cewa Isra’ila za ta yaba wa aya zaƙi idan kuskura ta kawo mata hari. Daga...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, shugaban kasar Xi Jinping, zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, da safiyar ranar 3 ga watan Satumban bana, tare da gabatar da jawabi. Kazalika a ranar, kasar Sin za ta gudanar da gagarumin bikin faretin soja a filin Tian’anmen dake nan Beijing, inda shugaba Xi zai duba faretin. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar 23 ga wata, Kirsty Coventry, wacce ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics ta kasa da kasa kwanan nan, ta yi hira ta musamman da wani shirin gidan talabijin na CCTV mai lakabin “High-End Interview” a birnin Lausanne na kasar Switzerland. Wannan ita ce hira ta farko da ta yi da kafar yada labarai tun bayan da ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics na duniya. Coventry ta ce ya zama wajibi a kiyaye kima da kuzarin wasannin motsa jiki na Olympics, tare da kara kiyaye su da kuma karfafa su. Ta ce, tana fatan yin mu’amala mai zurfi da dukkan masu ruwa da tsaki a watanni masu zuwa, tare da haduwa tare wajen tsara fasalin aiki na...
    Gwamnatin ƙasar Isra’ila ta ce ta amince da tsagaita wuta a yaƙin da aka kwana 12 ana gwabzawa tsakaninsu da Iran. Isra’ila ta ce ta amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ce bayan abin da ya kira cimma burinta na ƙaddamar da yaƙin a Iran tun a farko. Ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ta yi nasarar murƙushe duk wata barazanar da take fuskanta daga Iran na mallakar makamin nukiliya da makamai masu linzami. Isra’ila ta ƙara da cewa ta kuma yi nasarar wargaza lissafin shugabancin sojin Iran da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnatin ƙasar. A karshe ta ce tanq godiya bisa abin da ya kira ƙoƙarin Shugaban Amurka Donald Trump na wargaza shirin nukiliyar Iran.
    Iyalan mafarauta 16 ’yan Jihar Kano da aka yi wa kisan gilla a garin Uromi da ke Jihar Edo sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su. Wasu daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya a harin da kuma iyalan waɗanda aka kashe, sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin magani da tallafi da kuma diyya fa gwamnatocin jihohin Edo da Kano suka yi musu bai wuce fatar baki ba. Ayarin farautan sun baro garin Fatakwal na Nijar Ribas ne, a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, amma wasu ’yan banga a Uromi suka tare su, suka yi musu kisan gilla. Akasarin mafarautan sun fito ne daga yankin Toronkawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano,...
    Wasu kuma sun jikkata a harin. Gwamna Sani ya ce kisan rashin imani ne, kuma ya bayyana cewa ya tattauna da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu don tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika. Ya kai ziyara ga waɗanda suka tsira daga harin a Asibitin Rundunar Sojin Naieriya na 44 da ke Kaduna, sannan ya yaba wa jama’ar Kaduna kan zaman lafiya da kaucewa fitina. Ya kuma roƙi shugabannin Filato da su hana faruwar irin wannan mummunan lamari. Gwamnan ya buƙaci hukumomin tsaro da su hanzarta kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Haka kuma wasu ƙungiyoyi a Turai sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan. Majiyoyi sun bayyana cewa Brentford na son a ce darajar Mbeumo ta kai irin kuɗin da United ta biya wajen ɗauko Cunha kafin su yarda su sayar da shi. Mbeumo ya zura ƙwallaye 20 a kakar wasan da ta gabata, kuma ya taimaka aka zura wasu tara. Sai dai akwai yiwuwar shi da abokin wasansa na tawagar Kamaru, Andre Onana, ba za su buga wasannin farko na sabuwar kakar wasa ba saboda za su wakilci Kamaru a gasar cin kofin ƙasashen Afirka da za a buga a Maroko. Kamaru za ta fara buga wasa da Gabon ranar 24 ga watan Disamban 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Qatar da Iran bayan hare-haren da Amirkan ta kai wa Iran. Ya sanar cewa cikin awa shida na farko Iran za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani Isra’ila ta dakatar, wanda hakan zai kawo ƙarshen yaƙin ɗungurungum. Sanarwar tasa na zuwa ne bayan tsohon Fira Ministan Rasha, babbar ƙawar Iran, Dimitry Medvedev na cewa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i. Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga? NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Idan ba ku sani ba, ko kuma kuna buƙatar ƙarin sani, ku biyo mu a shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci. Domin sauke shirin, latsa nan
    Sai dai babu wani tabbaci daga gwamnatin Iran ko Isra’ila kan cewa sun yarda su dakatar da yaƙin. Trump ya kira rikicin da ake ciki da suna “yaƙin kwana 12,” yana mai cewa wannan rikici da za a iya yin shekaru ana fafatawa da shi bai bazu ba, kuma ba zai bazu ba. Mene ne ke faruwa yanzu? Bayan da Trump ya sanar da cewa an tsagaita wuta, Isra’ila ta ce an kashe mutane uku sakamakon hare-haren da Iran ta kai. Amma ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce babu wata yarjejeniya ta tsagaita wuta. Sai dai ya ce Iran za ta daina kai hari idan Isra’ila ma ta dakatar da nata. Rikicin ya tsananta ne bayan Iran ta...
    Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Qatar da Iran bayan hare-haren da Amirkan ta kai wa Iran. Ya sanar cewa cikin awa shida na farko Iran za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani Isra’ila ta dakatar, wanda hakan zai kawo ƙarshen yaƙin ɗungurungum. Sanarwar tasa na zuwa ne bayan tsohon Fira Ministan Rasha, babbar ƙawar Iran, Dimitry Medvedev na cewa...
    2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa. Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a: – Lagos (Kudu maso Yamma) – Enugu (Kudu maso Gabas) – Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu) – Jos (Arewa Tsakiya) – Maiduguri...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin majalisa ya ba NNPC kwanaki bakwai don ta ba da cikakken bayani kan batutuwan da aka bankaɗo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Leeds United ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan ƙungiyar Udinese na ƙasar Slovenia, Jaka Bijol mai shekaru 26 kan farashin fam miliyan 15. Wannan dai shi ne sabon ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta ɗauka bayan zuwan ɗan wasan gaban Jamus, Lukas Nmecha, kyauta. ‘Harin da Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka keta haddin Qatar ne’ Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka Cefanen Bijol da Leeds ta yi zai ƙara wa ƙungiyar tagomashi wajen tsaron bayanta a yayin da ake shirye-shiryen dawowa sabuwar kakar wasanni ta Firimiyar Ingila. Bijol dai ya buga ƙasarsa Slovenia wasanni 63 ciki har da rawar gani da ya taka a gasar Euro 2024, inda suka yi canjaras da Ingila a...
    Ya ce: “Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, ciki har da na Amurka, na fitar da gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasar su, yana da muhimmanci a faɗa a fili cewa Abuja tana da tsaro ga ‘yan ƙasa da mazauna da kuma baƙi baki ɗaya.”   Ya bayyana cewa hukumomin tsaro a Nijeriya suna aiki tuƙuru dare da rana don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ya ƙara da cewa tsarin tsaro a Abuja yana aiki yadda ya kamata tare da nasarori masu yawa wajen gano duk wata barazana da kuma daƙile ta kafin ta faru.   Ministan ya ƙara da cewa gargaɗin da Amurka ta fitar ba ya nuni da wata...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Qatar ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke yankin al-Udeid na kasar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.” Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka Babu dalilin kai wa Iran farmaki — Putin Ya ce na’urorin kakkaɓo makamai na ƙasar sun “samu nasarar daƙile hare-haren na makamai masu linzami” kuma tuni aka janye dakarun Amurka daga sansanin tun kafin harin. Ya ƙara da cewa “an ɗauki duka matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiyar dakarun a sansanin, ciki...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da gidauniyar Milano Cortina 2026, wanda aka dorawa alhakin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina ta shekarar 2026 dake tafe. Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, sassan biyu sun amince su zurfafa hadin gwiwa a sassan yayatawa, da tsara ayyukan watsa gasar ta Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina, tare da aiwatar da musayar jami’ai. Sakamakon wannan hadin-gwiwa, CMG ya samu ikon watsa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina dake tafe a shekara mai zuwa a hukumance. An kafa gidauniyar Milano Cortina 2026 a watan Disamban shekarar 2019, domin ya tsara, da...
    Rahotanni na cewa ƙasar Iran ta fara abin da ta kira martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka. Kamfanin Dillancin Labaran Iran na Tasnim, ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar da Iraƙi A halin yanzu ne aka samu labaran jin ƙarar abubuwan fashewar a Qatar.
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari. Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a Columbia A jawabin da ya gabatar a farkon tattaunawar wanda aka yada a gidan talabijin na gwamnatin Rasha, shugaba Putin ya ce: “Babu wata hujja ko dalili da zai sa a kai wa Iran farmaki.” Ya ƙara da cewa “na ji daɗin zuwan ka [Agarachi] Moscow a yau. Wannan zai ba mu damar tattauna waɗannan batutuwa masu wahala da kuma...
    Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Rasha, da Sin da Pakistan, sun gabatar da wani daftarin kudurin kwamitin sulhun MDD, kan halin da ake ciki a Iran. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya shaidawa nuni taron manema labarai da aka saba yi a yau Litinin cewa, harin da Amurka ta kai kan wuraren da kasar Iran ta girke na’urorin nukiliya ya saba wa manufar tsarin dokokin MDD, tare da kara ta’azzara tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya, don haka, dole ne kwamitin sulhun ya dauki mataki kan batun. Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin na sa ran mambobin kwamitin za su goyi bayan daftarin kudurin, tare da sa kaimin kwamitin ya taka muhimmiyar...
    Rundunar Sojin ƙasar Columbia ta tabbatar da cewa fararen hula sun yi garkuwa da dakarunta guda 57. Janar Federico Alberto Mejía  na Rundunar ya sanar a ranar Lahadi cewa mutane kimanin 200 sun yi garkuwa da sojojin ne bisa umarnin ’yan tawayen FARC da suka addabi ƙasar. Ta bayyana cewa al’ummar ƙasar suna fuskantar matsin lamba daga ’yan tawayen masu ɗauke da makamai. Sanarwar ta ƙara da cewa an sace sojoji 31 a ranar Asabar, ragowar kuma ranar Lahadi. Erik Rodríguez ya bayyana cewa sace sojojin na da alaƙa da kama wani jagoran ’yan tawayen kungiyar EMC da sojojin suka yi. Ya ce a yayin da suke ƙoƙarin daukar sa a jirgi ne mutanen suka yi musu ƙawanya suka yi...
    Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya. Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris...
    Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya. Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris...
    Rundunar ‘yansandan jihar Benuwe ta tabbatar da garkuwa da dukkan fasinjojin wata motar bas ta kamfanin Benue Links a hanyar Eke, Ugbokolo a karamar hukumar Okpokwu ta jihar a yammacin Lahadi. Wani ganau da ya zanta da LEADERSHIP ta wayar tarho, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Lahadi, inda wasu ‘yan bindigar suka tare wata motar bas din da ta taho daga Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, suka yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta bayan sun kwace kayayyakinsu, sannan suka tafi da su cikin daji. 2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega Ina Da Isassun Kuɗi, Ban Ciwo Bashin Ko Kwabo Ɗaya Don Gyara Jihar Zamfara...
    Bayan faruwar lamarin ne, wasu fusatattun dalibai matasa suka tare hanyar Agaie-Lapai, suna nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa abokin su.   Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Yau 23 ga watan Yuni, 2025 da misalin karfe 3 na dare, rundunar ta samu labarin cewa, da misalin karfe 2:30 na dare wasu ‘yan daba sun kai hari a wasu dakunan kwanan dalibai dake unguwar Ndakitabu ta Lapai, amma maharan sun tsere a lokacin da jami’an ‘yansandan suka isa wurin”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan Jaridar Daily Trust, Hamza Idris rasuwa. Kaninsa, mai suna Aminu Idris, ya bayyana cewa a safiyar Litinin ne Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan, Hajiya Rabi (Umma) cikawa bayan gajeruwar jinya a Jihar Kano. Za a gudanar da jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya ranar a Layin Ɗorawar ’Yan Kifi da ke unguwar, Rijiyar Zaki, Kano. Daga nan za a kai ya maƙabartar Walid Mai Zage da ke Kofar Mazugal. Muna roƙon Allah Ya yi mata rahama, Ya ba wa dangi haƙurin rashin da kuma dangana.
    Gwamnatin Amurka ta buƙaci ƙasar Sin da ta hana Iran rufe mashigar tekun Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi kiran ne bayan da kafar yada labarai ta Iran, Press TV ta ruwaito cewa majalisar dokokin ƙasar ta amince da shirin rufe mashigar. Duk wani cikas ga samar da man fetur zai yi tasiri mai tsanani ga tattalin arzikin duniya. Ƙasar Sin ce babbar mai sayen mai daga Iran kuma tana da kyakkyawar alaka da Tehran. Harin Iran: Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya Farashin man fetur...
    Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu.   Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023.   A cewar sa, inganta haɗin gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara.   Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waɗanda aka kammala a ƙarƙashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haɗa da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya...
    Manyan Hafsoshin Tsaro na ƙasar Iran sun sha alwashin mayar wa Amurka da martani mai tsanani wanda sai ta yi da-na-sanin harin da kai wa Iran. Rundunar Tsaro ta Iran ta sanar da haka ne bayan wani zama da Babban Kwamandan Sojojin ƙasar, Amir Hatami, ya yi da wasu manyan kwamandojinsa. Harami ya shaida wa taron tsare-tsaren cewa ya zama tilas Amurka ta girbi abin da ya shuka a Iran a wannan karon. Ya bayyana cewa ko a baya, Iran ta saba koya wa Amurka darasi a duk lokacin da ta takali Iran. Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya Babban Hafsan Tsaron Iran,  Abdolrahim...
    Rikicin Isra’ila da Iran ya kara dagula tabarbarewar harkokin man fetur da iskar gas a cikin fargabar barkewar rikicin Gabas ta Tsakiya wacce ta kasance jigo wajen hada-hadar man fetur da iskar gas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Akwai yiwuwar ƙasar Koriya ta Arewa mai ƙarfin makaman nukiliya za ta taimaka wajen gyara tashoshin nukiliyan Iran da hare-haren Amurka suka lalata da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya a Iran. Wani masani mai suna Ankit Panda daga cibiyar zaman lafiya ta kasa da kasa ta da ke Amurka, ne ya bayyana hakan, baya Amurka ta kai hare-hare kan tashoshin nukiliya na ƙasar Iran. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Ankit Panda, yana bayyana cewa matakin zai kawo ƙarshen irin takura da ƙasashen Yamma ke yi wa Iran. Hakan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai a matsayin keta hurumin...
    Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa a safiyar ranar Asabar ne aka sanar da ofishin kwana-kwana ta samu kiran gaggawa game da lamarin. Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki. A sakamakon wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar...
    Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa a safiyar ranar Asabar ne aka sanar da ofishin kwana-kwana ta samu kiran gaggawa game da lamarin. Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki. A sakamakon wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar...
    Hukumar ta kuma jaddada cewa, ana kokarin ganin an kawar da duk wata barazana domin dakile duk wani jinkirin da bai kamata ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da ka yi karatu a Italiya, yaya kake kwatanta ci gaban Kano, da na wasu biranen zamani da ka sani? Wannan tambaya ce mai amfani. Birane irin su Milan da Florence da Turin, suna da dogon tarihi a fannin ci gaban birane amma abin da ke bambanta Kano a yanzu shi ne saurin aiki da kuma hangen nesa, kuma wannan gwamnati tana da tsari a fagen. A matsayina na mai tsara gine-gine, zan iya saurin gano kyakkyawan shiri idan na gan shi. Kuma abin da ke faruwa a Kano ya na da kyau sosai. Ana gabatar da abubuwa masu alaƙa da biranen zamani, wato wuraren shakatawa da sanya fitilun titi da magudanan ruwa da kuma kula da tsarin taswirar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tare fasinjoji da kashe su a hanyoyin Najeriya na ƙara tsananta, musamman a yankunan Arewa. Misali, a shekarun baya an sha tare matafiya a kashe su a hanyar Abuja zuwa Kano. A kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a hanyar su ta komawa Kano. Sai na kwanan nan da ya faru a Jihar Filato inda aka kashe wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure. NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne da...
    Batun sauya sheka da ke faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya, Jega ya kira a hana sauya sheka ga wadanda aka zaba a bangaren zantarwa da kuma ‘yan majalisa. Ya kuma yi kira ga jami’an INEC a matakin tarayya, da na jihohi su shirya gudanar da zaben cike gurbi da zarar an samu labari game da sauya sheka. Ya ba da shawarar cewa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje su dunga kada kuri’a a zaben shugaban kasa, kuma ya yi kira a tsaurara dokoki kan kudaden kamfen ciki har samar da hukumar da za ta sa ido kan aiwatar da hukunci. Jega ya yi nadama da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da Nijeriya take fuskanta shi ne,...
    Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), inda ya karɓi ragamar shugabancin daga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. An sanar da hakan ne a taron shugabannin ECOWAS karo na 67 da aka gudanar a Abuja. An kashe matar aure, manomi ya jikkata a wani sabon hari a Kaduna ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa  Shugaba Tinubu, wanda ya yi wa’adin shugabancin ƙungiyar sau biyu tun daga shekarar 2023, ya bayyana cewa shugabancin ECOWAS babban abu ne a rayuwarsa. Ya ce: “Yayin da nake miƙa ragamar shugabanci ga abokina kuma ɗan uwana, Shugaba Julius Maada Bio, ina mai gamsuwa da fatan alheri ga makomar Yammacin Afirka.” Ya ƙara...
    Idi ya kuma yi nazari kan matakin da bangaren kiwon dabbobin kasar yake, inda yawan Shanu suka kai miliyan 20.9, Tumaki miliyan 49.1, Awakai miliyan 88.2, Kajin gidan gona kuma miliyan  258.5. Kazalika, Maiha ya jaddada muhimmancin hadakar ta zuba hannun jari a fannin na kiwon dabbobin, wanda ya sanar da cewa; hakan zai taimaka matuka gaya wajen dakile yaduwar cututtukan da ke yi wa dabbobin illa. A nasa jawabin, Babban Shugaban Kamfanin Ricardo Lacerda ya bayyana cewa; kasar Brazil na shirin samar da wuraren kiwon dabbobi na zamani kimanin guda 200,000 a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, musamman don kara samar da isasshen naman Shanu. Ya kara da cewa, kasar za kuma ta tabbatar da kokarin kara habaka...
    Yanzu haka ana shirye-shiryen gudanar da taron kasa da kasa na tattauna batutuwan raya tattalin arziki na Davos na yanayin zafi karo na 16, taron da aka fi sani da dandalin Davos. A bana za a gudanar da taron ne tsakanin ranakun Talata 24 zuwa Alhamis 26 ga watan nan na Yuni, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, bisa taken “sana’o’i a sabon zamani.” A bana taron zai mayar da hankali ne ga muhimman fannoni biyar, wadanda suka hada da warware batu game da tattalin arzikin duniya, da hange game da kasar Sin, da halin da masana’antun duniya suka fuskanta na taka musu birki, da zuba jari kan al’umma da duniyar bil’adama da batun sabbin makamashi da hajoji. Game...
    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. A yayin harin, wata matar aure ta rasu, yayin da wani manomi ya samu rauni. ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa  Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani Harin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025, a ƙauyen Ungwan Sarkin Hausa da ke Rimau. Ana zargin maharan sun gudu da shanun da suka sato daga Ƙaramar Hukumar Kauru. A lokacin harin, sun kashe wata mata mai suna Misis Alheri Danzaria. Sun kuma sace wasu mutum biyu, amma daga...
    Shugaban kwamitin hana kwacen waya da yaki da miyagun kwayoyi da fadace-fadacen daba da gwamnati Kano ta kafa a watanni 21 da suka wuce, Janaral Gambo Ahmed mai Addau mai ritaya, ya bayyana ce wa yanzu haka wannan kwamiti ya gano cibiyoyi 52 da ake aikata laifuka a daukacin Jihar Kano. Ya kara da cewa yanzu haka bisa umarni da amincewar gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wannan kwamiti ya dauki matasa 1,050 aiki, wanda kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kano, Ibrahim Umar ya kaddamar a madadin gwamnan, domin hada hannu da jami’an ‘yansanda da na NDLEA da cibil defence, da na leken asiri da na farin kaya (DSS), da ‘yan bijilanti da sauransu, domin murkushe wannan mummuna aiki...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford ya ce zai so ya taka leda tare da matashin ɗan wasa Lamine Yamal a Barcelona, Rashford mai shekaru 27, wanda ya shafe rabin kakar wasan bara ya na zaman aro a Aston Villa, a halin yanzu yana atisayen ƙara kuzari a ƙasar Sifaniya kafin a fara wasannin share fage na kulob ɗin, yayin da ake ta raɗe raɗin makomarsa a United. Lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar yin wasa tare da Yamal, Rashford ya ce: “E, tabbas, kowa yana so ya yi wasa tare da mafi kyawun dan wasa, don haka nima inada wannan burin kuma zamu gani, Yamal, mai shekaru 17, ya taka rawar gani sosai yayin da Barcelona...