Aminiya:
2025-07-23@22:55:18 GMT

’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su

Published: 29th, May 2025 GMT

Daya daga cikin maniyyata Aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani dan kasar Rasha kudinsa da ta tsinta a birnin Makka na kasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200.

Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a ranar Talata .

Ta tsinci kudin ne da yawansu ya kai Dala dubu biyar, kimanin miliyan takwas da dubu 200 a Naira, idan aka canza a kan farashin N1,648 a kan kowacce Dala daya.

Babu wanda ya tayar da bam a Abuja —Wike Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin dauri a gidan yari

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da kuma Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato, Hon. Dayyabu Dauda duk sun tabbatar da faruwar lamarin.

“Ta nuna halin dattaku, gaskiya da rikon amana ta hanyar mayar da Dala dubu biyar din da ta tsinta a masallacin harami ga mai su. Hakika ta nuna halin nagarta da tausayi,” in ji Hon Dayyabu.

A wani labarin kuma, hukumar ta NAHCON ta nuna rashin jin dadinta da yadda daya daga cikin maniyyatan jihar Zamfara ta haihu a Madina a makon nan.

Hukumar ta ce ta yi mamakinn yadda matar ta tsallake duk gwaje-gwajen da ake yi a kokarin hana masu juna biyun da suka kusa haihuwa tafiya.

Sai dai ta ce za ta yi cikakken bincike domin ta gano a ina aka samu matsalar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin

“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.”

“Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!”

A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar Sin, tare da hada kai da kasar Sin da ma sauran baki ’yan kasuwa wajen kyautata tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare
  • Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas
  • DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  • Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa
  • Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21
  • Hisbah Ta Lalata Barasa Ta Naira Miliyan 5.8 A Jigawa
  • NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa
  • Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin