Amurka za ta hana ‘’visa’’ ga daliban dake sukanta a shafukan sada zumunta
Published: 28th, May 2025 GMT
Gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta umarci ofisoshin jakadancinta da ke faɗin duniya su dakatar da bai wa dalibai da sauran mutane da ke neman bizar ziyara zuwa kasar.
Gwamnatin ta ba da umarnin ne yayin da take fadada shirin binciken bada bisa ta hanyar tantance abubuwan da mutum ke wallafawa a shafukan sada zumunta, musamma dalibai.
Wasu daliban kuma da tuni suke Amurka an kwace bizarsu saboda shiga gangamin nuna goyon-bayan Falasdinawa.
Wannan na daga cikin matakan da Trump ke dauka na hana manyan makarantun Amurka da suka yi fice wajen dogaro da kudaden makaranta da suke samu daga daliban ketare.
Kafin wannan lokaci fadar gwamnatin Amurka White House ta ce gwamnatin Trump ta bukaci dukkanin ma’aikatun Amurka su datse tallafin da suke bai wa jami’ar Havard da suke amfani da shi wajen bada tallafin karatu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
Yan majalisar dokokin kasar Iran sun bukaci majalisar dokokin kasar Iraki su kori sojojin Amurka daga kasar ta Iraki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yana cewa, yan majalisar dokokin kasar Iran sun bayyana haka ne a lokacin ganawasu da wani dan majalisar dokokin kasar Iraki mai wakiltan lardin Karbalar Imam Hussain (a) a majalisar dokokin kasar.
Labarin ya nakalto wakilin lardin Karbala a majalisar dokokin kasar Iraki yana cewa kasashen Iran da Iraki da gwamnatin kasar Iraki sun gamu a wannan ra’ayin kuma nan gaba abinda za’a yi Kenan. Yace dole ne sojojin Amurka su fice daga kasar Iraki, su kuma fice daga dukkan kasasjen larabawa a yankin. Ya ce da haka ne kasashen yankin zasu tabbatar da tsaron yankinsu.
Ebrahim Rezae dan majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa, kasar Amurka baa bin Amincewa ne, kuma shirin HKI na fadada mamayar karin yankunan kasashen larabawa na tafiya ne tare da umurnin Amurka kai tsaye.
A ranar 3 ga watan Jenerun Shekara ta 2020 ne shugaban Donal Trump ya bada umurnin kashe babban kwamandan rundunar Qudus ta Iran Janar Shahid Qasim Sulaimani a lokacinda ya shigo kasar Iraki daga Siriya tare da gayyatar gwamnatin kasar ta Iraki.