Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da shugaban kasar Kiribati, kuma ministan harkokin wajen kasar Taneti Maamau, sun jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashen yankin Pasifik karo na uku a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin.

A yayin taron, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda shida kan kafa kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin Pasifik. Na farko shi ne dagewa kan mutunta juna. Ya ce kasar Sin tana goyon bayan kasashen yankin wajen kiyaye cikakken ’yancinsu, tsaro da muradunsu na ci gaban. Kuma Sin ta yi imanin cewa, kasashen yankin za su ci gaba da bin manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya. Na biyu shi ne tsayawa tsayin daka kan sanya neman ci gaba a gaban kome. Ya ce bangarorin biyu za su aiwatar da shawarar ci gaban duniya tare da zurfafa hadin gwiwa kan raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” mai inganci, kana da gaggauta inganta shawarwari game da cimma yarjejeniyar cinikayya cikin ’yanci a tsakaninsu. Na uku shi ne, a dora muhimmanci kan muradun jama’a. Bisa ga haka, za a gudanar da wasu kananan ayyuka masu halin musamman da inganci guda 200 da suka shafi zaman rayuwar jama’a. Na hudu shi ne dagewa kan musayar ra’ayi da koyi da juna, ciki har da karfafa mu’amala tsakanin kafofin watsa labarai, matasa, mata, harkokin wasanni, da dai sauransu. Na biyar shi ne kiyaye adalci. Ya ce kamata ya yi a tsaya kan kare tsarin kasa da kasa bisa tushen dokokin kasa da kasa, da daukar Majalisar Dinkin Duniya a matsayin ginshikinsa. Na shida shi ne, a zama tsintsiya madaurinki guda. Ya ce kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa da kasashen yankin Pasifik wajen tinkarar sauyin yanayi, wanda duk duniya ke fuskanta. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: da kasashen yankin Pasifik harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma  October 30, 2025 Daga Birnin Sin Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC October 30, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
  • Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher