A nasu jawabin, kwamishinonin kudi da kasafin kudi Misis Augustina Wandamiya da Mista Emanuel Pridimso sun bayyana cewa, an yi bitar kasafin ne da nufin gano wuraren da aka samu rarar kudi da kuma tabbatar da cewa, an kashe kudin kasafin shekarar 2024 a inda ya dace.

 

Sun kara da cewa, jihar ta kula da tsari wajen aiwatar da kasafin kudi, tare da tabbatar da gaskiya, wanda hakan, ya taimaka wajen samar da kyakkyawan aiki a ayyukan raya jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin

Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin.

 

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi a hanyar Muritala Muhammed, daura da Cocin C & S, Ilorin.

 

A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobara sun gano cewa wani gini mai hawa biyu da ya kunshi dakuna 8 da shaguna 10 na fuskantar barazana. Ya bayyana cewa, ta hanyar daukar mataki cikin gaggawa da hadin kai, jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar yadda ya kamata, tare da hana yaduwarta zuwa gine-ginen da ke kewaye, inda ta kara da cewa a sakamakon haka, daki daya ne lamarin ya shafa.

 

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar lantarki ce dalilin ta tashin gobarar.

 

Da yake mayar da martanin Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara Prince Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kasance cikin shiri da kiyaye lafiya a gidajensu da wuraren kasuwancinsu.

 

REL/ALI MUHAMMAD RABIU

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Ma’aikata Ne Ya Hana Borno Fara Biyan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi – Zulum
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Jihar Kano Za Ta Hada Gwiwa FMBN Don Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi
  • Dalilin da muka gaza biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi — Gwamnatin Borno
  • Gwamna Sule Ya Ƙara Musanta Zargin Kare Ƴan Ta’adda A Nasarawa
  • UNICEF Ya Bukaci Jihar Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi
  • Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma’a – Gwamnati
  • PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin