Mutum 1 Ya Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Abuja
Published: 28th, May 2025 GMT
Ya ce jami’an FEMD, FRSC da ‘yansanda sun gaggauta zuwa wurin domin gudanar da aikin ceto. Mohammed ya ja kunnen direbobi da su tabbatar motocinsu na cikin ƙoshin lafiya kafin su hau hanya.
Ya kuma shawarci jama’a da su rika kiran lambar gaggawa 112 idan wani lamari ya faru. Wannan hatsari ya ƙara tayar da hankali kan lafiyar hanyoyi, inda hukumomi ke kira da a dunga bin dokokin kula da lafiyar motoci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Syria: Mutane Da Dama Sun Mutu Da Kuma Jikkata Sanadiyyar Gobara A Rumbun Ajiyar Makamai
An sami hatsarin tashin gobara a cikin wani rumbun ajiyar makamai a garin Mu’arrah dake gundumar Idlib ta Arewa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama.
Majiyar lafiya ta kiwon kasar Syria ta bayyana cewa; Mutane 2 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 70 su ka jikkata sanadiyyar fashewar rumbun makamai a garin Mu’arrah Masrin.
Hukumar agjin gaggawa ta kasar Syria ta ce; Har yanzu babu cikakken dalili akan abinda ya haddasa wannan gobarar ta Mu’arrah Msarin.
Ma’aikatan kwana-kwana sun nufi wurin da gobarar ta tashi domin kashe wuta da kuma dauke mutanen da su ka jikkata.