Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Borno
Published: 28th, May 2025 GMT
Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan.
Majiyar leken asirin hedikwatar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:35 na wayewar safiyar talata 27 ga watan Mayu.
Majiyar ta ce wasu ’yan ta’adda da ba a tabbatar da adadin su ba sun kai hari a bataliya ta 50 da ke Marte.
Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900 Tinubu ya ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya ta Kabo Zuwa Jami’ar Fasaha ta TarayyaDakarun da ke samun goyon bayan wata tawaga ta runduna ta 24 da bataliya ta musamman ta 134, sun yi gaggawar fafatawa da ’yan ta’addan a wani kazamin fadan da aka kwafsa.
A cewar rahoton, dakarun rundunar sojojin saman Najeriya na Operation Hadin Kai, ta aiwatar da aikin leken asiri ta sama, da kuma dauki ba dadi, wanda ya taka rawar gani wajen fatattakar ’yan tada kayar bayan da suka tsere.
Majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar dakile harin tare da dawo da cikakken iko a yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin zakulo abubuwan da suka rage da kuma kwato makamai da kayan aikin da ’yan ta’addan ke amfani da su.
“Sojoji biyu sun rasa ransu a yayin wannan farmaki, sannan an samu wasu asarorin kayayyakin da suka hada da lalacewar wata babbar mota mai dauke da bindiga da kuma tayar wata motar sojoji,” in ji majiyar.
Harin na baya-bayan nan a Marte na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji ke dada kai hare-hare a yankin tafkin Chadi da arewacin Borno, inda kungiyoyin ISWAP da Boko Haram suka yi yunkurin sake kafa sansanoninsu.
A halin da ake ciki dai, ana ci gaba da sanya ido sosai kan harkokin tsaro a jihar Borno, inda ake ci gaba da gudanar da sintiri da tattara bayanan sirri da nufin hana kutse a nan gaba, in ji majiyar ta sojan Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Marte
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Gombe ta rattaba hannu kan kwangilar biliyan 48 na aikin zaizayar Kasa
Jihar Gombe ta rattaba hannu kan kwangilar sama da biliyan 48 don aikin kula da Makarantar ‘yan mata ta Mega dake Doma da kuma zaizayar kasa
Baya ga sanya hannu kan kwangilar, an kuma bayar da cak don biyan diyya ga mazauna yankin mai nisan mita 10 da ke kan hanyar aikin.
Da yake jawabi a wurin rattaba hannu kan kwangilar a hukumance a Hayin Missau Bogo, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da muhallin Gombe da kuma kare makomar jama’a.
A cewarsa aikin ba wai kawai zai shawo kan zaizayar kasa ba ne zai dawo da fata ga al’ummomin da abin ya shafa.
Alh. Inuwa Yahaya wanda ya bada umarnin kammala aikin a cikin watanni 30 ya bukaci dan kwangilar da ya gabatar da aiki mai inganci.
Ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya da juna a tsakanin al’umma, da kuma kiyaye ayyukan da ba su dace ba kamar sare itatuwa da zubar da shara da ke cutar da muhalli.
Shima da yake jawabi kwamishinan albarkatun ruwa da muhalli da gandun daji na jihar Gombe Mal. Muhammad Fawu, ya yabawa hadin gwiwar da gwamnatin Gombe da Bankin Duniya suka yi wajen samar da kudaden aikin, ya ce wani gagarumin kokari ne na kare muhalli da kuma tabbatar da makomar al’umma.
KARSHEN HUDU