Akwai Ma’ana Mai Zurfi A Bayan Da’a
Published: 27th, May 2025 GMT
Tabbas a halin yanzu, wasu kasashe ba su ba da’a muhimmanci ba, kana suna ta daukar matakan kashin kai yadda suka ga dama, lamarin da ya sa al’amuran kasa da kasa suka shiga rudani. Dangane da wannan batu, dole ne Sin da kasashen Afirka masu da’a su karfafa hadin kai, su yi adawa da siyasar nuna fin karfi, da daukaka ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori masu fada-a-ji a duniya, da kare tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Masu Kare Hakkin Dan’adam Suna Allawadai Da Takunkumin Amurka Akann Jami’ar MDD A Falasdinu
Kungiyoyin kare hakkin dan’adam suna yin tir da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Francesca Albanese wacce it ace jami’ar MDD mai kula da hakkokin bil’adam a Falasdinu.
Shugaban cibiyar siyasar kasa da kasa da ta shafi hukumomi Dylan Williams ya bayyana takunkumin da cewa; Yana nuni da da halayyar gwamnatin ‘yan daba’.
Ita kuwa shugabar kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa “Amnesty International” Agnès Callamard kira ta yi ga gwamnatocin duniya da dukkanin masu bakin fada da su ka yi Imani da aiki da dokokin kasa da kasa da su yi duk abinda za su iya, domin ganin an hana takunkumin yin tasiri akan ayyukan Francesca Albanese, da kuma bayar da kariya ga dukkanin aikin hukumar ta kare hakkin dan’adam da kare ‘yancinsu.”
A jiya Laraba ne dai Amurka ta kakaba takunkumi akan Francesca Albanese saboda ta soki yakin da Isra’ila take yi a Gaza.
Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ne ya bayyana cewa: “A yau ina mai sanar da kakaba takunkumi na musamman akan jami’ar kula da hakkin dan’adam ta MDD Francesca Albanese, saboda ayyukan da take yi da su ka saba doka na Sanya kotun manyan laifuka ta duniya daukar matakan da suke cin karo da doka aakn kamfanoni da jami’ai na Amurka da Isra’ila.”
Francesca Albanese ta mayar da martani a sahfinta na X cewa: A cikin karsashi da gamsuwa, zan kasance a tare da adalci, kamar kowane lokaci.”
A wani rahoto da ta fitar jami’ar kare hakkin bil’adaman ta MDD ta zargi manyan kamfanonin fasahar zamani fiye da 60 da masu kera makamai da suke taimakawa ‘yan share wauri zauna a Isra’ila da kuma yakin da suke yi a Gaza. Haka nan kuma ta yi kira ga wadannan kamfanonin da su dakatar da taimakawa Isra’ila da suke yi, sannan kuma ta bukaci ganin an hukunta manajojin wadannan kamfunan saboda keta dokokin kasa da kasa da suke yi.