Adadin Zirga-Zirgar Fasinjoji Ta Jiragen Kasa A Sin Na Iya Kaiwa Sama Da Miliyan 80 Yayin Hutun Bikin Duanwu
Published: 31st, May 2025 GMT
Hukumar lura da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin, ta yi hasashen samun adadin zirga-zirgar fasinjoji ta jiragen kasa sama miliyan 80.5, yayin kwanaki biyar na hutun bikin Duanwu ko bikin tseren kwale kwale na bana.
An fara samun dandazon matafiya ta jiragen kasa a kasar Sin tun daga yau Juma’a, kwana guda gabanin kwanakin hutun uku, yayin da ake sa ran kaiwa kololuwar yawan matafiyan a gobe Asabar, inda ake hasashen adadin zirga-zirgar zai kai kusan miliyan 18.
Alkaluma daga kamfanin 12306, mai samar da hidimar yankar tikitin jiragen kasa na kasar Sin, sun nuna wuraren da matafiya suka fi yankar tikitin zuwa, wadanda suka hada da biranen Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Chengdu, da Hangzhou. Sauran su ne Wuhan, da Xi’an, da Nanjing, da Changsha da kuma Zhengzhou. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: jiragen kasa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasaAn ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.
Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.
“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.
Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.