Leadership News Hausa:
2025-11-02@08:43:31 GMT

Gwamna Zulum Ya Nemi A Zuba Hannun Jari A Harkar Noman Rani

Published: 31st, May 2025 GMT

Gwamna Zulum Ya Nemi A Zuba Hannun Jari A Harkar Noman Rani

Haka zalika, ya kara da cewa; gwamnatinsa ta bayar da kimanin Naira biliyan biyu, domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani mai amfani da hasken rana a garin Baga.

Gwamna Zulum ya ci gaba da cewa, kwanan nan ya tura wata tawagar bincike, don yin bincike tare da gano gaskiya zuwa Gamborun Ngala, sannan kuma tawagar ta tabbatar mana da samun albarkatun ruwan karkashin kasa, wadanda za mu iya amfani da su wajen noman rani ta hanyar ban-ruwa.

Kazalika, ya sanar da cewa, an kuma kebe karin wasu Naira biliyan 1.5, domin gudanar da irin wadannan ayyuka a garuruwan Gamborun Ngala da Marte, wadanda a halin yanzu an kusa kammala su baki-daya.

Bugu da kari, ya bayyana cewa; bisa kokarin gwamnatinsa na mayar da hankali wajen farfado da shirin noman rani na Tafkin Chadi ta Kudu, tuni aka fara noma hekta 1,000 a karkashin aikin noma na Baga a kan kudi kimanin Naira biliyan biyu.

Gwaman ya ci gaba da cewa, har ila yau; gwamnatin jihar ta Borno ta samar da hekta 200,000 a Gamboru da kuma wata hekta 200,000 na samar da wutar lantarki a Lamboru ta hanyar amfani da tsarin ban-ruwa, domin farfado da ayyukan noma a fadin yankin baki-daya.

Haka zalika, Zulum ya sanar da cewa, gwamnatinsa ta haka rijiyoyi kusan kimanin 3,000 a Damasak da ke Karamar Hukumar Mobba.

Sannan kuma, ya yi nuni da cewa; wannan ya bai wa manoma da dama damar yin noma a fili mai tsawon kilomita 16, matakin da ya bullo da hanyar noman ruwan karkashin kasa a yankin da a baya ba a saba yin irin sa ba.

Zulum ya kuma yi alkawarin ci gaba da hada kai da hukumar, musamman domin samun nasarar fadada noman a Ngala da Damasak da sabon yankin Marte tare da samar da ababen more rayuwa ga al’ummar yankin da suka dawo yankin da kuma tabbatar da dorewar samar da wadataccen abinci.

Gwamnan ya kuma sanar da cewa, gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa wajen farfado da tashar famfunan ruwa da ke Chadi Basin Kirenowa.

A cewarsa, gwamnatinsa na kan kokarin ganin ganin an kafa bataliyar soji a yankin, musamman don inganta tsaro tare da samun zaman lafiya, inda ya kara da cewa; gwamnatin tasa za ta so sanin inda za a iya shiga, sakamakon cewa abubuwan da za a iya samu suna nan.

Ya kara da bayyana cewa, yana ci gaba da tuntubar shugaban kasa da sauran shugabannin sojoji, kan yiwuwar kafa bataliyar soji a Kirenowa da nufin kare tashar famfon.

A nasu jawaban daban-daban tunda farko, shugaban hukumar, Farfesa Abdu Dauda Biu da Manajan Darakta, Alhaji Tijjani Tumsa sun sanar da gwamnan cewa; an kafa sabuwar hukumar ce a ranar 13 ga watan Disamba 2024.

A cewarsu, wannan ziyara na da matukar muhimmancin gaske, duba da cewa; wuraren da ke karkashin kulawarsu, ciki har da madatsar ruwa ta Alau, na samun kulawar da ta dace.

Kazalika, sun kuma jinjina wa Zulum; kan yadda yake gudanar da ayyukansa da kuma jajircewarsa, musamman a wannan bangare na madatsun ruwa da ke wannan jiha.

Har ila yau, shugabancin hukumar ya yi alkawarin hada kai da gwamnatin jihar ta Borno, musamman don samun nasarar aiwatar da wadannan ayyuka da suka shafi noman rani da kiwon dabbobi da kuma kamun kifi a wadannan yankuna.

Haka zalika, sun kuma bukaci goyon bayan Gwamna Zulum, wajen ganin an kammala wannan gyara na madatsar ruwa ta Alau a kan lokaci, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi a ‘yan kwanakin baya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Noman rani

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.

Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.

Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Ya ce an tsara wannan asusu  ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.

Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.

Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin  ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.

Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a  wuraren.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin