HausaTv:
2025-07-24@04:25:21 GMT

 Iran Ta Yi Watsi Da Jita-Jitar Cewa Za Ta Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium

Published: 29th, May 2025 GMT

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya sanar a marecen jiya Laraba cewa, Iran za ta iya dakatar da tace sanadarin Uranium a karkashin yarjejniyar da za a iya kullawa da Amurka.

Kakakin ma’ikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Baka’i ya yi watsi da labarin da kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya watsa na yiyuwar dakatar da tace sanadarin “Uranium’ yana mai kara da cewa; zai ci gaba babu kakkautawa, kuma ba abinda za ma za a yi tayi ba.

Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato Baka’i yana cewa; labarin na Reuters, ba komai ba ne sai farfaganda ake maimaitawa, da kuma an sha kore gaskiyarta.

Kamfanin dillancin labarun na “Reuters’ kamar yadda ya saba, ya ambato wata majiya Iran, wacce bai ambata kowacece ba, tana cewa za a dakatar da tace sanadarin Uranium din na wucin gadi, saboda a sakar mata kudadenta da ake rike da su.

A lukuta da dama dai jami’an kasar Iran sun sha ambata cewa batun tace sanadarin “Urani’um” wani abu ne da za a ci gaba da yinsa a cikin Iran,an cimma yarjejeniya, ko a’a.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa; Iran ba ta dauki batun tace Urani’um abin wasa ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da tace sanadarin

এছাড়াও পড়ুন:

Fizishkiyan: Batun Kare Hakkin Bil’adama Ba Komai Ba Ne Sai Karya

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Batun kare hakkin bil’adama da ake yi a duniya ba komai ba ne sai karya.

Shugaba Fizishkiyan ya yi ishara da yadda masu ikirarin kare hakkin bil’adama suke sa kafafunsu suna take hakkin mutanen Gaza da cikin kasashen yammacin Asiya da kuma tafka manyan laifuka.

A yau Talata ne dai shugaban kasar ta Iran ya gabatar da jawabi a wurin bikin girmama shahidan kallafaffen yaki na kwanaki 12, ya bayyana cewa: “A cikin wannan duniyar wacce take riya ci gaba da wayewa, a gaba idon duniya, ake yanke wa mutanen Gaza ruwan sha da abinci, a hana mata da kananan yara. Haka nan kuma ake tafka laifukan da su ka kunshi kisan kiyashi, amma kuma wai su ne ke Magana akan kare hakkin bil’adama.”

Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce, masu yin Magana akan kare hakkin bil’adama din ne suke sa kafafunsu suna take shi.

Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce, HKI da Amurka, sun kawo hari bisa riya cewa Iran tana son kera makamin Nukiliya, kuma wadanda su ka kai wa harin mata ne, kananan yara da kuma sauraren hula da ba su da makamai.

Shugaban kasar ta Iran ya ambato hudubar da Imam Hussain ( a.s) ya yi wa abokan gabarsa a karbala cewa: “Idan ba ku da addini, to ku zama ‘yantattun a cikin harkokinku na duniyu.”

Shugaba Fizishkiyan ya kara da cewa: A wannan lokacin suna yanke abinici da ruwa ga mutanen Gaza, sannan kuma a lokaci daya suna Magana akan kare hakkin bil’adama. Wane annabi ko addinin Allah ne ya halarta tafka laifuka irin wannan ?

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”
  • WFP zai dakatar da tallafin abinci da kiwon lafiya a Nijeriya
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  • Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetare
  • Fizishkiyan: Batun Kare Hakkin Bil’adama Ba Komai Ba Ne Sai Karya
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Iran Ba Zata Bar Tace Sinadarin Uranium Ba
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne
  • Birgediya Janar Sabahi Fard Ya Jaddada Cewa: Duk Wani Sabon Hari Kan Iran Zai Fuskanci Martani Mai Gauni