Shugaban Kasar Kenya: FOCAC Ya Samar Da Damammaki Ga Sin Da Afirka Wajen Inganta Hadin Kansu Da Samun Moriya Tare
Published: 26th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a sabon zamani.
Ruto ya ce, FOCAC ya samar da wani ingantaccen dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka dake shigar da karin jari daga ketare zuwa nahiyar Afirka, matakin da ya gaggauta bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a nahiyar, musamman a bangaren tasoshin jiragen ruwa da layin dogo da hanyoyin mota da sauransu karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, inda ya ce nasarorin da aka samu na jawo hankulan kasa da kasa.
Game da matakin kakabawa dukkan kasashe ciki hadda Kenya da takwarorinta na Afrika karin haraji da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka, masanan tattalin arziki sun bayyana shi a matsayin wanda ya sabawa dokar raya nahiyar Afirka da ba ta damammaki wato AGOA. A ganin Shugaba Ruto, dunkulewar tattalin arzikin duniya abu ne da ya zama dole ga daukacin al’ummun duniya, kuma manfunar gudanar da harkoki tsakanin mabambantan bangarori ita ce hanya daya tilo da za a bi na tabbatar da gudanar ciniki a duniya, duba da cewar tabbacin cinikin duniya ingantaccen karfi ne dake gaggauta ci gaba da bunkasuwar duniya baki daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana a yau Juma’a da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a Kuala Lumpur na Malaysia, inda suka yi musayar ra’ayi kan danganatkar Sin da Amurka da batutuwan dake jan hankalin kasashensu.
Wang Yi ya yi cikakken bayani kan matsayar Sin game da raya dangantakarta da Amurka, yana mai nanata bukatar bangarorin biyu su aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen suka cimma zuwa manufofi da ayyuka na hakika. Ya ce fatan ita ce Amurka ta kalli Sin da ra’ayi na sanin ya kamata da tsara manufar hulda da Sin bisa burin zaman lafiya da hadin gwiwar moriyar juna da tafiyar da dangantakarta da Sin bisa matsayi na daidaito da girmamawa da moriyar juna, tare da hada hannu da Sin wajen lalubo hanya mai dacewa da za su yi mu’amala ta fahimtar juna a sabon zamani.
Bangarorin biyu sun amince cewa, ganawar ta su ta yi ma’ana, kuma za su karfafa hanyoyin diplomasiyya na tuntubar juna da tattaunawa a dukkan matakai da bangarori, da ba sassan diplomasiyya masu kula da raya dangantakar kasashen biyu damar taka rawar da ta kamata da lalubo bangarorin fadada hadin gwiwarsu yayin da suke hakuri da bambance-bambancen dake tsakaninsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp