Aminiya:
2025-06-02@02:01:29 GMT

‘’Yan bindigar birni sun karɓe shugabancin Najeriya — El-Rufai

Published: 31st, May 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya soki tsarin shugabanci na Najeriya na yanzu, inda ya bayyana cewa ‘’yan bindigar birni’ sun karɓe ragamar mulkin ƙasar.

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a Abuja, yayin taron lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, mai taken ‘Amfani da Talauci a Matsayin Makami a Najeriya.

El-Rufai ya bayyana cewa a yanzu ne Najeriya take fuskantar matsalolinta mafiya muni tun bayan samar da ita da matsayin ƙasa ɗaya a shekarar 1914.

“Shi ya sa muke tare muna aiki tare da shirya wani haɗin gwiwa don dawo da Najeriya kan turbar da ta dace saboda ta riga ta kauce hanya,” in ji shi.

Mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwa a Neja sun ƙaru zuwa 151 Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba 

Ya danganta yanayin da ƙasar ke ciki a yanzu da gazawar shugabanci, inda ya ce, ƙasar “ta kai ga wannan mataki ne saboda mun bar ’yan bindiga, da ke zaune a birane, ba waɗanda ke cikin daji ba, sun karɓe ragamar shugabanci.”

Tsohon gwamnan ya ci gaba da nuna damuwarsa game da abin da ya bayyana a matsayin matsalar rashin ƙwarewa a mulki.

Ya ce, “Ina ganin matsalar da muke da ita, wadda ina ganin Gwamna Babangida ya ambata, ita ce muna samun mutane marasa ƙwarewa mu miƙa musu shugabanci. Yawancinsu ba su san abin da za su yi ba. Abin da sani kawai shi ne yadda za su karɓi mulki amma ba su san yadda za su yi amfani da shi ba,” in ji El-Rufai.

Ya kammala jawabinsa da kira ga ’yan Najeriya da su tashi tsaye su zaɓi shugabannin da ke da cikakkiyar ƙwarewa da ƙarfin hali, da kuma jajircewa don ci gaban ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan bindigar birni Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa a harsunan Najeriya 3

Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya.

Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci.

Harsunan huda uku na daga cikin  karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Binciken CGTN Ya Nuna Kaso Kusan 90 Bisa Dari Na Masu Bayyana Ra’ayoyi Na Kokawa Da Makomar “Mafarkin Amurka”
  • SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)
  • Gwamnonin Najeriya Sun Bayyana Alhininsu Bisa Rasuwar ‘Yan Wasan Kano
  • Za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa a harsunan Najeriya 3
  • Gwamnatin Tinubu na amfani da talauci a matsayin makami — Atiku
  • Unity Cup: Yau Nijeriya Za Ta Buga Wasan Ƙarshe Da Ƙasar Jamaica
  • Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Ci Rayukan Mutane 25 A Jihar Rivers
  • MDD: Yankin Gaza Ne Ya Fi Ko’ina Fama Da Yunwa A Doron Kasa
  • NAJERIYA A YAU: Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu?