Aminiya:
2025-10-15@05:47:23 GMT

Amarya ta kashe uwargida da wuka a Katsina

Published: 27th, May 2025 GMT

’Yan sanda sun tsare wata matar aure kan zargin ta da kashe kishiyarta a Ƙaramar Hukumar Daura da ke Jihar Katsina.

Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa matar ta yi wa uwargidarta kisan gilla ne bayan wata hatsaniya da aka samu a tsakaninsu, wanda ya ƙazance har ya kai ga kisa.

Amaryar, mai shekara 23 a duniya, ta yi wa uwargida wannan aika-aika ne ranar Lahadi a unguwar Sabon Gari, daura da Makaranta Firamare ta Daɗi.

DSP Abubakar Aliyu, ya ce a ranar ce bayan mijinsu ya dawo daga kasuwa ya kai ƙara Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Daura cewa ya iske uwar gidansa kwance a cikin jini.

An yanke wa wanda ya yi wa agolarsa fyaɗe ɗaurin rai-da-rai  Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano  NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su

“Ya bayyana cewa an sossoka wa matar tasa wuƙa, lamarin da ya sa DPO ya jagoranci jami’ansa suka je aka kai ta Babban Asibitin Tarayya na Daura, inda likita ya bayyana musu cewa rai ya riga ya yi halinsa,” in ji DSP Abubakar Aliyu.

Ya bayyana cewa a yayin bincike, an kama kishiyar amaryar, kuma ta amsa cewa ita ce ta kashe uwargidar bayan sun ba hamata iska saboda wani saɓani da suka samu.

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Katsina, Bello Shehu ya bayyana cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.

Ya kuma buƙaci jama’a da su guji hawa dokin zuci ko ɗaukar doka a hannunsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Amarya Kishiya uwargida ya bayyana cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Aikin Titin Abuja–Kaduna–Kano Shekara Mai Zuwa

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kammala aikin titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano kafin ƙarshen shekara mai zuwa.

Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka, Barista Bello Muhammad Goronyo, ne ya bayyana haka bayan ya kai ziyara domin duba yadda aikin ke tafiya a ranar Talata.

Barista Goronyo ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba da umarni cewa a tabbatar da kammala aikin cikin lokaci, ganin muhimmancin hanyar wajen haɗa Arewa da Kudancin ƙasar da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Ya bukaci kamfanin da ke gudanar da aikin da ya hanzarta kammalawa kafin wa’adin da aka tsara, tare da gyara ramukan da ke hanyar domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a.

Ministan ya kuma nuna damuwarsa kan halin da masu amfani da hanyar ke ciki, inda ya jaddada bukatar gaggauta cike ramuka da gyaran sassan da ke da matsala domin inganta sufuri da tsaron fasinjoji.

Rel/Ibrahim Idris K/Namoda

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ni na nema wa Maryam Sanda yafiya —Mahaifin mijinta
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Aikin Titin Abuja–Kaduna–Kano Shekara Mai Zuwa
  • Sakin Maryam Sanda shi ne ƙololuwar zalunci —Dangin Bilyaminu
  • ‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Tabbatar Da Masu Sa-kai Kan Sahihiyar Kariya.
  • An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
  • Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)