Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Mayar Da Martani Ga Barazanar Trump Kan Cibiyoyin Nukiliyar Iran
Published: 30th, May 2025 GMT
Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran
Ali Shamkhani mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen siyasa ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta mai tsayayyen tsarin tsaro, al’umma masu tsayin daka, da jajayen layi.
Shamkhani ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa: “Burin isa ga cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma ‘tarwatsa su’ ba komai ba ne illa mafarki da shugabannin Amurka da suka gabata sun kasance sun yi has ashen hakan.
Ya kara da cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta, mai tsarin tsaro mai karfi, mutane masu juriya da jajayen layi. Ya kuma jaddada cewa tattaunawa ita ce hanyar samun ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba tilastawa ko mika wuya ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Kasashen Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran
Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata.
Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata 22 ga watan Yuli 2025, aka gudanar da taron tawagogin kasashen uku.
Mahalarta taron a karkashin inuwar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, sun tabbatar da aniyar kasashensu na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da yin musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar.
Sun kuma jaddada muhimmancin ci gaba da wannan shawarwari domin biyan muradun kasashen uku wajen tinkarar manufofin kasashen yamma, musamman takunkuman Amurka.
Tawagogin sun amince su ci gaba da bude hanyoyin karfafa alakokinsu da kuma ci gaba da gudanar da taruka a nan gaba a matakai daban-daban a cikin makonni masu zuwa, a wani bangare na abin da suka bayyana da “kokarin hadin gwiwa na tallafawa zaman lafiyar yankin da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.”