2025-05-25@18:17:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 85

«Haɗaka»:

    Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce goyon bayan da wasu gwamnonin APC suka nuna wa Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a 2027 bai dame su ba. Ya ce su a cikin ƙungiyarsu ta masu haɗaka sun fi mayar da hankali ne kan talakawa, ba shugabanni ba. Gwamnatin Gombe za ta...
      Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025. Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu...
    Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta soke lasisin gidajen wasannin gala guda takwas bisa karya wasu dokokinta. Idan za a tuna a kwanakin baya hukumar, ta soke lasisin wasu gidajen galar bisa samun su da laifin karya dokar hukumar. Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano Sojoji da ’yan siyasa...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari...
    Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da naɗin sabbin sakatarorin ƙananan hukumomi guda 21 a faɗin jihar.   Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala ya sanya wa hannu, wacce aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.   Ya bukaci sabbin sakatarorin da aka naɗa da su yi...
    Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da masu shirya fina-finai sun cimma matsaya bayan dakatar da wasu fina-finai 22 da suka haɗa da Labarina da Dadin Kowa, Manyan Maga da Garwashi. An bai wa masu shirya fina-finan wa’adin mako guda daga Litinin 19 zuwa Lahadi 25 ga watan Mayu 2025 domin miƙa fina-finansu don tantancewa...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin dakatar da wani hadiminsa, Ibrahim Rabi’u nan take daga muƙaminsa.  Abba ya dakatar da hadimin ne wanda yake ɗauko masa rahoto a ma’aikatar sufuri, saboda wasu kalamai da ya furta kan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya murƙushe ƙungiyar Boko Haram lokacin da ta fara bayyana a shekarar 2002. Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Jihar Kogi a birnin...
    Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.   Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma...
    Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyar yayin da suka kai hari ana tsaka da cin kasuwa a ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato. A cewar mazauna, maharan sun wawushe kayayyaki a shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna masu tarin yawa. Jami’ar...
    Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba.   Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.  ...
    Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal.  Ya ce,...
    Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.   Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata...
    Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kama wasu jami’an tsaro huɗu da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas. Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu jami’ai biyu na rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojoji domin yaƙar ’yan ta’addar. ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe  An kama masu garkuwa...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, tare da wasu manyan muƙamai guda huɗu. Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Hakimin Nassarawa, wanda ya zama sabon Wamban Kano; Alhaji Mahmud Ado Bayero Hakimin Gwale, wanda aka naɗa a matsayin...
    Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya. A ranar 9 ga Afrilu,...
    Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a...
    Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero, a matsayin Galadiman Kano, bayan rasuwar Abbas Sanusi. A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, wanda ke ta ƙaddamar kan sarautar Kano da Aminu Ado Bayero a gaba kotu, ya naɗa Mannir Sanusi a...
    Matsalar faɗace-faɗacen daba da kuma ƙwacen waya na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba ba ko na ƙwacen waya a sassan jihar ba, abin da ke sanya fargaba a zukatan al’umma. Munin...
    Wannan naɗi ya zama wani babban mataki a cikin mulkin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiyaye al’adun masarautar tare da haɗa kan al’umma. Sai dai kuma a cikin wannan wata ne Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido Sanusi II, ya fara naɗa Alhaji Mannir Sanusi (Hakimin Bichi) a wannan muƙami...
    A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi. HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa...
    Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cika hannu da wani matashi da aka gani a wani yanayi mai kamanceceniya da baɗala da wata Akuya, lamarin da ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta. Matashin, Shamsu Yakubu mai shekaru 24 da ke zaune a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta Kano, ya shiga hannu ne bayan ɓullar...
    An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya. Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu. An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne...
    Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne...
    Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar...
    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ziyarar da Atiku ya kai...
    Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka.   Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu.   Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali...
    Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal. ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar...
    Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa. Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an. Gidauniyar Zakkah ta raba wa...
     Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa. An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da...
    A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa....
    Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za...
    Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood....
    Ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da haƙuri da fahimtar juna domin haɗa kai tare da tabbatar da goyon baya ga jam’iyyar. A nasa ɓangaren, Sakataren APC na Zamfara, Hon. Ibrahim Umar Dangaladima, ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu da Minista Matawalle bisa wannan tallafi. Ya ce shinkafar ta zo a daidai...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantad da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers. Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, da Shugaban Ma’aikatan Fadar  Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da wasu hadiman Shugaban Kasa sun halarci wannan gajeren bikin rantsuwar da aka gudanar a Fadar Gwamnati a...
    Da wannan sabon matsayi, Farfesa Pate, zai haɗa kai da sauran ƙwararru da ke aiki domin tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da inganta shigar da al’umma cikin harkokin shugabanci, wanda ake kyautata zaton ƙwarewarsa za ta taimaka wajen tsara sabbin hanyoyi da cibiyar WSCIJ za ta amfana.   WSCIJ, wacce an sanya mata suna daga...
    Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, mahaifinsa ne kaɗai shugaban ƙasar da ba shi da burin azurta kansa da kuɗin talakawa. Har wa yau ya ƙara da cewa shi kaɗai ne shugaban da ke bai wa matasa damammaki a gwamnatinsa. Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano Ana zargin...
    Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyuka Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja.  Taron ganawar wanda ya haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da...
    An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci. Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai...
    Shugaban Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Mista Peter Tanko Dogara, ya tabbatar da aniyarsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya domin samar da tsaro da samar da ayyukan ci gaban ƙaramar hukumar. Mista Dogara ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai zuwa ga masarautu...
    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta noma, sufuri da ma’adanai na jihar.   A ranar Talata ne gwamnan ya karbi baƙuncin masu kamfanoni na ƙasar Sin a gidan gwamnati da ke Gusau.   A wata sanarwa da mai magana da yawun...
    Sabbin hadiman da aka naɗa za su fara aiki nan take, tare da kawo sabbin dabaru domin inganta sadarwa a gwamnatin jihar. Wannan shiri kuma na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafawa matasa guiwa da rage rashin aikin yi a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi. Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura...
    ’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines,  Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar. Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong. Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet...
    Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba. Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina. Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin. Yadda za a samu rufin asiri...