2025-07-08@19:05:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6522

«majalisar Amurka»:

    Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta Nijeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’in ƙasar. Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja. An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC Haka kuma, ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin samun gurbin kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100. Alƙaluma dai sun tabbatar da cewa an samu gagarumar faɗuwa a jarawabar...
    Wani jami’in sojan HKI ya yi furcu a karon farko cewa, martanin Iran ya shafi cibiyoyinta na soja. A yau Talata ne jami’in sojan na HKI ta yi furuci irinsa na farko cewa martanin da Iran ta mayar a watan da ya shude, ya shafi sansanonin soja.  Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ne ya ambato jami’in sojan na ‘yan sahayoniya yana yin wannan sharadin bisa sharadin kar a ambaci sunansa. Harin wuce gona da iri na HKI a ranar 13 ga watan Yuli ya shafi kwamandojin soja da masana fasahar Nukiliya. Martanin jamhuriyar musulunci na Iran akan kallafaffen yakin HKI ya shafi cibiyoyin soja, leken asiri, wuraren binciken masu alaka da soja. Iran ta yi amfani da jiragen yaki marasa matuki...
    Hukumar abinci ta duniya ta fara aikewa da kayan abinci zuwa kudancin Sudan, ta hanyar amfani da jiragen sama domin jefa kayan agaji ga mazauna Kudancin Sudan da sauran yankunan da suke a killace tun cikin watan Maris. Tun watanni 4 da su ka gabata ne dai hukumar abincin ta duniya ta fara aikewa da kayan agaji a kudancin Sudan din, bayan da fada mai tsanani ya hana a iya bi ta hanyoyin kasa. A gefe daya, shugabar kungiyar ta Abinci reshen Afirka Mary Elen macgroti ta ce, fada da ake ci gaba da yi a yankin ya haddasa karacin ab inci, tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa domin magance wannan matsala. Da akwi mutane kusan miliyan...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa, tana nazarin sabuwar gayyatar da Amurka ta yi mana na komawa teburin tattaunawa.  Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto wata majiya mai karfi tana cewa, bayan da Amurka ta kasa dakatar da Shirin kasar na makamashin Nukiliya, ta aiko ma ta da takardar gayyata domin yin zama da ita akan teburin tattaunawa. Majiyar ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fada wa kamfanin dillancin labrun “Mehr” cewa, Amurka ta aiko da sakwanni ta hanyar ‘yan aike na kasashe masu yawa.” Ma’aikatar harkokin wajen ta Jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin nazari akan hakikanin abinda Amurkan take so, da kuma yadda tattaunawar za ta kasance wacce za ta zama ta dage takunkumai, da...
    Fim din  Iran mai taken: Akharin Kuse Nahang” wanda Ramtin Balf ya shirya shi ya samu kyauta a baje kolin fina-finan ta Shangahi. Shugaban ma’aikakar al’adu da koyarwar musulunci ta Iran a yankin Bu-Shehr Muhammad Hussain Zaduyan ya sanar da cewa; Fim din wanda na ilmantarwa ne, yana daga cikin fina-finai masu muhimmanci da aka fitar da shi a Iran. Shi dai wannan bikin  na baje kolin fina-finai a Shanghai an yi shi ne daga ranar 3 ga watan Yuli zuwa 7 ga gare shi a wannan shekarar ta 2025. An yi wannan bikin ne na baje-koli ne a daidai lokacin da ake yin taron kungiyar “BRICS” da taron kasashen Asiya. Zanduyani ya kuma ce; Fim din na Iran wanda...
    A matsayin sabon babban manaja, Musa ya buƙaci haɗin kai da goyon bayan kowa don tabbatar da gaskiya da amana a dukkan harkokin kulob ɗin. Ya kuma roƙi magoya bayan ƙungiyar su ci gaba da marawa kulob ɗin baya a wannan sabuwar tafiya ƙarƙashin jagorancinsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya fada a yau Talata cewa, kasar Sin a shirye take ta kara bayar da goyon baya da zurfafa hadin gwiwa da MDD, domin neman tabbatar da jagorancin duniya mai cike da adalci da daidaito. Li ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da babban sakataren MDD Antonio Guterres, a gefen taron kasashen BRICS karo na 17. Ya kuma yi kira ga MDD da ta taka rawar gani a duniyar da take fama da tashin-tashina, yana mai gargadin cewa, duniya na fuskantar karuwar rashin kwanciyar hankali da rashin tabbas. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kananan hukumomin lardin Shanxi, tare da gabatar da wasu bukatu na ayyuka na mataki na gaba na wurin. Xi ya ce, gina wani yankin gwaji na gyare-gyare na kasa, domin kawo sauyi kan tattalin arziki bisa albarkatun kasar, wani muhimmin aiki ne da kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin ya dorawa lardin Shanxi, don haka ya kamata a mai da hankali kan sauyin makamashi, da habaka masana’antu, da kuma samu ci gaba da ya dace. Bugu da kari, Xi ya jaddada cewa, dole ne a tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali yayin kawo sauyin ci gaba. Dole ne mu mai da hankali kan daidaita ayyukan yi, masana’antu, kasuwanni,...
    Wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ta samu nasarar kuɓutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su da shanu da aka sace a Jihar Kebbi. Bayanai sun ce an sace mutanen da dabbobin ne a ƙauyukan Ukuhu da Kokanawa a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar. ‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’ Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC Wani daraktan tsaro a Gwamnatin Kebbi, Abdurrahama Zagga ne ya sanar wa manema labarai nasarar da aka samu a ranar Talata, inda ya ce an kai samamen ne bayan umarni da aka samu daga Gwamna Nasiru Idris bisa bayanan sirri da aka tattaro a yankin. A cewar Zagga, tawagar jami’an tsaro...
    Tsohon Ministan Sufuri, Idris Umar, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ce za ta ceto Najeriya daga halin da take ciki, tare da mayar da APC jam’iyyar adawa a Zaɓen 2027. Yayin wani taron haɗin gwiwar jam’iyyu na adawa a Gombe, an amince da amfani da ADC a matsayin dandalin siyasa na bai ɗaya domin fuskantar zaɓen 2027. Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi Taron ya gudana a Shugleez Event Centre wanda ya samu halartar fitattun ‘yan adawa daga sassa daban-daban na jihar. Idris ya ce za su yi haɗakar ce ba wai kawai don karɓar mulki ba, sai dai domin ceton...
    Ahmed Musa ya ce zai buƙaci haɗin kai daga duk masu ruwa da tsaki domin ciyar da ƙungiyar gaba. Ya kuma ce zai taimaka wajen samar da kayan aiki da tallafin da ƙungiyar ke buƙata domin ta yi fice a sabuwar kakar wasa mai zuwa. Ya ce: “Ina tabbatar wa kowa cewa da goyon bayanku da na mambobin hukumar, zan yi iya ƙoƙarina don dawo da Kano Pillars matsayin ya kamata a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi ba kawai a Afirka ba, har ma a duniya.” Ƙungiyar Kano Pillars, wacce ta taɓa lashe kofin NPFL sau huɗu, ta fara shirin tunkarar kakar wasa ta shekarar 2025/2026. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Amurkawa sun jefa bama-bamai a kan teburin tattaunawa tare da lalata harkar diflomasiyya Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce Iran na gudanar da shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, amma sai suka jefa bama-bamai a kan teburin tattaunawa tare da lalata hanyar diflomasiyya. A wata hira da Tucker Carlson mai watsa labarai na Amurka, shugaba Pezeshkian yayi magana da Carlson cewa: Mr. Carlson! Mun kasance a kan teburin shawara kuma ana cikin tattaunawa saboda shugaban Amurka ya kira zuwa ga zaman lafiya kuma a wannan taron sun gaya mana cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta kai wani hari ba. Pezeshkian ya kara da cewa: Amma a jajibirin taro na shida, muna cikin...
    Kakakin hafsan hafsoshin sojojin Iran ya ce; Iran tana dora wa Amurka  alhakin duk wani hari da za a kai mata Kakakin hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Birgediya Janar Abul-fazl Shekarchi ya jaddada cewa: Iran tana dorawa Amurka alhakin duk wani harin wuce gona da iri da za a kaddamar kan kasarta. A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Shekarchi ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran ba su ne suka kaddamar da harin kan wata kasa ba, amma sun mayar da martani cikin kwanaki 12 na arangama da munanan hare-hare da suka fuskanta daga mabartan ‘yan sahayoniyya makiya. Ya kara da cewa, “An sanya wa makiya tsagaita bude wuta ne bayan da suka fuskanci...
    Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin...
    Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.   Yana...
    Falasdinawa 13 ne suka yi shahada da suka hada da yara kanana da mata a hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gidaje da matsugunan Falasdinawa a Gaza Sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza da asubahin ranar Talata, inda suka kai hare-hare kan gidajen fararen hula da matsugunan ‘yan gudun hijira. Hare-haren sun yi sanadiyyar shahadan  fararen hula 13 da suka hada da yara da mata, yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu munanan hare-hare ta sama da aka kai a yankuna daban-daban na zirin. Asibitin Al-Shifa ya sanar da shahadan Falasdinawa hudu ciki har da wani jariri, sakamakon harin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai a wani...
    Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An bukaci masu hannu da shuni da ‘yan kasuwa da ma daidaikun jama’a su rika tallafawa mata da matasa da dukkanin abin da Allah ya hore mu domin ganin sun iya dogara da kansu. Kogunan Kasar Hausa Alhaji Aliyu Da’u Abubakar ne yayi wannan kiran a wajen bada tallafi ga mata da matasa fiye da dari hudu da Kungiyar Matasan Abban Gandun Albasa Kano ta shirya a Kano. Kogunan Kasar Hausa ya bayyana cewa irin wannan tallafi zai taimaka matukar gaske wajen karfafa mata da matasa su tsaye da kafafun su. Yayi bayanin cewa babu shakka wadannan matasan zasu dogara da kansu kana da daukar dawainiyar iyalansu da wannan tallafi. Taron da aka gudanar a asabar ta karshen mako ya...
        Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bukaci hukumomin tsaro da Sarakuna da kuma kungiyoyin matasa su dauki matakan gaggawa wajen dakile gina gine-gine a karkashin manyan layukan lantarki da kuma hana lalata kayan hasken lantarki.   Babban Manajan TCN na Yankin Kaduna, Injiniya Nasir Mansur Fada, ne ya yi wannan kira a yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar da masu ruwa da tsaki a hedikwatar TCN da ke Mando, Kaduna.   Taron ya samu halartar Sarakuna da jami’an tsaro da kungiyoyin masu zaman kansu domin bin umarnin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa domin ci gaba da kokarin da TCN kiyi na dakile mamaye filayen layin lantarki da kare dukiyoyin kasa.  ...
    “Wannan yajin aiki ba wata sabuwar tattaunawa ba ce,” in ji shi. “Abin da muke yi kawai martani ne ga halin ƙunci da mambobinmu ke ciki. Ofishin Akanta-Janar na ƙasa ne ke jinkirta biyan albashin da gangan.” ASUU ta ce ta riga ta gana da hukumomin gwamnati don bayyana matsalolinta, amma ba a ɗauki mataki ba. Farfesa Piwuna, ya kuma ƙara da cewa har yanzu malaman jami’a na bin gwamnati Naira biliyan 10 daga cikin Naira biliyan 50 da za a biya su a matsayin haƙƙoƙinsu (Earned Academic Allowances – EAA). Ya gargaɗi gwamnati cewa duk wata jami’a da ba a biya malamanta albashi ba, za ta ci gaba da yajin aiki har sai an warware matsalar. Daga kanmu,...
    “Mun riga mun binne sama da mutum 60 a Kukawa kaɗai,” in ji shi. “Wadanda suka tsira sun ce ‘yan bindigar sun fi ƙarfinsu.” Wani mazaunin ƙauyen Bunyun da ke gundumar Nyalun a ƙaramar hukumar Wase, Musa Ibrahim, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyensu, inda suka kashe ‘yan sa-kai 10 da ke tsaron yankin. Musa ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun ƙone gidaje da dama a ƙauyen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta zargi kasar Amurka da nuna adawa da kungiyar BRICS ta raya tattalin arziki na kasashen kungiyar ta kuma kara da cewa kokarin kare kanta da ga shirye-shiryen BRICS ba zai amfane ta ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar China na cewa kungiyar kungiya ce wacce bata son babakere da Amurka take nunawa a yadda take tafiyar da al-amura a duniya kamar Ita ce, take iko da kowa. Tace kungiyar tana son duniya ta zama mai kudubobi, wadanda su ma za’a iya fada su kuma aikata abinda suke so karkashin dokokin duniya. Don haka mamayar da takardan dalar Amurka ta yiwa mafi yawan...
    Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas arachi ya bayyana cewa mutanen kasarsa a shirin suke su ci gaba da kare kasarsu daga Amurka da kuma HKI . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da tawagar kasar Brazil a gefen taron kungiyar BRICS karo 17 wanda ke tafiya a halin yanzu a birnin Rio de Jenero na kasar Brazil. An gudanar da wannan taron ne saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa JMI a baya bayan nan, da kuma tasirinsa a cikin al-amuran siyasa da kuma tattalin arziki a yankin Asiya ta yamma da kuma duniya gaba daya. Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren...
    Wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta a nan Iran ta fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa a ziyarar da Benyamin Natanyaho yake yi a halin yanzu a kasar Amurka ya nuna cewa yana son ci gaba da yaki da kasar Iran sannan da alamun shugaba Trump yana tare da shi. Labarin ya kara da cewa matsayin shuwagabannin biyu a yanzun bai da bambanci da matsayinsu bayan yakin kwanaki 12. Majiyar ta bayyaa cewa Iran a shirye take ta kare kansa, kuma tana ganin ziyarar da Natanyahu yake a Amurka duk yaudara ce, saboda tuni sun rika sun yanke shawara kan ci gaba da yaki. Dangane da sake dawowa kan teburin tattaunawa da Amurka kuma,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin  wajen kasar Iran Isma’el Baka’e ya yi allawadai da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu yankuna a kasar Yemen a ranar Lahadi. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya litinin ya kuma yi tir da hare-hare kan a Hudaydah, Ras-Isa, as-Salif da kuma tashar wutan lantarki na Ras al-Kathib. Har’ila yau Baka’ee ya yi allawadai da kai hare-hare kan cibiyar tattalin arziki na kasar ta Yemen a Hudaida, wadanda suka hada da kayakin jama’a wadanda suka hada da gadoji da hanyoyiu da tashar Jiragen sama, da tashar jiragen ruwa da kuma rumbunan ajiyar abinci. Wandanda gaba dayansu yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Hare-harin...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu a takardan doka ta soke kungiyar yan ta’adda ta Jihatun Nusra, wacce ake kira Hay’at Tahrirusham a matsayin kungiyar yan ta’adda a duniya. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya, ya bayyana cewa shugaban ya cire HTSH daga jerin kungiyoyin yan ta’adda ne, saboda taimakawa kungiyar tabbatar da ikonta a kan kasar Siriya ta kuma share fagen dauke wa kasar takunkujman tattalin arzikin da aka dorawa kasar. Labarin ya kara da cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ne ya sanya hannu a kan takardan cire shugaban kasar Siriya mai ci Ahmed Al-Sharaa ko wanda aka fi sani da Jolani daga jerin yan ta’adda a duniya. Wanda kuma...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan  wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027.   Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane. Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027? NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ɗan wasan gaban Napoli, Victor Osimhen, ya amince da komawa Galatasaray na dindindin, wani ɗan jarida a Nijeriya kuma makusancin Osimhen, Buchi Laba ne ya bayyana hakan. Ya ce “Osimhen ya bayyana cewa yana son komawa Galatasaray daga Napoli, duk da cewar ƙungiyar ta ƙasar Italiya na fatan ci gaba da kasancewa da tsohon ɗan wasan na Lille, Bula ya rubuta a shafinsa na X. Manyan Kugiyoyin Gasar Firimiya Sun Fara Zawarcin Victor Osimhen Rashin Osimhen A Cikin Tawagar Nijeriya Babbar Asarace – Samson Siasia Yayin da yake zaman aro a Galatasaray, Osimhen ya taimakawa ƙungiyar ta lashe gasar Super Lig ta Turkiyya, ɗan wasan na Super Eagles ya zura ƙwallaye 25 a wasanni 36 da ya buga, hakan yasa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe. Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan kasa da shekaru biyar sama da 38,000 a fadin jihar. Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Gwamnan ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba yayin da ya kaddamar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin fadada harkokin kiwon lafiya, musamman ga marasa galihu. Ya bayyana hakan ne a ranar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar raya kasa da aiwatar da gyare gyare ta kasar Sin (NDRC) ta ce kasar za ta kara daukaka tsarin wuraren cajin lantarki da gina tsarin ta yadda zai zama mai inganci da ingantaccen lantarki da kyakkyawan fasali, da amfani da fasahohin zamani. NDRC da wasu hukumomin gwamnati 3 sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa game da bangaren a yau, inda suka ce wuraren cajin ababen hawa masu amfani da lantarki na da muhimmanci matuka wajen goyon bayan raya masana’antar kera ababen hawa masu amfani da lantarki da ginin sabon tsarin samar da lantarki tare da rage fitar da hayakin Carbon a bangarorin sufuri da na makamashi Zuwa karshen shekarar 2027, kasar Sin na sa ran samun sama da...
    Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe. Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan kasa da shekaru biyar sama da 38,000 a fadin jihar. Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Gwamnan ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba yayin da ya kaddamar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin fadada harkokin kiwon lafiya, musamman ga marasa galihu. Ya bayyana hakan ne a ranar...
    An gudanar da taron kafa kungiyar masana masu binciken sararin samaniya mai zurfi ta kasa da kasa wato IDSEA a birnin Hefei dake lardin Anhui, yau Litinin. Wannan ita ce kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasa da kasa ta farko da kasar Sin ta kafa a fannin binciken sararin samaniya mai zurfi. A cikin watan Afrilun bana ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da kafa kungiyar IDSEA, wadda kungiyoyi guda 5 suka ba da shawarar kafa ta tare, ciki har da cibiyar binciken duniyar wata da ayyukan binciken sararin samaniya ta hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, da cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Faransa mai suna “Planetary Exploration, Horizon 2061.” Kuma ta zama wata kungiya...
    ‎Wata ƙungiya mai zaman kanta, Nigeria Health Watch ta ce ta gano har yanzu fiye da rabin matan da ke zaune a yankunan karkarar Jihar Kano sun fi son haihuwa a gida a maimakon zuwa asibiti. ‎Kungiyar ta alaƙanta hakan da al’adun mutanen, waɗanda ta ce an fi samun masu su a ƙauyuka da kuma yankunan karkara fiye da a birane. ‎Daraktar shirye-shirye ta ƙungiyar, Kemisola Agbaoye ce ta bayyana hakan ranar Litinin, yayin gabatar da rahoto a wani taron masu ruwa da tsaki don bayyana abubuwan da suka gano a binciken da suka gudanar a ƙananan hukumomi shida na jihar. Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Yangquan na lardin Shanxi a yau Litinin. Shugaban ya ziyarci dandalin da aka kebe domin tunawa da katafaren gangamin soji na yaki da harin Japan, inda ya gabatar da furanni ga wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin. Ya kuma ziyarci babban dakin tunawa da gangamin. Shugaban ya kuma yi bitar irin jarumtar da sojojin suka yi yayin yakin da kuma tarihin yadda JKS ta jagoranci sojoji da al’umma wajen hada kai domin yakar ‘yan adawa da bijirewa kutsen Japan, da fahimtar tarihin juyin juya hali a wurin da gado da yayata ruhin yakin kin harin Japan. Daga baya, ya je wani kamfanin kere-kere na valve dake birnin, inda ya fahimci...
    (ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu  Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
    (ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu  Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
    Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar...
    Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda take bazuwa cikin sauri a kwanakin nan. Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci A cewarsa, ’yarsa da ta nuna alamun kamuwa da cutar na kumburin wuya da sarkewar numfashi, an gaggauta mika ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, amma daga bisani ta ce ga...
    Kasar Sin ta gudanar da bikin cika shekaru 88, da dukkan al’ummar kasar ta fara yakin kin jinin harin sojojin Japan a yau Litinin. Inda a wani bangare na bikin aka kaddamar da wani baje koli mai taken “Domin ‘yantar da kasa da zaman lafiyar duniya”. An gudanar da bikin tare da baje kolin ne a babban dakin adana kayayyakin tarihi masu nasaba da yakin, wanda ke kusa da gadar Lugou, wadda kuma ake kira da “Marco Polo Bridge”, wurin da sojojin Japan suka fara kaiwa sojojin kasar Sin hari a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937, lamarin da ya zamo tushen mamayar da sojojin na Japan suka yiwa kasar Sin. Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS,...
    Kamfanin jirgin sama mallakar jihar Enugu, wato Enugu Air, ya fara aiki a hukumance ranar Litinin bayan ƙaddamar da shi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu. Mutane da dama sun halarci bikin ƙaddamarwar tare da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da sauran manyan baki da suka halarci bikin ƙaddamarwar. APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu  Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Enugu Air wani ɓangare ne na hangen nesa da ƙudurin Gwamna Peter Mbah, don inganta harkar sufuri da mayar da Enugu cibiyar jiragen sama a Nijeriya. Kamfanin ya fara aiki da jirage uku na Embraer E170 da E190, wadanda suka dace da zirga-zirgar cikin gida. Jirgin zai fara tashi tsakanin...
    A yau Litinin ne kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa wacce ta kunshi yin Allawadai da harin ta’addancin da HKI ta kai wa kasar Yemen, wanda ya shafi tasoshin jiragen ruwa da muhimmacin cibiyoyin kasar. Bayanin na Hizbullah ya kuma ce; Makiya suna tsammanin cewa ta hanyar wannan irin harin na wuce gona da iri za su yi hana Yemen ci gaba da matakin da take dauka na daukaka wajen taimakawa Gaza, ta daina kai hare-hare masu tsanani da take kai musu. Haka nan kuma Hizbullah ta ci gaba da cewa: Har yanzu ‘yan sahayoniya sun kasa fahimtar dabi’ar mutanen Yamen masu hakuri da juriya akan tafarkin jihadi, domin akida ce, cewa gaskiya ita ce wacce ta cancanci a...
    Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Kenya sun ce tun safiyar yau Litinin ne ‘yan sanda su ka rufe muhimman hanyoyin da su ka nufi tsakiyar babban birnin kasar Nairobi da kuma muhimman cibiyoyin kasuwanci. Kafafen watsa labarun kasar ta Kenya sun ce da akwai jami’an ‘yansanda masu yawa da aka girke su a cikin muhimman wurare da shatale-tale a cikin birnin da kuma hanyoyin da suka nufi fadar gwamnati.  Dubban mutane ne su ka fito titunan birnin Nairobi domin nuna kin amincewarsu da salon Mulki William Ruto wanda suke zargi da cin hanci da rashawa da kuma kama karya. Zanga-zangar ta yau dai ana ba ta sunan; 7/7, wacce ta samo asali a 1990 da al’ummar kasar su...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida, “Shabak” ta kama shugaban ofishinta a Falasdinu dake karkashin mamaya  Nasir al-Lahham, a gidansa da yake a garin Beithlaham. Majiyar ta kara da cewa; Jami’an kungiyar leken asirin ta “Shabakh” sun dade suna binciken dakin watsa labarin da Lahham yake watsa shirye-shiryensa. Tashar ta “Almayadin’ dai ta bayyana cewa kamun da aka yi wa ma’aikacin nata yana a karkashin Takura mata ne da HKI take yi, domin a cikin watan Oktoba na 2023 ma dai jami’an tsaron sun kai hari cikin gidansa, su ka ci zarafin maidakinsa da kuma kama ‘ya’yansa Basil da Baasil.
    A nasa bangaren, Abiy ya ce Habasha da Sin amintattun kawaye ne na manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma kasarsa tana mika tsantsar godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da ta dade tana bai wa Habasha a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa. Yayin da yake nuni da irin muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa, musamman a fannin raya ci gaban duniya, Abiy ya ce Habasha a shirye take ta rubanya mu’amala a matakin koli da kasar Sin da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Saboda matsin lamba na doka da kuma la’akari da mahimman batutuwan siyasa, ya zama dole Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da duk wani ci gaba na aikin kwamitin da aka kafa a ranar 4 ga Yuli 2025 domin duba yiwuwar ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauye-sauye ga tsarin majalisun gargajiya—musamman a yankunan da har yanzu ke fuskantar shari’a a kotu. Ci gaba da wannan lamari mai sarkakiya alhali wasu muhimman ƙarar shari’a na ci gaba a kotuna, ba wai kawai zai saɓa wa kundin tsarin mulki da ikon shari’a ba, har ila yau, zai iya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a cikin al’umma, musamman a yankunan da ke da tarihi na rikice-rikicen ƙabilanci kamar Tafawa Balewa da kewaye. Wannan kira na...
    Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta ware dala miliyan 130 a kasafin kudinta na 2026 karkashin Yaƙi da ISIS da Kudin Kayan Aiki (CTEF) don taimaka wa kungiyoyi masu dauke da makamai a Syria, cikin su har da SDF da YPG ta mamaye. Wannan dai na zuwa ne a yayin da Siriya ke ci gaba da fuskantar rashin kwanciyar hankali da kalubale masu yawa tun bayan kawo karshen mulkin Bashar al-Assad. Bidiyon tsiraici: Babiana ta sake jawo ce-ce-ku-ce Madatsar Ruwan Lagdo na yi wa jihohi 3 na Nijeriya barazanar ambaliya Manyan matsaloli sun haɗa da kasancewar kungiyoyi masu dauke da makamai daban-daban, rikice-rikicen filaye da ba a warware ba, tsoma bakin sojojin ƙasashen waje, da tattalin arziki mai rauni wanda ke...
    A ƙarshe, lauyoyin Majalisar sun ja hankalin lauyoyin Sanata Akpoti-Uduaghan da su yi taka-tsantsan don kauce wa yi wa kundin tsarin mulki kutse ko sanya rikici a majalisa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ƙarshen makon da ya gabata ne fitacciyar ’yar TikTok wacce aka fi sani da Babiana ta fitar da wani sabon bidiyo tana rusa ihu tana kira ga Shugaba Bola Tinubu da wasu mawaƙan kudancin Najeriya da su shiga tsakaninta da ’yan Arewa a kan abin da tace suna yi mata na cin zarafi tun bayan bayyanar bidiyo tsiraicinta a shekarar 2024. Babiana ta yi bidiyon ne cikin harshen Ingilishi inda ta ce ba a yi mata adalci a Arewa kuma ana barazana da rayuwarta. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Ta bayyana cewa tsawon shekara ɗaya ta yi tana raɓe-raɓe saboda ba ta son maganganun...
    Rahotanni sun bayyana cewa mazauna wasu jihohin Nijeriya uku na cikin shirin ko-ta-kwana, sakamakon ƙaruwar fargabar samun ambaliya saboda yiyuwar sakin ruwan Madatsar Lagdo ta Kamaru. A cewar wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, jihohin da mazauna ke cikin zaman ɗar-ɗar sun haɗar da Benuwe da Edo da kuma Bayelsa, waɗanda tuni suka fara shiri don kauce wa barazanar ambaliyar. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Sai dai Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Nijeriya ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa an buɗe madatsar ruwan, a yayin da tuni jihohin suka fara shirya wa barazanar. Gwamnatin Benuwe ta ce ta fara aikin wayar da kan...
    A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai wajen tabbatar da tsafta da kuma bayar da rahoton duk wani da ake sayarwa da ba bisa ka’ida ba, ko kuma cikin rashin tsafta. Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Adamu Sabo ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan kira ya zama wajibi sakamakon nasarar da hukumar ta samu na kwace gurbatattun kayayyakin na sama da naira miliyan 14 a lokacin sintiri da binciken kayayyaki a fadin jihar daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025. Alhaji Adamu Sabo ya kara da cewa, mafi yawancin kayayyakin da aka kwace na...
    Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine. Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye wurin aikin ne da safe, inda suka yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a wurin. An bayyana cewa bayan harin, maharan sun ajiye motarsu a kusa da tashar watsa shirye-shiryen Radio Kogi da ke Otite, da nisan ‘yan mitoci kaɗan daga inda suka sace ɗan Chinan. CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara...
    Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji  ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato. Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita. Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari. ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno Turji: Gwamnatin Sakkwato ta ba da sharadin sulhu da ’yan ta’adda Wani mazaunin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025. Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano. Ya ce wannan karamci na gwamnatin jihar Kano shaida ce ta jajircewarta wajen kula da walwalar fursunoni, gyaran dabi’unsu da kuma dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata. “Biyan kudin rajistar jarrabawa da gwamnatin Kano ta yi alama ce ta jajircewarta wajen samar da dama ga fursunoni domin su...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana kuma ya zanta da wani babban malamin yahudawa mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron kasashen BRICS a kasar Brazil. Rabbi Yisrael Dovid Weiss, wanda ya je Brazil domin ganawa a gefen taron BRICS, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, inda suka yi musayar ra’ayi da shi. Wani abin lura shi ne cewa a baya malamin ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Brazil bayan bude littafin ta’aziyya ga shahidan da yahudawan sahayoniyya da suke kai wa hari a                                                                    kasar hari. A...
    Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji  ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato. Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita. Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari. Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin.
    Shugaban kasar Rasha ya aike da sako mai zafi wa kasashen Yammacin Turai da suke tallafawa Ukraine A daidai lokacin da yakin Rasha da Ukraine yake ci gaba da ruruwa, kuma har yanzu an gagara cimma tsagaita wuta. Sabbin abubuwan da suka faru a fagen sojan Rasha sun hada da ma’aikatar tsaron kasar da ta sanar da cewa sojojin kasar sun ‘yantar da garuruwan Poddubnoye na Donetsk People’s Republic da Sobolevka a yankin Kharkiv. Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin kasar Rasha sun ci gaba da zurfafa kai hare-hare kan makiya, inda suka yi ta janyo hasarar bil’adama da na dukiya kan sojojin kasar Ukraine a yankuna da dama na jamhuriyar Donetsk People’s Republic da...
    Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan  tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan tashar ruwan Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen, biyo bayan barazanar da sojojin kasar suka yi a yammacin jiya Lahadi. Majiyar Yemen ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa: An ji karar fashewar abubuwa masu yawa a tashar jiragen ruwa na Hodeida, sakamakon farmakin da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankin. A cewar majiyoyin cikin gidan Yemen, sama da fashe fashe 20 ne aka samu a Hodeidah sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin Isra’ila suka kai.
    Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin  gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen. Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa...
    Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya. Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai. Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa. A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.
    Mummunan lamari ya faru ne a lokacin da wata mota kirar bas ta kasuwanci da wata babbar mota ta yi taho-mu-gama da tare da daukar rayukan mutane 21 a hanyar Zariya zuwa Kano.   Hadarin ya afku ne a Kasuwar Dogo, Dakatsale, wanda ya hada da wata motar kasuwanci kirar Toyota Hiace da wata tirela ta DAF.   Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa direban motar bas din ya saba ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa, lamarin da ya kai ga yin karo da babbar motar da ke zuwa.   Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji 21 nan take, wadanda suka hada da manya maza 19 da manya mata 2, yayin...
    Hukumomi a jihar Texas da ke Amurka sun tabbatar da mutuwar fiye da mutum 80 sakamakon ambaliyar da ta auka wa jihar tun a ranar Juma’a. Mutum 68 daga cikin waɗanda suka mutu ciki har da ƙananan yara 28, a gundumar Kerr suke. Har yanzu akwai ƴanmata 10 da mai kula da wurin shaƙatawar Mystic da ba a ji ɗuriyarsa ba. Alƙaluman waɗanda suka mutu na sauyawa cikin hanzari, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da lalubo gawarwaki. Shugaba Trump ya ce ya tsara zuwa yankin da lamarin ya faru cikin wannan mako
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar.   AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a wani taro da aka gudanar a Ilorin.   Gwamnan ya amince da damuwar al’ummar tare da tabbatar musu da matakin da gwamnati ke jagoranta kan lamarin.   Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare a dazuzzukan da aka gano a matsayin sansanin ‘yan ta’adda a Kwara ta Arewa da Kudu.   Gwamna AbdulRazaq ya ce ayyukan za su hada da sabbin...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta gudanar da aikin samar da wutar lantarki ga jami’ar tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe domin tabbatar da samar da isasshen wutar lantarki domin inganta harkokin ilimi.   Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron hadaka karo na uku na jami’ar tarayya ta Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe.   Shugaba Bola Tinubu ya kuma bayyana cewa ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya za ta fara aikin gina madatsar ruwa a kogin Kashere domin tallafa wa shirin koyar da aikin gona na jami’ar da inganta samar da ruwa ga al’ummomin da ke kewaye.   Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta samar da ingantaccen ilimi ta hanyar...
    A ƙarshe, Farfesa Pate ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gina sabbin gine-gine a jami’ar kamar ginin Majalisar Jami’a, katangar jami’a, da ɗakunan kwana. Ya bayyana cewa dalibai 6,870 ne suka kammala karatu, ciki har da 91 da suka samu First Class da kuma 16 da suka kammala karatun digiri na PhD. Haka kuma, jami’ar ta karrama mutane biyar da digirin girmamawa saboda gudummawarsu ga ci gaban kasa da ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44.   Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki.   Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara.   “Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake halattan taron kungiyar raya tattalin arziki ta Bricks ya yabawa kungiyar kan yin tir da Amurka da kuma HKI kan keta hurumin kasar da yaki na kwanaki 12 da kuma da kuma kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar ta zaman lafiya wadanda suke Fordo Natanz ta kuma Esfahan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalti ministan yana fadar haka a taron kungiyar karo 17 wanda ke gudana a hilin yanzu a birnin Rio De jenero na kasar Brazil. A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne jiragen yaki na HKI suka kutsa cikin Iran inda suka kashe manya-manyan kwamandocin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliyar kasar ga shahada. Bayan haka...
    Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren  HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
    Miliyoyin yan Najeriya ne suka gudanar da tattakin Ashoora a birne daban daban a kasar a jiya Lahadi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, da farko ya nakalto daruwan da suka fito tattakin na Ashoora a Abuja babban birnin kasar a safiyar jiya Lahadi. A wannan karon dai masu tattakin Ashoora a Abuja sun fito ba tare da sanya bakaken kaya ba saboda kaucewa rikici da kuma kamu daga Jami’an tsaro a birnin, kamar yadda suka sabayi a shekarun da suka gabata. Labarin ya kara da cewa an gudanar da irin wannan tattakin na Ashoora a garurwa kimai 25 a duk fadin kasar, kuma an kammala ba tare da wata matsala ba. An gudanar da tattaki a jihar Bauchi...
    Kamfanin dillancin Labaran Assosciated Press ta bayyana cewa ana ci gaba da sukar Amurka da HKI kan cibiyoyin kisa da suka kafa a Gaza da sunan tallafawa Falasdinawa da abinci. Labarin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu Amurka da HKI sun kashe Falasdinawa kimani 635 wajen karban abinda suka kira taimakon abinci bayan sun sa su yunwa mai tsanani wanda zai sa su dole su fito su ne mi aminda zasu a sa a cikinsu. Amma idan sun so sojojin HKI su kashesu. Kamfanin dillancin labaran Associeated Press ya nakalto kamfanoni Amurka guda biyu wadanda sun ce sun shigar da kara Amurka da kuma HKI kan yadda suke gudanar da cibiyoyin rabon abinda suka kira abinci a gaza, wanda bai...
    Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe  kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
    Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙalubalanci jagoran ’yan bindiga Bello Turji, wanda ke neman sulhu, da cewa idan da gaske yake yi, to ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, ya daina kai hare-hare, kafin ta zauna da shi. Mashawarci na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman ne ya bayyana hakan baya yaɗuwar wani bidiyo da Turji ya saki, wanda a ciki yake neman a yi tsakaninsa da gwamnati. Ɗan ta’addan wanda ya addabi yankunan jihar da makwabta ya saki bidiyon ne kwanaki kaɗan bayan jami’an tsaro sun kashe wasu gaggan kwamandojinsa da Faransa sama da 100. Kamar Ahmed, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa babu yadda za a tabbatar cewa neman...
    Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya ta fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasashen Afirika da kafar dama, bayan lallasa ƙasar Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga yau Lahadi a filin wasa na Prince Moulay Abdellah. Asisat Oshoala da Rinsola Babajide da Chinwendy Ihezuo ne suka jefa kwallayen da suka yi sanadiyar samun nasarar ‘yan matan, yanzu Nijeriya ta dare teburin rukunin ‘B’ wanda ke ɗauke da ƙasashen Algeria da Botswana da Tunisia da Nijeriya. Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka? ‘Yan matan da Madugu ke jagoranta za su haɗu da ƙasar Botswana...
    Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, ya yi kira da a gaggauta samar da sabbin fasahohin kimiyya a fannonin aikin gona da kiwon lafiya, da karfafa cin gashin kan fasahar kirkire-kirkiren magunguna da na’urorin likitanci. Liu, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar bincike da ya kai lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin daga ranar Alhamis zuwa Asabar da ta gabata. Ya jaddada cewa, ya zama wajibi a mai da hankali kan bukatu na gaggawa da ake da su a bangaren masana’antar da kuma ba da karfi ga muhimman fannoni kamar masana’antar fasahar samar da iri, da injunan noma, da kayan abinci, da fasahar shuka da kiwo. Liu...
    “Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomin gwamnati.” “Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori kara mai kyau ta fashin zabe.” Ya bayyana. Ya ce irin wannan matsalar na samar da mutanen da ba su ko iya cin zabe a cikin dangin su ko al’ummar su amma sune ke tinkahon lashe zabe. A cewarsa a matsayinsa na dan majalisar dattawa suna kokarin gabatar da dokokin da za su shawo kan wadannan matsalolin, ya ce sun san hukumar zabe ba za...
    A cikin ‘yan kwanakin nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mayar da jawabi ga malamai da daliban tawagar musayar al’adu ta matasan Amurka masu buga wasan kwallon pickle daga gundumar Montgomery ta jihar Maryland, wadanda suka ziyarci kasar Sin a karkashin shirin gayyatar matasan Amurkawa 50,000 zuwa kasar Sin domin yin musaya da kuma nazarin karatu a cikin shekaru biyar.   Xi ya ce, makomar alakar Sin da Amurka ta dogara ce da matasa, yana mai bayyana fatan wakilan tawagar za su zama sabbin jakadu na sada zumunci a tsakanin kasashen biyu, da ba da gudummawa sosai wajen yaukaka zumuncin da ke tsakanin jama’ar kasashen biyu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Kungiyoyi farar da jam’iyyun adawar  siyasa a kasar Togo, sun sake yin kira da a gudanar da Zanga-zanga a ranar 16 da 17 ga watan nan na Yuli da ake ciki. Masu Zanga-zangar dai suna son nuna kin amincewa ne da siyasar hukumar kasar da suke bayyanawa da ta kama-karya, haka nan kuma kashe wasu mutane da aka yi a Zanga-zangar da ta gabata. Bugu da kari, kiran a yi zanga-zangar dai ya zo ne bayan kama wasu ‘yan hamayyar siyasa da aka yi da kuam kara kudin wutar lantarki, da amince da sabon tsarin mulki da ya kara bai wa shugaban kasar Faure Gnassingbe karfin iko. Wasu fitattun masu fafutuka a kasar, sun watsa sanarwa a shafukan sada zumunta...
    Raundunar sojan jamhuriyar Nijar sun sanar da cewa, an kashe  sojoji 10 da kuma jikkata wasu 15 a wasu hare-hare biyu da masu dauke da makamai su ka kai a yankin Telaberi da kudu masu yammacin kasar. Yankin Telaberi dai yana cikin yankunan da masu dauke da makamai su ka fara kai hare-hare saboda kusancinta da iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso. Bayanin na sojojin kasar ta Jamhuriyar Nijar wanda kafafen watsa labarun kasar su ka watsa ya kunshi cewa; Daruruwan masu dauke da bindiga sun kai hare-hare a kan sansanonin soja biyu da suke a yankin Telaberi da hakan ya yi sanadiyyar kashe sojoji 10 da kuma jikkatar wasu 15.” Sai dai kuma sanarwar ta ce, sojojin sun yi...
    Dubun dubatar mutanen kasar Lebanon sun yi gangamin raya ranar Ashura ta shahadar Imam Hussain ( a.s) a unguwar Dhahiya wacce aka sauya wa suna suna unguwar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Mahalarta taron sun daga hotunan Sayyid Hasrallah wanda a shekarar da ta wuce yana raye, ya kuma gabatar da jawabi a wurin jimamin Ashura. Haka nan kuma sun rika bayar da taken da yake cewa: ” Muna Akan Riko Da Alkawali Ya Nasrallah.” A yau 10 ga watan Muharram ne dai al’ummar musulmi Mabiya mazhabar Ahlul bayti suke tunawa da shahadar Imam Hussain ( a.s) da iyalansa da kuma sahabbansa madaukaka.
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’ima Kassim ya bayyana cewa; Dakarun Hizbullah mazajen fagen daga ne da ba su karbar kankanci. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a wurin babban taron Ashura a ungiyar Dhahiya dake birnin Beirut, ya bayyana cew; Yaki na tsaron kasa zai ci gaba saboda mun yi Imani da ‘yanto da kasa, kuma wajibi ne akansu, ko da kuwa an dauki lokaci mai tsawo sannan kuma sadaukar da kai ya yawaita.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Isra’ila abokiyar gaba tana ci gaba da mamaye yankuna 5 na Lebanon, don haka babu yadda za a yi mu mika kai.” Haka nan kuma ya yi tambayar cewa; Ta yaya za a tsammaci za mu ki...
    A kasar Iraki,miliyoyin mutane sun cika birnin Karbala domin yin juyayin shahadar  Ahlul Bayti ( a.s) da iyalansa tsarkaka, a tsakanin hubbaren Imam Hussain da dan’uwansa Abul Fadal Abbas ( a.s). Masoya Ahlul Bayti ( a s.) da su ka fito daga cikin kasar ta Iraki da kuma wasu kasashe, sun yi cincirindo a cikin birnin na Karbala a tsakanin hubbaren Imam Hussain da Abul Fadal Abbas ( a.s). Cibiyar da take kula da wuraren masu tsarki a Karbala ta yi tsari na kula a tafiyar da juyayin a cikin tsaro  da kuma gabatar da hidima ga masu Ziyara. An girke jami’an tsaro masu tsaro yawa a cikin birnin na Karbala da zagayen haramin Imam Hussain ( a.s) , haka...
    Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu aminci daga kasashe masu tasowa. Kuma har ila yau, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa ya riga ya samu gagarumin ci gaba, don haka makomar kasashe masu tasowa na bukatar ci gaba da kasancewar Sin a cikinsu. Bugu da kari, Cavince Adhere ya jaddada cewa, Sin ta bayyana bukatun kasashe masu tasowa na duniya yadda ya kamata, kana tana inganta ra’ayoyin da...
    Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa. A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC . Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya. A gun taron, sassan da abin ya shafa na kasashen uku sun cimma matsaya kan zurfafa hadin gwiwar tabbatar da doka da oda, kuma za su ci gaba da yin hadin gwiwa wajen dakile laifukan zamba ta hanyar sadarwar waya a Myawaddy da sauran wurare, da kawar da harkokin zamba ta hanyar sadarwar waya gaba daya, da kame dukkan ma’aikatan da ke da alaka da laifin zamba, kana za su yi tsayin...
    Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu. Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Tinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.” Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne. “Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar ce ta tabbatar aukuwar hatsarin. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM. FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda...
    Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM. FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya sa...
      Za ka so karin bayani kan sabbin ‘yan wasan da Arsenal ke shirin dauka? ⚽ Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma wata manufa ta ƙashin kansu. Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ya ce yana nan daram a jam’iyyar APC kuma yana biyayya ga jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. Sanarwar ta ce, “Mun ji wani labari da ake yaɗawa cewa zan koma jam’iyyar ADC tare da wasu gwamnoni biyar. “Wannan...
    Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar shiga filayen kiwo ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ƙara tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma. Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka “Duk wanda aka kama yana da hannu a wannan aika-aikar, za mu hukunta shi bisa doka,” in ji Gwamna. Ya kuma roƙi makiyaya da su guji shiga gonaki domin...
    Majalisar Dattawan Nijeriya ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan gabanin cikar wa’adin dakatar da ita da ta yi tsawon watanni shida. Majalisar ta ce ala tilas ne dakatacciyar Sanatar ta bayar da hakuri tare da neman afuwa a hukumance gabanin cika umarnin da ta wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar na dawo da ita. Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Shugaban Kwamitin Labarai da Harkokin Jamaa na Majalisar Dattawa, Sanata Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan hukuncin da kotun ta yanke a kan Sanata Natasha. Ya yi bayanin cewa, a yayin yanke hukuncin da ta bayar da...
    Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara  daga sassan duniya ke tururuwa zuwa hubbaren Imam Husaini da kuma titunan da ke kewaye. Mai ba da shawara ga babban sakataren cibiyar Hubbaren Imam Husain {a.s} Fadel Oz a cikin wata sanarwa da ya aikewa kafafen watsa labarai ya bayyana cewa: “A shirye-shiryen wannan juyayi, babban Sakatariyar Haramin Imam Husain (a.s) da haramin Abbas sun samar da dukkan sharuddan da suka dace don kula da masu ziyara da kuma tabbatar...
    An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 192,000 tare da jikkata yawancinsu mata da kananan yara. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ma’aikatar harkokin wajen kasar a Quito babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a zirin Gaza. Masu zanga-zangar sun yi kira da a kawo karshen yaki da kisan...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na Farko ya ce; Al’ummar Imam Husaini a Iran ba za su bari makiya su cimma mummunan burinsu ba Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na farko Muhammad Reza Aref ya rubuta a cikin wata wasika cewa: Domin kare martabar Iran da kasar al’ummar Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba barin mafarkin masu kyama ya tabbata ba. Aref ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram a jajibirin ranar Ashura inda ya rubuta cewa: “Saboda Iran da kasar da tushen al’ummar Mabiya Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba bari mafarkin makiya...