Aminiya:
2025-05-29@00:18:04 GMT

Tinubu na neman ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje

Published: 28th, May 2025 GMT

Shuganan Kasa Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman amincewarta domin ya ciyo bashin jimillar kudi Naira tiriliyan 39 daga kasasahen waje domin aiwatar da wasu ayyuka.

A wasiku ukun da ya aike wa majalisar, wadanda shugabanta, Abbas Tajudeen, ya karanta a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan majalisa domin ciyo bashin daga kasashen waje a shekarar 2025–2026.

Ya ce rancen na 2025–2026, ya kunshi Dala biliyan 21.5 (kimanin Naira tiriliyan 34) da Yuro biliyan 2.2 (kimanin Naira tiriliyan 3.96) da Yen na Japan biliyan 15 (kimanin Naira biliyan 164.7) da kuma Yuro miliyan 65 (kimanin Naira biliyan 116.79) a matsayin tallafi.

Yana kuma neman cin bashin cikin gida ta hanyar bayar da takardun lamuni na Dala biliyan biyu, kimanin Naira tiriliyan 34.285, don biyan basussukan fanshon adashi gata da suka taru.

An ga watan Babbar Sallah a Saudiyya Matashi ya shiga hannun ’yan sanda kan kisan matar aure a Kano

Tinubu ya nemi amincewa da bayar da takardun lamuni na Naira biliyan N757.98 a cikin gida domin biyan basussukan fansho da suka taru har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

Shugaban kasan ya bayyana cewa an tsara neman bashin ne don tallafa wa muhimman ayyukan a fannonin ababen more rayuwa, noma, lafiya, ilimi, da tsaro a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

Ya bayyana cewa bayar da takardun lamuni na Dala biliyan biyu ya yi daidai da Dokar Zartarwa ta Shugaban Kasa da nufin samar kuɗin domin farfado da darajar Naira da gudanar da muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa da samar da ayyukan yi.

Tinubu ya jaddada gaggawar buqatar wadannan kudade, yana mai nuni da tasirin cire tallafin mai da raguwar kudaden shiga na cikin gida.

Ya lura cewa hakan zai magance rashin bin tanade-tanaden Dokar Gyara Fansho a baya saboda matsalolin samun kuɗi, da nufin dawo da ƙwarin gwiwa a tsarin fansho da inganta jin daɗin tsofaffin ma’aikatan gwamnati.

Dukkan buƙatun guda uku an miƙa su ga Kwamitin Kula da Kuɗi na Majalisar don ɗaukar matakan majalisa na gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Amincewa rance takardun lamuni Naira tiriliyan kimanin Naira

এছাড়াও পড়ুন:

Rundunar Ƴansanda Ta Gayyaci Jami’anta Da Bidiyonu Ya Yaɗu Suna Karɓar Cin Hancin Naira 5000

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin dauri a gidan yari
  • Kamfanoni Mallakin Gwamnatin Sin Sun Samu Bunkasa Bisa Daidaito Cikin Watanni Hudu Na Farkon Bana
  • Gwamna Uba Sani Ya Kammala Titin Unguwar Su El-Rufai
  • Bashin da ake bin Najeriya zai koma tiriliyan 162
  • DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada”
  • Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Jakadun Kasashen Afirka
  • Sin Za Ta Kara Zurfafa Dunkule Rawar Yankunan Raya Tattalin Arziki Da Fasahohi A Fannin Janyo Jarin Waje
  • Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Amso Bashin $21.5bn Da ₦757.9bn
  • Rundunar Ƴansanda Ta Gayyaci Jami’anta Da Bidiyonu Ya Yaɗu Suna Karɓar Cin Hancin Naira 5000