2025-09-17@23:26:01 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1926
«Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya»:
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar. An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na...
Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban...
Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana. Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.” Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS...
Kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da wani rahoto mai zargin Isra’ila da laifin aikata kisan kiyashi a zirin Gaza. A cikin sabon rahoto da ta gabatar a ranar Talata, MDD ta zargi shugaban kasar Isra’ila Isaac Herzog, da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da kuma tsohon ministan tsaro Yoav Gallant...
Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin Wannan bayannin ya fito ne a yayin ganawar sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh inda suka tattauna kan dangantakar...
Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da sabon farmakin soji da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza. Kasashen Biritaniya, Faransa, Italiya, Masar, Jordan, Qatar, Spain, duk sun yi tir da farmakin kan Gaza suna masu cewa zai kara dagula halin kunci da ake ciki. Kungiyar tarayyar Turai, ta bakin Jami’ar kula da harkokin wajen ...
Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin,...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya...
Sojoji biyu sun ji rauni bayan wani harin kwanton baya da ’yan bindiga suka kai kan ayarin motocin Kwamandan kwamandan Rundunar Sojoji ta 382 Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ruwan Godiya, kan hanyar Sheme–Kankara, lokacin da tawagar Operation Fansan Yamma (OPFY) ke wucewa. Ganau sun ce sojojin na...
JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa wannan...
An fara taron hukumar IAEA ta kasa da kashe karo na 69TH a jiya Litinin, inda a taron ne ake fayyana al-amura masu muhimmanci da ya shafi makamashin Nukliya a duniya, kuma tuni shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Muhammad Eslami yakejagorantar tawagar Iran a taron. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya...
Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da...

Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
Shugaban kasar Iran yana mai jaddada cewa wajibi ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka tare da daukar matakai na zahiri a fagen tattalin arziki, al’adu da zamantakewa, yanke alakarsu da gwamnatin sahyoniyawan....
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo...
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki. A ranar 4 ga Satumba, 2025,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne...
Dan kasar Iran Aryan Salawati ya sami kyautar tagulla a wurin gasar kirkire-kirkire ta kasa da kasa wacce aka yi a kasar China. A yayin wannan bikin dai masu kirkira daga kasashe masu yawa ne su ka gabatar da abubuwan da su ka kirkira. Matashin dan kasar Iran ya kirkiri karamar na’ura wacce take iya...
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya ƙaryata zargin da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi masa, dangane da mutuwar wasu marasa lafiya sakamakon katse wutar lantarki da aka ce kamfanin ya yi. Asibitin na AKTH ya bayyana damuwarsa a ranar Lahadi kan abin da ya kira abin takaici yana mai...
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa. A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na...
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda...
Tun daga ranar 18 ga wata, za a kaddamar da fim mai taken 731 a sassan duniya da dama, fim din da ya bayyana yadda rundunar sojojin kasar Japan da suka kutsa kasar Sin suka gudanar da nazari a kan hada makamai da cututtuka tare da gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’ummar kasar Sin, a...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
Masu lura ko sa ido kan harkokin ilimi sun ce biyan kuɗaɗen cikin lokaci za su taimaka matuƙa wajen samun matsin da takurar da ƴan makaranta ko Iyayensu ke fuskant, bugu da ƙari kuma za su kasance a wuraren da suke karatu domin maida hankali kan abinda ya sa suke a makarantar ko kwalejin Hukumar...
Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran Muhammad Islami ya yi karin haske kan yadda Iran za ta halarci taron shekara -shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA. Mohammad Eslami ya bayyana dangane da...
Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da...
Wani mutum mai shekara 67 aka kai asibiti da raunuka masu barazana ga rayuwa, abin takaici kuma ya rasu a asibiti a ranar Juma’a, 5 ga Satumba. An bayyana sunansa da James Gbadamosi.” Bayan faruwar lamarin, ƴan sanda sun bayyana cewa sun kama Wright-Walter mai shekaru 37, suka gurfanar da shi bisa laifin kai hari...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa alakar iran da Tunusiya wani babban misali ne na irin yadda kasar iran ke son su fadada dangantaka da sauran kasashen musulmi bisa girmamawa da mutunta juna. Haka zalika Araqchi ya jinjinawa kasar Tunusiya game da irin matakin da ta dauka musamman a lokacin harin...
Rahotanni sun bayyana cewa babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince daftarin kudirin dake nuna goyon bayan kafa kasar falasdimu mai cin gashin kanta, inda ka samu kasashe 142 suka kara kuri’ara amincewa yayin da kasashe 10 kuma sun nuna rashin amincewa sai kuma guda 12 da suka kauracewa kada kuria. Wannan daftarin kudurin ya...
Shugaban rikon kwaryar Siriya ya bayyana cewa; Babu sabani na dindindin da Iran Shugaban rikon kwarya na Siriya Abu Mohammed al-Jolani ya yi magana kan alakar Siriya da sauran kasashe, inda ya mai da hankali kan Rasha, Iran da Masar. Ya kuma yi jawabi game da zaben Siriya da ayyana kundin tsarin mulkin kasar da...
Akalla Falasdinawa 64,756 sukayi shahada a kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar lafiya a yankin Falasdinawa da ke kewaye. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce an kawo gawarwakin mutane 38 da suka hada da biyu da aka zakulo daga baraguzan gine-gine a cikin sa’o’i...
A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan...
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta raba kayan tallafi ga al’ummar Jalingo-Kamo da ambaliyar ruwa ta shafa a Karamar Hukumar Kaltungo, inda iftila”in ya shafi gidaje kimanin 90. Rabon kayan ya biyo bayan umarnin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya amince da bayar da kayan abinci da na masarufi...
Wani dalili da ba zato ba tsammani ya janyo gazawar kashe manyan shugabannin Hamas a Doha Kafofin yada labarai sun bayyana wani dalili na bazata a ranar Laraba da ya biyo bayan gazawar da Isra’ila ta yi na kashe manyan shugabannin Hamas a Doha babban birnin Qatar. Kamfanin dillancin labaran RT ya nakalto tashar talabijin...

Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan
Bugu da kari, kafa wurin kare muhalli na kasa da kuma tsara ayyukan kamun kifi a tekun tsibirin Huangyan na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antar kamun kifi a yankin. Matakin da Sin ke dauka a wannan karo ya nuna iyakoki da manufofin da aka tsara a karkashin doka, ya kuma fayyace iyakokin...
’Yan bindiga sun kai wa wata mota hari a kan hanyar Tegina zuwa Kontagora a Jihar Neja, inda suka jikkata mutum biyu. Harin ya faru ne a Tudun-Fulani bayan direban motar ya ƙi tsayawa lokacin da ’yan bindigar suka buƙaci ya tsaya. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista...
Firaiministan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani Ya bayyana shugabannin Isra’ila a matsayin masu tsattsauran ra’ayi da ke kishirwar jefa duniya cikin rikici. Al-Thani, ya bayyana hakan ne a birnin New York, inda ya halarci taron gaggawa na kwamitin tsaro kan harin da Isra’ila ta kai Qatar. Qatar ta yi lale marhabun da matakin kwamitin sulhu...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho a daren jiya Alhamis da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, inda suka mai da hankali kan shirin nukiliyar Iran da batutuwan da suka shafin yankin. tattaunawar na zuwa ne bayan da Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye. A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima...

Rashin Wutar Lantarki: Masana Sun Nuna Damuwa Kan Asarar Dala Biliyan 29 Da Ƙananan Masana’antu Ke Yi
Masanan sun yi gargaɗi yayin da Shugaba Bola Tinubu ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na sake fasalin ɓangaren lafiya na Nijeriya, inda ya bayyana cewa babu wani ɗan ƙasa da ya kamata ya rasa rayuwarsa saboda rashin wutar lantarki a cibiyoyin lafiya. Yayin da yake jawabi a Taron Tattaunawar Masu Ruwa da Tsaki na...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da kasashen Turai uku suka dauka na yin biris da batun harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a baya-bayan nan, da kuma barazanar da suke yi na maido da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka soke,...
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Doha babban birnin kasar Qatar, ba tare da ambaton sunan Isra’ila ba. TY kuma jaddada wajabcin daina kai irin wadannan hare-hare da kuma nuna cikakken goyon baya ga ga ‘yancin kasar...
Shugaban kungiyar Ansar Allah, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan kasar Yemen a ranar Laraba ba ta nuna wata nasara ba, sai dai yana nuna rashin bin dokokin kasa da kasa wajen ci gaba da aikata laifukan yaki. A cikin jawabinsa na mako-mako a wannan Alhamis, yayin da...
Ministan harkokin wajen Tunisiya Mohamed Ali Nafti ya ce kasarsa da Iran sun amince da karfafa hadin gwiwa tare da shirya taron komitin hadin gwiwa, yayin da yake maraba da sabuwar yarjejeniyar da Tehran ta kulla da hukumar IAEA. A cikin rubuce-rubuce uku na X a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Tunisia ya bayyana cewa,...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia....