Ministan Harkokin Wajen Iran Yace Faransa Bata Da Yencin ZarginWata Kasa Dange Da Kare Hakkin Bil’adama
Published: 26th, May 2025 GMT
Mainistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Faransa bata da hakkin sukar wata kasa a duniya dangane da abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Bayan matsayinta a kissan kiyashin da HKI take aikatawa a gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan yana maida martani ne ga tokwaransa na kasar Faransa Jean-Noel Barrot ya fada bayan da wani ba’irane ya sami lambar yabo mafi girma a gasar fina-fina mafi girma a duniya da ake kira ‘ Cannes Film Festival’ .
Aragchi ya bayyana cewa, Faransa ta tabbatar da cewa kare hakkin bil’adama idan ya shafi kawarsu HKI ce , kissan Falasdinawa 56,000 kare kaine amma ba’ira ne ya ci lamba mafi girma bai dace ba don kasarta tana take hakkin bil’dama. Wannan shi ne fuska biyu a mizanin kare hakkin bil’adama a wajen kasar farsanda da kasashen yamma da dam.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kare hakkin bil adama
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Yace Huldar kasar Iran Da IAEA Zai Ci Gaba Ne Idan Ta Daina Fuska Biyu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu kai tsaye ko kuma ta yi amfani da wakilanta a cikin Iran don yin wannan aikin.
Banda haka Hukumar ta rufe idanunta kan shirin makaman Nukliya na HKI gaba daya. Daga karshe yace Iran zata sauya yadda take hulda da hukumar a lokaci guda tana bin hanyar diblomasiyya don warware matsalolin da suke rage tsakaninta na hukumar.