Daesh ta yi ikirarin kai hari kan gwamnatin Syria
Published: 31st, May 2025 GMT
Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na farko a kan tsoffin kawayenta tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya.
A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce ta sanya “bama-bamai” kan motar dakarun da HTC ke jagoranta a lardin Suwayda da ke kudancin kasar.
Wannan dai shi ne harin farko da Daesh ta yi ikirarin doka kan sabuwar gwamnatin ta Siriya.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) ta bayar da rahoton cewa, a yayin harin, wasu mambobi uku na runduna ta 70 na rundunar HTC sun jikkata, a yayin da suke sintiri yayin da wata nakiya da aka tayar daga nesa ta tashi a ranar Laraba.
An kuma kashe wani mutum da ke tare da wadannan sojoji a yankin hamadar da ke kewaye.
Shi dai shugaban Syria na yanzu Abu Mohammed al-Jolani tsohon jigo ne a kungiyar Al-Qaeda da Daesh.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Jikkata Sojojin Sahayoniya 9 Ta Hanyar Take Su Da Mota
Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam.
Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba.
Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin ‘yan sahayoniyar da su ka jikkata sojoji ne.
Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; Wanda ya take sojojin ya iya gudu daga wurin, ba tare da an tsayar da shi ba.
Ita kuwa jaridar ‘ Yasrael Home” ta bayyana cewa; An baza ‘yan sanda a wurin da aka kai hari, domin gano inda maharin yake.
Kungiyoyin Falasdinawa sun yi maraba da wannan harin, tare da yin kira a ci gaba da gudanar da irinsa da yawa.
Kungiyar Hamas ta ce, dole a tsammaci wannan irin harin, bisa la’akari da laifukan da HKI take tafkawa a Gaza da yammacin kogin Jordan.
Kungiyar Jihadul-Islami kuwa cewa ta yi, hari irin wannan yana kara tabbatar da yadda al’ummar Falasdinu ta sha alwashin ci gaba da riko da kasarta da kuma kalubalantar ‘yan mamaya da dukkanin abinda su ka mallaka.
Shi kuwa kwamitin gwagwarmaya na Falasdinu ta yi kira ne ga dukkanin Falasdinawa da su yunkura domin fada da sojojin sahayoniya.
Ita kuwa kungiyar “Mujahidun-al-Falasdiniyya ta sa wa harin albarka tare da bayyana shi a matsayin babban sako ga ‘yan mamaya dake cewa martani akan kisan gillar da suke yi zai fadada.