HausaTv:
2025-07-12@02:09:08 GMT

Iran ta yi kira da a karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka

Published: 26th, May 2025 GMT

Iran ta yi kira da a karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka bisa tsarin yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar

A yayin bikin karo na 62 na kafuwar kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a birnin Tehran, ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar Iran na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afirka, musamman ta hanyar yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA).

A cikin jawabin da ya yi ga jakadun kasashen Afirka a Iran, Araghchi ya yaba da dabi’u da tarihin gwagwarmayar al’ummar Afirka, yana mai cewa Afirka, mai al’umma biliyan 1.4, na zaman kawa a huldar tattalin arziki ga Iran.

Ya kara da cewa: “Iran da kasashen Afirka za su iya hada kai da juna saboda irin karfin da suke da shi: dimbin albarkatun kasa a bangaren Afirka da fasahohin zamani a bangaren Iran.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma tunatar da zurfafa alaka ta tarihi da ke tsakanin Iran da nahiyar Afirka, inda ya yi kira da a fadada hadin gwiwa a fannoni daban-daban: masana’antu, noma, kiwon lafiya, ilimi, makamashi, yawon bude ido, da ababen more rayuwa.

Ya yi maraba da nasarar taron koli na hadin gwiwar tattalin arziki na Iran da Afirka karo na uku da aka gudanar kwanan nan a birnin Tehran, yana mai kallon hakan a matsayin wata alama mai kyau ga makomar dangantakar bangarorin biyu.

A karshe Araghchi ya tabbatar da cewa Iran za ta tsaya kafada da kafada da nahiyar Afirka a kokarinta na samun ci gaba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a hadin gwiwar tattalin arziki

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya

Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 24 a wasu sabbin hare-hare da suka ƙaddamar a maɓoyar ’yan ta’addan a yankunan daban-daban a Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Kwamandan haɗakar rundunar Operation Haɗin Kai a Arewa Maso Gabas, Janar Abdulsalam Abubakar ya ce an kai samamen ne bayan tattara bayanan sirri.

A cewarsa, an kuma kashe mutum biyar da suke samar wa ’yan ta’addan kayayyakin amfani, a wani kwanton ɓauna da aka yi musu da daddare.

An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu

An gudanar da waɗannan ayyuka ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli a Dajin Sambisa, da Dandalin Timbuktu da kuma Tsaunukan Mandara da ma wasu wuraren daban.

A yayin samamen, rundunar ta ce an yi nasarar ƙwato muggan makamai da dama da babura da kekuna da kayan abinci da kuma kaki da takalman sojoji.

Manjo Janar Abdulsalam ya ce rundunar hadin gwiwa ta bangaren sojin sama, da Civilian Joint Task Force, da na sojojin Nijeriya ne suka gudanar da aikin.

Shi ma Kakakin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ Kyaftin Reuben Kovangiya, ya bayar da cikakken bayanin ayyukan a cikin wata sanarwa.

A ci gaba da gudanar da jerin hare-hare na hadin gwiwa a fadin Arewa maso Gabas, sojojin Operation HADIN KAI (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunonin sojin sama da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force da mafarauta, sun yi nasarar gudanar da samame a kan ’yan ta’addar Boko Haram/ISWAP daga tsakanin 4 zuwa 9 ga Yulin 2025 inda suka kawar da ’yan ta’adda da dama.

A daya daga cikin samamen da aka kai a Platari a ranar 4 ga watan Yulin 2025, yayin da sojojin suka yi kwanton ɓauna, sun far wa ’yan ta’addar JAS/ISWAP da ke kan babura da ke tafiya daga dajin Sambisa zuwa Dandalin Timbuktu.

Nan take aka fatattaki ‘yan ta’addan ta hanyar buɗe musu wuta, lamarin da ya kai ga halaka ‘yan ta’adda 3.

Kazalika, bayan samun bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan tada kayar bayan a kewayen yankin Komala, sojoji sun sake yi wa ’yan ta’adda kwanton ɓauna, inda suka kashe wani mayakin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 
  • Najeriya Ba Za Ta Karbi ‘Yan Ci Ranin Kasar Venezuela Da Amurka Za Ta Kora Ba
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki
  • Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Hadin Gwiwar Hukumar Kwastam Don Farfado Da Yankin Kasuwanci Na Maigatari
  • Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista
  • Aragchi Ya Tattauna Da Bin Salman Kan Karfafa Zumunci Tsakanin Kasashen Biyu
  • An Yi Hasashen Karuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 35 Tsakanin 2021 Zuwa 2025
  • Ma’anar Sabon Tsarin Hadin Kan Mambobin Brics a Sabon Zamani Ga Dunkulewar Kasashe Masu Tasowa