Hare-Haren HKI Kan Wata Makaranta A Gaza Ya Kashe Mutane 46 Daga Ciki Harda Yara Kanana
Published: 26th, May 2025 GMT
Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana.
Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara suna gudu a cikin wuta suna kokaron kubutar da kansu.
Labarin ya kara da cewa a cikin wadanda yahudawan suka kashe a Gaza, akwai Mohammad Al-kasih shugaban bangaren yansandan bincike na arewacin Gaza da Matarsa da yayansa.
Wata majiyar Palasdinawa ta bayyana cewa kafin hari a kan makarantar yahudawan sun kai hare kan wani gida a unguwar Thawra da birnin Gaza.
Manufar yahudawan dai shi ne mamayar dukkan gaza da kuma korar Falasdinawa daga yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Kwamandan Sojin Iran Ya Bayyana Cewa Iran Ta Koyawa Gwamnatin Isra’ila Hankali
Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran
Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya.
A wata ganawa da iyalan shahidi Kanar Bostan Afrouz, Manjo Janar Hatami ya kara da cewa: Makiya sun kasa cimma tsare-tsare da shirye-shiryensu da suka rigaya sukaaniyar cimmawa, kuma sun fuskanci mummunar martani da shan kashi.
Ya ci gaba da cewa: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya duk da karfin soja da kudi da suke da su, baya ga bayanan sirri da suke tabbatar da samun goyon bayan gwamnatin kama karyar Amurka, wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran.