Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin.

Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda ke bukatar dukkanin hukumomin gwamnati 774 su bayar da akalla shekaru biyu na rahotannin kudinsu kafin su iya karbar kasafin kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

Babban bankin ya bayyana cewa dole ne gwamnatocin kananan hukumomi su cika bukatun kafin su bude asusu don kura musu kudadensu kai tsaye.

Ka’idojin da aka gindaya wa kananan hukumomin ya kara janyo tsaiko wajen jinkirta aiwatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi.

Ko da yake, yunkurin farko na jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, tsawon watanni uku da gwamnatin tarayya ta bai gwamnonin na gudanar da shirye-shirye a watan Agusta na 2024.

Gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi sun yarda da dakatar da aiwatar da hukuncin har da an tantance hanyoyin biyan albashi, tabbatar da ingancin aiki, da gudanar da zaben hukumomin kananan hukumomi da sauran batutuwa.

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON), ta hannun sakatarenta, Muhammed Abubakar, ta yi korafin cewa rashin aiwatar da hukuncin ta ta’allaka ne bisa umarnin da ministan shari’a na tilasta wa CBN wajen bude asusu dukkan kananan hukumomi.

ALGON ta ce rashin bayar da umurnin ya kawo cikas ga fara zantar da hukuncin kotun.

A cikin wannan lamari, ana zargin wasu gwamnoni da yin amfani da ikonsu wajen musgunawa da kuma matsin lamba ga shugabannin kananan hukumomi don kar su bude asusun da za tura musu kasun kai tsaye.

Ana ce wasu gwamnan suna matukar adawa da bude asusun a CBN, kasancewar hakan zai hana su samun damar yin amfani da kudaden kananan hukumomi da suka dade suna juyawa.

Saboda haka, ana zargin sun bai wa shugabannin kananan hukumomi umurnin kar su yarda su bude asusun a Babban Banki Nijeriya.

Idan za a iya tunawa dai, ministan shari’a ya shigar da karar a kotun koli a madadin gwamnatin tarayya da kananan hukumomi 774, yana rokon kotun ta ba da cikakken ‘yanci da bayar da kudade kai tsaye ga kananan hukumomi daga asusun tarayya.

Kotun ta duba karar sannan ta amince da wannan bukata tare da bayar da umarnin cewa a dunga bai wa kananan hukumomin kasunsu kai tsaye ba tare da gwamnonin jihohi sun rike kudaden ba wanda ya saba wa tsarin dimokuradiyya.

Shari’ar mai al’kalai bakwai, wanda ke karkashin jgorancin, Mai Shari’a Emmanuel Agim, ya bayyana cewa Nijeriya na da bangarori guda uku na gwamnati, wadanda suka hada da gwamnatin tarayya, gwamnatin jiha, da gwamnatin karamar hukumu, kuma babu wata gwamnatin jiha da ke da ikon nada kwamitin riko na kananan hukumomi saboda gwamnatin karamar hukuma ana zaben ta ne karkashin tsarin dimokuradiyya.

Kotun ta ce amfani da kwamitin riko ya saba wa kundin tsarin mulki na shekarar 1999, kuma ta kara da cewa gwamnatocin jihohi suna ci gaba da jawo mummunan rudani ta hanyar kin yarda a gudanar da zaben kananan hukumomi ta hanyar dimokuradiyya a jihohisu said ai su nada kwamitin riko ko kuma su dora wadanda suka so.

Kotun koli ta umarci a gaggauta fara aiwatar da hukuncin nan take.

Bayan wata guda da yanke hukuncin, gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin don aiwatar da hukuncin, wanda ke karkashin shugabancin sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume. Kwamitin ya kashe tsawon yana tattaunawa kuma har ya mika rahotonsa.

Duk da haka, abun mamakin shi ne, bayan wata daya da zartar da hukuncin kotun kolin wacce ta bayar da umurnin a gaggauta aiwatar da shi, amma har yanzu an kasa aiwatar da hukuncin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: aiwatar da hukuncin gwamnatin tarayya da gwamnatin a aiwatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”