MDD Ta Gudanar Da Bikin Ranar Tunawa Da Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Duniya Ta 2025
Published: 29th, May 2025 GMT
Shima a nasa jawabin Janar Martin Luther Agwai cewa ya yi, “Aikin wanzar da zaman lafiya na daya daga cikin muhimman aikin Majalisar Dinkin Duniya da ake iya gani, inda sama da sojoji 87,000 ke sanye da rigar wanzar da zaman lafiya da farar hula suka taka rawa a cikin wasu ayyuka 12, daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa Lebanon, daga Sudan zuwa Mali.
Wadannan jajirtattun maza da mata suna taimakawa wajen daidaita yankuna, ba wa fararen hula kariya, tallafawa tsagaita wuta, da sake gina da amana inda ta lalace.
Mahimmanci lamari shi ne, tun lokacin da aka kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta farko a shekara ta 1948, dakarun wanzar da zaman lafiya sun ceto mutum sama da miliyan biyu daga kasashe sama da 125 cikin ayyuka 71 da suka gudanar.
Tun da fari a jawabinsa na maraba, Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Kuma Mai Kula Da Ayyukan Jin Kai a Nijeriya Mohammed Malick Fall, maraba da zuwan bikin cika shekaru 77 na ayyukan samar da zaman lafiya na MDD ya yi, inda ya ce “Taro ne mai muhimmanci kuma ya zo daidai da cika shekaru 80 da kafuwar Majalisar Dinkin Duniya,” in ji shi.
“A tsawon tarihinta, Majalisar Dinkin Duniya babban aikinta ga al’ummar duniya shi ne inganta zaman lafiya, tsaro, ci gaba, da mutunta bil’adama, kuma ta yi fice a wajen cimma wadannan manufofi.”
“Tun daga 1948, Majalisar Dinkin Duniya ta sa ido kan ayyukan wanzar da zaman lafiya fiye da 70, da ceton rayuka da dama da kuma yin aiki a matsayin mai magance manyan tashe-tashen hankula.
A halin yanzu, sama da dakaru 87,000 masu sanye da kaki ana tura su cikin ayyuka mabanbanta kamar 12 a duniya.
Wanzar da zaman lafiya ya kasance daya daga cikin abubuwan da Majalisar Dinkin Duniya ta fi gani da inganci.”
“Karni na 21 ya zo da qalubalen tsaro da ba a tava ganin irinsa ba kuma masu alaqa da juna. Wadannan suna bukatar sabbin hanyoyi, kakkarfan hadin gwiwa na yanki da na duniya, da kuma sake nazarin yadda muke gudanar da ayyukan zaman lafiya-musamman yayin da rarrabuwar kawuna na siyasa ke kara hana shawo kan lamarin.
Wannan shi ne dalilin da ya sa muka sanya wa taron ranar dakarun wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a yau, taken “Makomar wanzar da zaman lafiya,” kuma ya dace sosai, in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya wanzar da zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe
Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe.
Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar.
Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan AmurkaA cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa.
DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da su taimaka da bayanai da za su taimaka wajen sake kama shi.
Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su kusanci fursunan da ya tsere, domin hakan na iya zama hatsari.
“Domin kare lafiyarku, idan kuka ga wani da kuke zargi shi ne, ku sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa ko gidan gyaran hali, ko kuma ku kira lambar 08038452982,” in ji sanarwar.