Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ’yanci tsakanin Sin da da GCC.

Idan mun waiwayi wannan sanarwa ta hadin gwiwa, za ku gano manufofin da sassan uku ke fatan cimmawa, wadanda suka hada da fatan dunkule shiyyoyinsu waje guda, da kara yin tafiya tare, da neman samun ci gaba mai dorewa. Karkashin wadannan burika, sassan uku za su yi amfani da fifikonsu wajen cimma moriyar juna da karfafa kawance a tsakaninsu.

Masharhanta na ganin baya ga hadin gwiwar bunkasa tattalin arziki, da dunkule sassa daban daban, da inganta tattaunawa, da wanzar da ci gaba, wadannan sassa uku za su more damar sabbin fannonin raya kansu, kamar fannin sauya akala zuwa ga amfani da makamashi mai tsafta, da cin gajiya daga fasahohin dijital, da fannin bunkasa noma, tare da yaukaka hadin gwiwa a sauran muhimman fannoni.

Ko shakka babu, idan har Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC sun rike ruhin wannan taro na koli, hakan zai taimaka wajen dinke al’ummunsu waje guda, da yaukaka fahimtar juna, matakin da zai haifar musu da ci gaba ta fuskoki masu tarin yawa, daidai da burin kasar Sin na gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hadin gwiwar

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.

Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.

Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Ya ce an tsara wannan asusu  ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.

Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.

Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin  ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.

Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a  wuraren.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba
  • Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin