Limamin Sallar Juma’ar Tehran Ya Jaddada Cewa: Babu Wanda Zai Dakatar Da Iran Tace Sinadarin Uranium
Published: 31st, May 2025 GMT
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba
Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Iran ba ta neman mallakar makamin nukiliya, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana ba.
Limamin Juma’ar Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Hakika dogaro da yarda da kai, a halin yanzu ta kai Iran ga duk harkokin bunkasa ci gaban kasarta, yana mai jaddada cewa: Za a ci gaba da sarrafa sinadarin Uranium a kasar Iran duk kuwa da matsayar adawa da kasashen yamma suke nunawa kan haka.
A cikin hudubar sallar Juma’ar a jiya Juma’a Ayatullah Khatami ya kara da cewa: “Al’umma sun ga yadda suke son mayar da Iran baya a fagen makamashin nukiliya, suna cewa bai kamata Iran ta kasance ta mallaki na’urar taken Uranium koda guda daya ba, amma godiya ga Allah da kokarin masana kimiyya na kasar Iran, kasar ta samu gagarumin ci gaba a wannan fanni na kimiyya.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka.
“Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem.
Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen duniya da gaza aiwatar da dokokin kasa da kasa, yana mai cewa, “Shiru da kasashen duniya suka yi, abin Allah wadai ne ga gwamnatocin kasashen duniya, musamman na kasashen musulmi da larabawa.
Da yake ishara da kiraye-kirayen baya-bayan nan da kasashe sama da ashirin suka yi na a dakatar da yakin, Sheikh Qassem ya yi ishara da cewa irin wadannan kalamai da cewa ba su isa ba ko kadan, Ya ce, “bai isa ba a ce kasashe 25 sun yi kira da a dakatar da yakin Gaza, wannan furucin kadai bai wadatar ba.
Sheikh Qassem ya yi kira da a kakaba takunkumi kan “Isra’ila”, da gurfanar da su a gaban shari’a, da kuma dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.