Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, tun daga rubu’i na hudu na shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da matakai a jere na kula da harkokin tattalin arziki, da kyautata yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma hasashen kwarin gwiwa da ake yi kan kasuwanni cikin kwanciyar hankali.

Matakin da kamfanin nazari na Moody’s ya dauka na tabbatar da daidaiton mizanin matsayin kasar Sin, wani lamari ne mai kyau, na kyakkyawan fatan bunkasar tattalin arzikin kasar.

 

Ma’aikatar kudin ta kasar Sin ta bayyana cewa, a mataki na gaba, wasu tsare-tsare za su gudana tare, kuma za su ci gaba da yin tasiri, da samar da cikakken goyon baya ga bunkasar tattalin arziki mai inganci. Duk yadda yanayin waje ya sauya, kasar Sin za ta kasance cike da kwarin gwiwa, kuma za ta mai da hankali kan yin abun da ya dace.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.

Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.

Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin  noma daban daban.

A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.

Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.

Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.

Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.

Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.

Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.

Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam  yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.

Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.

A garin Chuwasu  dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.

Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.

Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.

Yace da farko suna da shakku akan amfani  da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.

Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.

Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar  Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.

A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.

A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.

Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.

Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma