AU Ta Jinjinawa Goyon Bayan Sin Ga Ci Gaban Nahiyar Afrika
Published: 29th, May 2025 GMT
Shugaban kwamitin kungiyar Tarayyar Afrika (AU) Mahmoud Ali Youssouf, ya nanata godiyar kungiyar bisa irin goyon bayan da kasar Sin ke ba ta da ma kasashen Afrika a muhimman bangarori kamar na cinikayya da raya ababen more rayuwa da aikin gona da kiwon lafiya da bunkasa kwarewar jami’ai.
Wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba, ta ruwaito Mahmoud Ali Youssouf na bayyana haka ne yayin da yake bankwana da Hu Changchun, shugaban tawagar kasar Sin a AU.
Shugaban na kwamitin AU ya kuma yaba wa jajircewar Hu tare da gode wa kasar Sin dangane da gudunmuwar da ta bayar na gina Cibiyar Kandagarki da Dakile Yaduwar Cututtuka ta Afrika, da taimakonta ga aikin wanzar da zaman lafiya da sauran taimakon da take bayarwa a sauran muhimmman bangarori da suka shafi jama’a a fadin nahiyar Afrika.
Jami’an biyu sun kuma waiwayi nasarorin da aka samu karkashin taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika da ya gudana a Beijing a shekarar 2024 tare da bayyana hadin gwiwar AU da Sin a matsayin misalin cudanyar bangarori daban daban. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp