Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin Zirin Gaza

Falasdinawa fararen hula 23 ne suka shahada tare da jikkata wani adadi masu yawa a wani sabon kisan kiyashi da sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila suka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin zirin Gaza.

Rahotonni sun bayyana cewa: sojojin mamayar sun kai hare-hare ne ta hanyar jiragen saman kan gidajen jama’a, ciki har da gidan iyalan Al-Qarnawi da ke gabashin sansanin.

Haka hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar wani Bafalasdine a yankin Qizan al-Najjar da ke kudancin Khan Yunus. Sannan jami’an ceto sun gano gawar wani Bafalasdine a wani gidan da aka jefa bam a Abasan al-Kabira da ke gabashin birnin.

Bugu da kari, gobarar da jiragen saman sojojin mamayar Isra’ila suka tayar a kan yankunan Falasdinawa ta janyo shahadan wani Bafalasdine a kusa da wata cibiyar agaji a yankin da ake kira “Morag axis,” kudu maso yammacin Khan Yunis.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!

“Mun kasance muna jiran a ba mu garin alkama, saboda muna jin yunwa sosai, muna neman abin sha da abinci, kwatsam tankokin sojan Isra’ila suka zo suka kewaye mu, suka fara harba bindiga a kanmu, ba mu iya motsawa ba. Ba mu samu gari ba, an kuma kewaye mu na tsawon sa’a daya da rabi zuwa biyu, wasu sun gudu, wasu an kashe su, wasu kuma sun ji raunuka.” In ji wani dan Gaza game da abin da ya faru gare shi a ranar 21 ga wata.

Tsawon kwanaki 140 ke nan da Isra’ila ta rufe hanyoyin shiga Gaza. A halin yanzu, kashi 93% na iyalai a Gaza ba su da ruwan sha, kuma fiye da kashi 87% na yankunan Gaza sun zama yankunan soja ko kuma sassan da mazauna wurin suka bar muhallansu, kusan mutane miliyan 2.1 aka tilasta musu shiga wani karamin yanki, ba su da abubuwan da ake bukata na yau da kullum. Isra’ila ta hana shigar da kayayyakin agaji, da garin madarar jarirai da man fetur, wanda ya sa abinci da magunguna suka kusan kare a Gaza. Fararen hula na Gaza da dama da suka je wuraren rarraba kayayyakin agaji na Isra’ila da ake kira “Gaza Humanitarian Foundation” (GHF) sojojin Isra’ila ne suka harbe su. Firaministan Falasdinu Muhammad Mustafa ya ce adadin wadanda aka kashe ya wuce 995. A Gaza, Isra’ila tana amfani da yunwa a matsayin makami, har ma wuraren rarraba abinci sun zama “tarkon mutuwa”, mutanen Gaza ba su samu gari ba, a maimakon haka ana kashe su da harbin bindiga.

A ranar 21, kakakin harkokin wajen kasar Sin ya jaddada cewa bai kamata a rika kai wa fararen hula hari ba, kuma bai kamata masu ba da agaji na kasa da kasa su fuskanci barazanar tsaro ba. Bugu da kari, kwanan nan kasashe 25 sun fitar da sanarwar hadin gwiwa suna bukatar a kawo karshen yakin yankin Gaza nan take, tare da bukatar Isra’ila ta bi dokokin kasa da kasa na jin kai, da kuma soke takunkumin da aka sanya na shigar da kayayyakin agaji.

Da fatan gwamnatin Isra’ila za ta saurari kiran kasa da kasa na kada ta yi amfani da “yunwa a matsayin makami”. Da kuma gaggauta dakatar da yakin nan take a yankin Gaza, don ba da damar shigar da kayayyakin agaji cikin sauki, tare da tabbatar da hakkin fararen hula.(Mai zane da rubutu: MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman
  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
  • Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Na Isra’ila Da Makami Mai Linzami Nau’in Flasdinu
  • Yahudawan Sahayoniyya Sun Bullo Da Dabarar Kisa Kan Falasdinawa Musamman ‘Yan Gudun Hijira
  • WHO Ta Buƙaci Isra’ila Ta Saki Ma’aikacinta Da Aka Kama A Gaza
  • MDD Ta Gargaɗi Isra’ila Kan Tilasta Wa Al’ummar Deir al-Balah Na Gaza Tashi
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne
  • Jaridar Washington Post Ta Ce; Yeman Ta Gurguta Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Isra’ila
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi