Shugaban Shirin HKI Da Amurkan Na Raba Kayan Agaji A Gaza Ya Yi Murabus
Published: 26th, May 2025 GMT
Jaridar ” Up Isra’el” ta buga labarin cewa; shugaban cibiyar Ayyukan Agaji A Gaza” wacce ke karkashin Amurka da Isra’ila” ya yi murabus saboda abinda ya kira rashin gaskiya da ‘yanci a cikin Shirin.
Jaridar ta ambato Jake Wood yana cewa; Ba abu ne mai yiyuwa ba a aiwatar da Shirin agaji a Gaza, sannan kuma a ce za a yi aiki da ka’idojin ‘yan’adamtaka, tsaftar aiki, da cin gashin kai, da abubuwa ne wadanda ba zan taba ja da baya a kansu ba.
Wood ya yi kira da a yi ayyukan gabatar da kayan agajin a cikin yankuna masu yawa na Gaza,a kuma a yi aiki da dukkanin hanyoyin gabatar da taimako.”
Wood ya bayyana cewa; Tun watanni biyu da su ka gabata ne aka tuntube shi domin ya jagoranci wannan cibiyar,saboda kwarewar da yake da ita a fagen ayyukan agaji, sannan ya kara da cewa: ” Daidai da sauran mutane masu yawa a duniya, na firgita, na kuma yi bakin ciki saboda yadda na ga ake fama da yunwa a Gaza,sannan kuma a matsayina na jagora a fagen ayyukan agaji na ji cewa nauyi ne da ya rataya a wuyana in yi abinda zan iya saboda rage wahalhalun da mutane suke cki.”
Jaridar ta “Up-Isra’el” ta kuma ce; Ajiye aiki da Wood ya yi, babban ci baya ne ga Isra’ila, kuma ya zuwa yanzu babu tabbacin ko wannan cibiyar za ta yi aikinta.”
Da akwai alamar tambaya akan ayyukan cibiyar wacce ba a adade da kafa ta ba, sannan kuma babu cikakkiyar masaniya akan inda ta samo kudin da su ka kai dala miliyan 100.
MDD dai ta ce ba za ta shiga cikin ayyukan agaji a Gaza ba, matukar ba za a bi dokokin kasa da ka sa ba.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ayyukan agaji
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Jami’in Sojan HKI A Gaza
Rundunar sojan mamaya ta sanar da kashe daya daga cikin jami’an sojojinta dake karkashin rundunar “Golani” a yankin Khan-Yunus dake Gaza.
Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin mamayar HKI su ka snar da cewa wani daga cikin mayakansu mai mukamin Captain ya halaka a Gaza, kuma tuni sun bude bincike akan abinda ya faru.
Rahoton tashar talabijin din ” Cane” ta HKI ya ambaci cewa, sojan da aka kashe yana cikin wadanda su ka kai hari a garin Khan-Yunus a jiya Alhamis.
Sojojin mamaya sun kai hari ne a cikin wani gida a ci gaba da kashe ‘yan gwgawarmaya da suke yi, sai dai ginin gidan ya rufta da su, bayan da nakiyar da take cikinsa ta fashe.
Tun a jiya Alhamis ne dai kafafen watsa labarun na HKI su ka fara Magana akan cewa sojojin da suke Gaza, suna fuskantar yanaki mai tsanani, da hakan yake nufin cewa an halaka wani adadi nasu.
An ga jirgin sama mai saukar angulu yana shawagi a yankin da aka yi kazamin fada a tsakanin ‘yan gwgawarmaya da kuma sojojin mamaya.
A cikin kwanakin bayan nan dai ‘yan gwgawarmaya suna kara samun nasarar halaka sojojin HKI da suke yi wa al’ummar yankin kisan kiyashi da kuma jikkata wani adadi mai yawa nasu.