Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (2)
Published: 30th, May 2025 GMT
Na zauna da Manzon Allah (SAW), na zauna da Sayyidina Aliyu, na zauna da Sayyidina Hassan da Hussaini, na zauna da Sayyidina Aliyu Zainul-Abidina (Babanka), don haka tambayi duk abin da kake so.” Shi (Jabir) makaho ne a lokacin, ina cikin tambayarsa kenan (in ji Ja’afarus Sadik) sai lokacin sallah ya yi, sai ya tashi a cikin wani dan mayafi da ya daura kuma ya yafa.
Sai matar Sayyidina Abubakar Asma’u bintu Umaisin ta haifi dan da ya sa ma sa sunan Annabi (Muhammadu bin Abubakar). Ta aika (jaririn) zuwa wurin Annabi (SAW) kuma ta tambaye shi cewa ga shi ta haihu, yanzu ya za ta yi (da batun Hajjinta)? Annabi (SAW) ya aiko mata da amsar cewa, “Ke ma ki yi wankan harama da Hajji, daga nan ki yi kunzugu (Nafkin, wannan yana nuna macen da ba ta tsarki idan za ta yi Aikin Hajji dole sai ta yi wankan harama duk da cewa ba za ta yi sallah ko ta shiga Ka’aba ba). Sai Manzon Allah (SAW) ya yi sallah a Masallacin Zul-hulaifa, daga nan ya hau rakumarsa (Kaswa) har ta daidaita da shi a sarari. Sai na duba sarari; ga mahaya nan da masu tafiyar kasa a ko ina dama da hagunsa (SAW) iya ganina. Annabi (SAW) kuma yana tsakiyar yara (matasa), sai ya yi niyya ya daga muryarsa yana cewa “Labbaikal lahumma labbaik… zuwa karshe”, (ma’ana amsawarka ya Allah, ka ce in je Hajji kuma na amsa). Mutane su ma suka amsa. Mu dai (in ji Sayyidina Jabir), Hajji kadai (ban da Umura) muka yi niyya a lokacin, a haka muka rinka tafiya tare da Annabi (SAW) har muka zo Makka muka shiga Masallaci.
Farkon abin da Annabi ya fara yi bayan mun shigo Masallacin shi ne sumbantar Dutsen Hajarul As’wad. Sai ya fara Dawafi tare da sassarfa muma muna yi, har sai da aka yi zagaye uku sai (Annabi SAW) ya koma yin tafiya har aka yi zagaye hudu. Bayan haka, Annabi ya zo daidai Mukamu Annabi Ibrahim (AS) sai ya tsaya a bayansa, ya sa Mukamun a gabansa (tsakaninsa da Ka’aba), ya karanta ayar da ke cewa, “… Sai ku riki Mukamu Ibrahim a matsayin wurin Sallah”. Daga nan ya yi Sallar Nafila raka’a biyu, a ta farko ya karanta Kulya Ayyuhal Kafiruun, a ta biyu ya karanta Kulhuwallahu Ahad. Sai Annabi (SAW) ya koma ya sake sumbantar Hajarul As’wad. Daga nan ya fita zuwa kofar Safa, yayin da ya hau kan Safa sai ya karanta ayar da ke cewa, “Hakika Safa da Marwa alamomi ne daga alamomin Addinin Allah…” ya ce “Na fara da wanda Allah ya fara ambata”, da ya hango Ka’aba sai ya ce “La’ilaha illallahu wahdahu la shariykalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli sha’in kadiyr. La’ilaha illallahu anjaza wa’adahu…” Sannan ya yi addu’a (idan Alhaji ya haddace wannan ya karanta, idan bai haddace ba ya karanta Subhanallahi wal-Hamdulillah wal-Lahu akbar ko ya yi ta fadin la’ilaha illallah). Bayan Annabi (SAW) ya gama addu’ar sai ya sake maimaita wannan addu’ar sau uku, sai ya sauko daga Safa ya taho Marwa.
A lokacin da ya zo kwari (tsakiyar Safa da Marwa), sai ya yi sassarfa (a nan maza ke yin sassarfa, ban da mata). Da ya hau kan Marwa sai ya tsaya ya yi addu’a kamar yadda ya yi a Safa. Haka ya rika yi har ya kammala Sa’ayin a Marwa. Sai Annabi (SAW) ya ce “Idan na sa gaba kan abu ba na dawowa, da ban zo da abin hadaya ba, sai in yi Hajjin Tamattu’i in mayar da wannan Hajjin Umura. Amma yanzu duk wanda bai zo da abin hadaya ba, ya mayar da wannan Hajjin ya zama Umura (ya kwance haramarsa, ya yi aski)”. Sahabbai suka ce “Ya Rasulallahi bai fi kwana hudu a yi Arfa ba”, Annabi (SAW) ya ce “Ku cire haramar kawai, ku yi aski.”
Ba shikenan darasin ba, za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah har da kawo darussan da hadisin yake nuna mana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.