Unity Cup: Yau Nijeriya Da Ghana Zasu Kece Raini A Birnin Landan
Published: 28th, May 2025 GMT
A wani wasa da masana ke ganin zai matuƙar ƙayatarwa a gasar kofin Unity, yau Laraba za a buga wasa tsakanin manyan ƙasashen Afrika biyu Nijeriya da Ghana, ba kawai wasan ƙwallon ƙafa bane yau, kare mutunci, da ɗaukaka martabar ƙasa da kuma ramuwar gayya duk suka haɗe a wasan da za a buga a filin wasa na Gtech dake birnin Landan.
Babu kanwar lasa a cikin ƙasashen biyu in dai batu ake na taka leda a nahiyar Afrika duba da cewa dukkansu sun lashe manyan kofuna na cikin gida kuma sun nuna abinda zasu iya a fagen ƙwallon ƙafa a Duniya, Ghana ta lashe gasar AFCON ta ƙasashen Afrika sau huɗu a tarihi yayin da Nijeriya ta lashe sau uku.
Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan Trump Zai Shirya Liyafar Musamman Ga Manyan Ƴan CryptoWasan na yau shi ne karo na 46 da ƙasashen biyu suka haɗu da juna, a wasannin da suka buga a baya ƙasar Ghana ce ke gaba wajen samun nasarori inda ta doke Nijeriya sau 18 aka buga canjarasa 16 sannan Nijeriya ta doke Ghana sau 12, a shekarar 2022 a wani wasa da aka buga a filin wasa na Moshood Abiola Stadium dake Abuja wanda aka tashi canjaras, hakan yayi sanadiyar kasa zuwan Nijeriya buga kofin Duniya da aka buga a ƙasar Qatar.
Wasa tsakanin Nijeriya da Ghana na ɗaya daga cikin manyan wasannin gasar, inda ake hasashen ya kasance mafi zafi da za a buga a cikin dukkan gasar kuma wanda zai sake farfaɗo da ɗaya daga cikin gasar ƙwallon ƙafa ta Afrika, Ahmed Musa, daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi buga wa Nijeriya wasa, ya dawo cikin tawagar duk da cewar bai samu gayyata domin buga wasannin share fagen shiga gasar cin kofin Duniya da aka buga a baya-bayan nan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a RibasMajiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.
“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.
Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).
Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.
Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.
Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.