Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani
Published: 29th, May 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a matsayin bashi.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wasu ’yan jaridu a Kaduna ranar Alhamis, albarkacin cikarsa shekaru biyu a mulki.
A cewar Gwamnan, bankuna da dama sun tunkare shi suna neman ya ci bashi amma ya ki saboda ba ya so ya ci gaba da dilmiyar da jihar a kangin bashi.
Gwamnan ya ce a maimakon haka, ya ma rage kudaden alawus-alawus na Sakataren Gwamnatin jihar da ma na Kwamishinoninsa domin ganin an rage facaka da kudaden gwamnati.
Ya ce, “Sakataren gwamnatina tsohon Babban Sakatare ne a gwamnatin tarayya, kuma tsohon ma’aikacin Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO). Wasu daga cikin Kwamishinonina kuna suna karbar albashi mai tsoka a wuraren aikinsu na baya.
“Hakan ne ya sa na roke su da su yi hakuri da wasu alawus-alawus din su sannan su yi amfani tsofaffin motocin da gwamnatin baya ta yi amfani da su. Haka muka yi muka ci gaba da tafiyar da gwamnatinmu ba tare da ciyo bashi ba ko daya ba,” in ji Uba Sani.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ina Karanta Rantsuwar Da Na Yi A Kullum Don Tuna Nauyin Da Ke Kaina-Gwamna Namadi
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel.
A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu.
“Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”. In ji shi.
Ya bukaci masu rike da madafun iko da su kasance masu kula da al’amuransu cikin tsoron Allah da sanin cewa akwai ranar hisabi da mutuwa.
Da yake jawabi ga sabon shugaban karamar hukumar, Gwamnan ya ce: “Rantsuwar da ka dauka ita ce mu ma muka dauka. Na ajiye tamu a kan teburi a ofishina, kuma kullum ina karanta ta. Ina ba ka shawarar kai ma ka rika karanta taka kafin ka fara aiki a kullum.”
Ya ja hankalin sabon shugaban da kada ya bari son zuciya ya shige masa gaba wajen gudanar da ayyukansa, yana mai cewa son kai na daga cikin manyan matsalolin da ke gurgunta mulki mai nagarta.
Ya bukaci sabon shugaban da ya yi aiki da kowa, ya rika tuntubar masu ruwa da tsaki, tare da sanya mutanen da ya ke wakilta gaba a kowanne lokaci.
Gwamnan ya kammala da cewa shugabanci yana bukatar hakuri, kwarewa, da tsoron Allah, yana mai cewa“babu wanda aka haifa da basirar shugabanci, amma da kaskantar da kai da tsoron Allah, za ka yi nasara”
Usman Muhammad Zaria