Babu Wata Sauran Mafaka Ga ‘Yan Ta’adda, In Ji Shugaban Rundunar Sojin Sama
Published: 28th, May 2025 GMT
Air Marshal Abubakar ya ba da misalin harin da sojin saman suka kai, inda suka dakile harin ‘yan ta’adda a sansanin soji na ‘New Marte’ da sanyin safiyar ranar 24 ga Mayu, 2025, a jihar Borno
A wannan rana, gungun mayakan ISWAP sun yi yunkurin kutsawa sansanin soji ta hanyar amfani da babura da jefa bama-bamai (VBIED).
Jiragen NAF ne ke bayar da bayanan sirri kan duk wata zirga-zirgar masu tada kayar baya a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
Kimanin mutum 16 sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan wani jirgin rundunar sojin sama ta Bangladesh ya fadi a cikin harabar wata makaranta a Dhaka, babban birnin kasar.
Haɗarin jirgin saman yaƙin ya kuma yi sanadin jikkatar gommai, wanda ya kasance guda daga cikin haɗɗura masu muni da ƙasar ta gani a baya-bayan nan a fannin jiragen sama.
Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’aWani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wurin ya ce ya ga jami’an kashe gobara suna kwasar daliban da suka jikkata yayin da sojoji ke taimakawa wajen zakulo mutane daga cikin baraguzan jirgin da ya fadi.
Fiye da mutane 100 ne suka jikkata a hadarin, inda akalla 83 ke karbar magani a asibitoci daban-daban, in ji wani jami’i a ofishin gwamnatin kasar, Muhammad Yunus.
Bayanai sun nuna cewa waɗanda suka jikkata mafi yawansu ɗalibai na karɓar kulawar likitoci, yayinda wasu yayi munin da sai anyi musu gagarumar tiyatar sauya hallita.
Jirgin na F-7 BJI da aka kera a kasar Sin ya tashi ne da karfe 1:06 na rana (07:06 GMT) kuma ya faɗi mintuna kaɗan bayan da aka saki ɗaliban daga ajujuwansu don fita tara a harabar makarantar mai suna Milestone School and College.
Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda iyayen ɗaliban suka isa filin makarantar a ƙiɗime, don neman yaransu, amma wasu anan suka ci karo da gawargwakin yaransu.