NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu?
Published: 29th, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A yau shekara biyu ke nan cif tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai.
Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da kawar da tallafin man fetur.
Yayin da yake cika shekaru biyu, ana ci gaba da muhawara mai zafi game da irin nasarorin da aka samu da kalubalen da ake fuskanta da kuma yadda al’ummar ƙasa ke amfana da tsare-tsaren gwamnati. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada”
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu daga cikin muhimman manufofin Shugaban Kasa Bola Tinubu a cikin shekara biyu, da yadda suka shafi rayuwar ’yan Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya shekara biyun Tinubu
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.
Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi.
Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba.
Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati?
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan