Yadda ambaliyar Neja ta ci mutum 12 ’yan gida daya
Published: 30th, May 2025 GMT
Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ta afka wa yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a ranar Laraba.
Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na Laraba, ta kuma lalata dukiyoyi da dama, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu mutanen da suka bace.
Garin Mokwa dai ya shahara da zama wani zango na direbobin manyan motoci, wanda hakan ya sa garin ya zama daya daga cikin mafiya hada-hadar mutane a jihar ta Neja.
NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a NejaAminiya ta gano cewa akasarin wadanda iftila’in ya fi shafa mata ne da kananan yara.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da mutuwar mutum 21, amma mutanen yankin sun ce wadanda suka mutu za su iya haura 60.
Daga cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar har da wata dalibar Kwalejin Kiwon Lafiya ta Jihar Neja mai suna Binta, wacce ta je garin na Mokwa domin yin hutu, kuma tuni har an samo gawarta.
Wata ’yar yankin mai suna Hajiya Hassana Mokwa, ta shaida wa wakilinmu cewa akalla danginta 12 zuwa 13 ne suka rasu a ambaliyar, wanda kawai ya saura kuma yanzu haka yana can a kwance a asibiti ranga-ranga.
Ta kuma ce akwai wasu daliban makarantar Alkur’ani mallakin dan uwanta da su ma suka rasa ransu.
“Akwai almajirai da dama a makarantar Alkur’anin dan uwana da su ma suka rasu. Babu wanda ya saura da rai a cikin gidan, gaba daya gidan nitsewa ya yi. Idan ka je wajen yanzu, ba za ka taba tinanin ma an taba yin gini a wajen ba,” in ji Hajiya Hassana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya Mokwa a ambaliyar
এছাড়াও পড়ুন:
Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
Sama da mutum 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jihar Katsina, sakamakon sabbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Ƙananan Hukumomin Bakori da Faskari.
Mutane daga ƙauyuka sama da 10 sun nemi mafaka a garin Bakori, inda da dama ke zaune wajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke kwana a waje ba tare da masauki ko abinci ba.
Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kuraWasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa, maharan sukan shiga ƙauyuka da yawa, inda suka dinga harbi, ƙone gidaje, sannan suka sace mutane ciki har da mata da ƙananan yara.
Hare-haren sun fi muni a auyuka irin su Guga, Anguwar Danmarka, Gidan Sule, da sauransu.
Wani dattijo mai shekara’u 68 daga ƙauyen Doma ya ce sama da mutum 250 aka kashe a yankinsa cikin shekaru biyar da suka wuce.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sukan ƙone rumbunan abinci tare da sace dabbobi.
Wata mata da ta kuɓuta daga harin a Anguwar Galadima ta ce iyalinta su 17 sun tsere, inda ta ce an sace sama da mutum 20 a ƙauyen nasu.
Wani saurayi daga Anguwar Dan Marka ya bayyana yadda aka harbe shi sau biyu a ƙafa, kuma yanzu yana amfani da sanda wajen yin tafiya.
Wasu da dama har yanzu suna hannun maharan, yayin da suke neman fansar Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum ɗaya.
Manoma ma na kuka da halin da suka tsinci kansu sakamakon hare-haren.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wani manomi daga Ƙaramar Hukumar Sabuwa ya koka da yadda aka lalata gonarsa.
Amma a martanin da suka bayar, shugabannin Ƙaramar Hukumar sun ce an lalata gonakin da ke kusa da manyan tituna ne domin hana ’yan bindiga amfani da su wajen ɓuya da kuma kai wa matafiya hari.
Amma manoman suna kallon wannan a matsayin wata matsala a gare su.
Shugabannin ƙauyuka da hukumomin gwamnati sun tabbatar da cewa mutane suna ƙara zuwa Bakori kowace rana don neman mafaka.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori, ya ce akwai sama da mutum 3,500 da ke zaune a Bakori, yayin da wasu sama da 2,000 ke zaune a ƙauyen Guga.
An fara raba wa waɗanda suka rasa matsugunansu abinci da kayan masarufi, amma ana buƙatar samum ƙarin taimako.
Ƙungiya ta buƙaci a ayyana dokar ta-ɓaci a BakoriAn buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da kuma ƙungiyoyin agaji su kai wa waɗanda lamarin ya shafa ɗauki cikin gaggawa.
Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna ‘Grassroots Advocates for Peace’ ta nemi Gwamnatin Tarayya ta ayyana Bakori a matsayin yanki mai hatsari.
Sun buƙaci ƙarin jami’an tsaro, da ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Sun kuma buƙaci a kula da lafiyar kwakwalwar waɗanda suka kuɓuta daga hare-haren da kuma hukunta masu kai hare-haren.
Gwamnatin Katsina na ƙoƙarin magance matsalarA nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina, ta ce tana ƙoƙarin wajen magance matsalar.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Nasir Muazu, ya ce suna ƙoƙarin magance matsalolin da Ƙaramar Hukumar ke fama da su.
Ya ce akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin yada ƙarya a kafafen sada zumunta don haifar da tsoro da ruɗani a zukatan jama’a.
Ya kuma ce an samu sauƙin kai hare-hare a wasu yankuna kamar Jibia da Batsari.
Kwamishinan, ya bayyana cewa an kafa rundunar ‘Katsina Community Watch Corps’ domin taimaka wa sojoji, ’yan sanda da ’yan sa-kai wajen shiga dazuka da ke da wuyar shiga.
Sai dai ya buƙaci jama’a da su ci gaba da jajircewa da kuma bayar da rahoton duk wani abu da su yarda da shi ba.
An samu sauƙin kai hare-hare cikin shekara 2 — RibaduA yayin da gwamnati ke cewa ana samun ci gaba, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce Najeriya ta fi samun zaman lafiya a yanzu sama da shekaru biyu da suka wuce.
Ya ce an ceto da mutum sama da 11,000 da aka sace, kuma an kashe wasu daga cikin manyan shugabannin ’yan bindiga.
Ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa jagoranci da tsare-tsaren tsaro da suka haifar da wannan sauyi.
Sai dai waɗanda ke zaune a matsuguni na wucin gadi a Bakori da wasu yankuna, rayuwa cikin tsaka mai wuya.
Wasu sun ce har yanzu ba su da ƙwarin gwiwar komawa gidajensu.
Sun tabbatar da cewar sai gwamnati ta samar da tsaro mai ɗorewa, sannan za su koma muhallansu, saɓanin haka za su ci gaba da zama a inda suke a yanzu.