HausaTv:
2025-11-02@17:19:54 GMT

 Kasar Chile Na Shirin Yanke Alakar Diplomasiyya Da “Isra’ila”

Published: 29th, May 2025 GMT

Jaridar Vadiot Ahranot ta HKI  ta buga labarin dake cewa; Shugaban kasar Chile Gabriel Boric ya bayar da umarni a janye jami’an diplomasiyyarsa kasarsa masu kula da alakar soja daga ofishin jakadancin kasar tasa a Tel Aviv.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Chile ta wallafa wani sako a shafinta na “Internet” cewa; Ofishin jakadancin nata ya sanar  da mahukunta wannan haramtacciyar cewa sun janye jami’an diplomasiyyar biyu.

Kasar ta Chile ta bayyana dalilinta na yin haka da cewa, shi ne yanayin da mutane Gaza suke ciki ta fuskar jin kai ta tabarbarewar harkokin rayuwa saboda yakin da Isra’ila take yi. Haka nan kuma kin amincewar “Isra’ila” da a shigar da kayan agaji cikin yankin na zirin Gaza.

Ita dai kasar Chile tana cikin wadanda su ka yi ta kira ga “Isr’ila” da ta datakar da yakin da take yi a Gaza, sannan kuma ta bari a shigar da kayan agaji cikin yankin.

A bisa rahoton jaridar ta Yedioy Ahranot, kasar Chile tana da jami’an soja uku a ofishin jakadancinta da su ne na ruwa, kasa da sama, amma tun watanni biyu da su ka gabata aka janye daya daga cikinsu, yanzu kuma aka jane biyun da su ka saura.

Ana sa ran cewa a ranar Lahadi mai zuwa da shugaban kasar ta Chile za iyi jawabin shekara-shekara ga al’ummar kasar, zai sanar da yanke alakar diplomasiyya da HJKI.

A gefe daya, Falasdinawa sun yaba da matakin da kasar ta Chile ta dauka na janye jami’an diplomasiyyarta daga HKI tre da bayyana shi da cewa; mataki ne mai muhimmanci da kuma nuna jarunta domin nuna kin amincewa da laifukan da HKI take tafkawa a Falasdinu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar ta Chile kasar Chile

এছাড়াও পড়ুন:

Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka

A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya.

Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar.

Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 

“Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar da ‘yan ta’addan Musulmai da ke aikata wannan ta’asar,” in ji Hegseth.

Trump dai ya yi wannan barazanar ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, inda ya ce Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma tana iya “shiga ƙasar da ƙarfin soji domin share ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci.”

“Idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wata tallafi, kuma mai yiwuwa ta shiga wannan ƙasar, ta cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’addan Musulmai masu zafin kishin addini,” in ji Trump.

Ya kuma gargaɗi gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ɗaukar mataki, yana cewa idan Amurka ta kai farmaki “za ta yi shi cikin sauri, da tsananin ƙarfi, da gamsuwa.”

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya mayar da Nijeriya cikin jerin ƙasashen da za a sanyawa ido, yana zargin cewa “ana yi wa Kiristoci kisan gilla” a hannun ƙungiyoyin Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.

Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.

A cewar mai ba wa Tinubun shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, za a yi ganawa tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Trump “a cikin kwanaki kaɗan masu zuwa” domin tattaunawa da warware wannan saɓanin fahimta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu