WAEC: Daliban Taraba Sun Zauna Jarabawar Turanci Da Karfe 8:25 Na Dare
Published: 29th, May 2025 GMT
A wani lamari mai ban al’ajabi, a daren jiya dalibai a jihar Taraba sun zana jarrabawar kammala karatunsu na Ingilishi na WAEC da karfe 8:25 na dare, sama da sa’o’i 12 da fara sa’o’i 8:00 na safe.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa jinkirin ya haifar da rudani da damuwa a tsakanin iyaye da masu kula da su, wadanda ke nuna shakku kan dalilan dage jarabawar da ba a taba ganin irinsa ba.
Lamarin dai ya yi matukar tayar da hankali idan aka yi la’akari da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a yankin. Ba tare da wani bayani a hukumance daga WAEC ba, dalibai da iyaye suna mamakin abin da ya jawo tsaikon da kuma yadda hakan zai yi tasiri a ragowar jarabawar.
Wannan lamari da ba a saba gani ba ya haifar da tambayoyi fiye da amsoshi, kuma masu ruwa da tsaki suna dakon sanarwar hukuma daga WAEC domin fayyace lamarin.
KARSHE/JAMILA ABBA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
WHO Ta Buƙaci Isra’ila Ta Saki Ma’aikacinta Da Aka Kama A Gaza
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya bukaci Isra’ila ta saki wani ma’aikacin hukumar da ya ce sojojin Isra’ila sun kama a wani farmaki da suka kai a tsakiyar Gaza ranar Litinin.
Tedros Ghebreyesus ya ce sojojin sun jefa ma’aikatan agaji da iyalansu cikin hatsari a lokacin da suka shiga gidajensu da kuma babban dakin ajiyar kaya a Deir al-Balah.
Ya yi alƘawarin cewa WHO za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a yankin.
Deir al-Balah dai na cike makil da Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu a kusan shekaru biyu na yakin Gaza