Aminiya:
2025-09-18@06:57:30 GMT

NAJERIYA A YAU: Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu?

Published: 30th, May 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Rashin tsaro na cikin matsalolin da suke ci gaba da ci wa ’yan Najeriya da dama tuwo a kwarya, har a wannan lokaci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yake cika shekara biyu a kan mulki.

 

Wasu rahotanni da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar dai sun koka da yadda suke ganin matsalar ta kara kamari a wadannan shekarun.

NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada”

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan matsala ta rashin tsaro.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.

Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.

 

Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.

Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.

Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na  zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.

Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.

Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?
  • Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS